Sashe 61
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Romeo ko mai na shi a nitse yake yin sa, san nan komai daki daki yake bin sa ɗaya bayan ɗaya, baya son hargagi da rashin nitsuwa a lamuran sa, bai taɓa damuwa da yan uwan sa sai sun yi aiki ba, shi a ganin sa dukiyar sa ya ishe su da suji daɗin duniyar su, shi yasa yake sake musu kuɗi baya damuwa da lallai sai ya san abun da suke saboda ya yarda da su, a baya kafin yanzu baya basu kuɗi sosai lokacin da James ke School wan nan dalilin yasa James ya shiga wan nan har kan, daga baya bayan ya kammala school Romeo ya fara sake musu kuɗi over dan a cewar sa yanzu sun yi hankali, bai taɓa bibiyar su ko bincikan su dan yaga me suke ba, dan ya basu yarda 100, yana bala'i son su fiye da tunanin mai tunani, amma duk da wan nan son da yake musu baya hanawa ya basu horo idan suka masa ba dai dai ba, duk cikin yan uwan sa yafi son Michael hakan yasa ko Michael yayi laifi baya iya hukun ta shi dan yana kaunar sa over, bai taɓa hora Michael ba, idan Michael yayi laifi a gaban kowa, kowa yaga yayi laifin kuma sun san yayi laifin, sai Romeo ya fiske yace Tga ya hukun tashi ko kuma James, gaba ɗayan su daga James ɗin har Tga ɗin basa iya hukun ta Michael ɗin saboda son da suke masa, shi yasa Michael ke zuba tsiyar sa iya son ran sa, yanzu haka jiya da daddare yaje ya samu Romeo ya rinƙa zuba masa kukan shagwaɓa yana rokan sa da yayi hakuri a kan bai rubuta Exam ba amma next time yayi alƙawarin zai rubuta, sosai Romeo ya masa faɗa a kan ya tsaya yayi karatu, amma ya kasa hukun ta shi, su uncle Herry duk sun fi kaunar Michael fiye da kowa, sosai Romeo ke sakar masa kuɗi yana abun da ya ga dama, sai dai yana da kyau ta over da mutun ya roke sa zai bada, abokan sa su dest duk ya sai musu motocin hawa, a School na su kowa ya san shi da kyauta idan ka cire tsoro kazo ka tambaye sa tofa zai baka abun da ma baka taɓa zato ba, haka zalika duk kuɗin nan da Romeo ke bashi hakan bai sa ya nemi matan ban za ba, shi mace ma bata gaban sa, saboda gani yake halin su ɗaya da mum ɗin sa, a baya yana shaye shaye daga baya yazo ya dai na saboda wani friend na shi dake hana shi, kuma yana kaunar abokin nasa over, duk sati yana zuwa gidan gajiyayyu da marayu ya ta raba musu abubuwa kamar dai yadda yaga Romeo na yi, sai dai shi Romeo har da church ɗin su yake bawa taimako shi kuma Michael saboda tsanar da yayi wa Pasto church ɗin ma sai an yi da gaske yake zuwa kuma baya bawa Pasto ko biyar, idan yaje church ɗin ma baya sauraron komai da suke faɗe, saboda gani yake ba amfani, dan bai da ilimi ba karatu yayi ba shi gani yake ɓata masa lokaci kawai suke da surutun banza, kan sa emty yake duk mate na shi a School wasu sun zama lectures wasu kuma sun kama aikin yi amma shi yana nan sai jagaliyanci ya sa a gaba, wan nan dalilin ne yasa ba abun da ya sani sai kashe kuɗi da zuwa party clubs da abokan sa, hakan yasa yake kallon Pasto a matsayin mahaukaci mara aikin yi, shi kwanta kwata bai yarda da wasu addinai ba a cewar sa duk adinin nan ɓata lokaci ne.
Bari mu leƙa Nigeria mu dawo
*KADUNA*
Har bakin hanya Rufaidat ta rako Aafia sai murna take tana zuba mata godiya, ita kuma Aafia sai fatan alkhari take wa Rufaidat da fatan ta tsaya tayi karatu da kyau, dan karatu shi ne mutun, anguwar nasu shiru ba hayani sosai, shi kan shi bakin hanyar ba jama'a sosai, kafa ta É—auke saboda ba babban hanya bane, irin kana nan titin nan ne dake ratsawa ta cikin layi
suna tsaye a bakin hanya suna jiran taxi yazo Aafia ta hau ta koma gida, wata dankareriyar mota kirar *Mercedes-Benz* tazo tayi parking a gaban su, a hankali mamallakin motar ya sauke glass É—in motar sa, babban Alajine mai É—an yawan shekaru, dan a kalla zai kai, 45 to 47 years, sanye yake cikin manyan kayan hausawa da hula, yayi shiga irin ta kamala da cikar bahaushe, nan take Aafia ta É—aure fuska kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, ita kuma Rufaidat sai washe baki take an ga mai kuÉ—i.
"Sannun ku yan mata" Alhajin ya faɗa yana washe baki, cikin sauri Rufee tace "Yauwa Alhaji Sannun ka" ita kuwa Aafia ko kallon in da yake ba tayi ba dan a koi ta da jiji da kai over "Yan mata idan ba damuwa ku shigo na kai ku in da zaku je mana, dan baku yi kalar tsayuwa cikin ranar nan ba" yana magana yana kallon Aafia, kara washe baki Rufee tayi tace "Kawata ce kaɗai zata tafi ita zaka ragewa hanya ni kuma ga gidan mu a nan idan ka dawo" a sukwane Aafia ta juyo tana kallon Rufee da mamaki, wato ita rufe har tallan kan ta take, shi kuwa Alhaji washe baki yayi tare da shafa gemun sa yana faɗin "Daman ai kawar taki ita ta tsai dani" hannu Aafia ta miƙawa Rufee suka gaisa, san nan tace "Sai kin zo gida ko sai mun haɗu ga taxi nan zuwa na wuce"
"Wow gaskiya izzar ki ya kara burgeni ba kaÉ—an ba, hakan ya sa naji na kara son ki" cewar Alhaji, ita kuwa Aafia wucewa tayi abun ta, ta tari taxi É—in da yazo ta shiga, cikin sauri Alhaji ya buÉ—e motar ya fito waje ya nufi wajen taxi É—in yana faÉ—in "Dakata malam, haba yan mata, dan Allah ki tsaya mana, minti biyu kawai nake bukata daga gareki" a kule Aafia tace "Kai malam ko in ce baba, kai baka ji kunyar tare yarinya sa'ar yar cikin ka kace kana so ba, to idan kai baka san kunya ba ni na san shi, kai mai taxi muje!!!" Ta kai karshen maganar cikin faÉ—a,
kunna taxi É—in mai taxin yayi suka bar wajen sai magana Alhaji yake amma Aafia taki kula shi
Sai da taxi É—in ya kurewa ganin sa san nan ya juya cikin sauri ya koma cikin motar sa, cikin rangwaÉ—a Rufee tace "Alhaji ai daman ni nasan ba zata saurare ka ba, saboda bata da mutunci ga girman kai da izzar banza, ga rashin kunya da rashin girmama manya, amma ni ba ruwana ina girmama manya musamman irin ka mai kima da daraja" kakalo murmushi dole Alhajin yayi kafin yace "Nagode" tana kokarin sake magana sai ga yayan ta Yusuf, a sukwane ta wuce ta nufi gida ba dan taso ba, dan tana bala'i tsoron Yusuf, bashi da wasa ko kaÉ—an
shi kuwa Yusuf cikin fushi ya nufo Alhaji, yayin da Alhajin ke kokarin kunna motar sa yabi bayan Aafia.
"Kai malam wanene kai?" Cewar Yusuf, shiru Alhajin yayiwa Yusuf bai yi magana ba, kasan cewar Yusuf mutun ne mafaɗa ci hakan yasa ya fara faɗa "Wato kune irin Alhazawan dake ɓata yaran talakawan ko? To wlh ƙanwata tafi karfin ka idan ka kuskura na sake ganin kafar ka a layin nan wlh sai ran ka ya ɓaci bar ganin kana da kuɗi, maganin ka zan yi, a kan kanena bani da mutunci" ba karamin ɓatawa Alhajin nan rai Yusuf yayi ba, gashi ya dakatar da shi daga bin Aafia, cikin fushi ya juyo da idon sa kan Yusuf, nan take idon nasa suka sauya launi suka koma light purple mai bala'i haske kamar torchlight, hasken na haska face ɗin Yusuf, Yusuf ya zube kasa a wajen sai gawa, a guje Alhaji ya ja motar sa ya bar layin.
sai da ya É—an yi nisa san nan ya dakatar da motar tasa tare da canza kalar idon sa ya koma irin na mutane, fari da baki, haÉ—e da canza kalar face nashi da jikin sa dukka ya zama matashi mai jini a jika wadda ba zai wuci 25 years ba kyakkyawa fari tas da shi kamar balarabe, san nan ya ja motar yabi hanyar da su Aafia suka bi, ko zai gan ta.
*KANO*
Daddyn Jelly ya shiga damuwar da har ta jawo masa rashin lafiya mai tsanani dan shi a gaskiya ba zai iya cin amana ba, gashi yana tsoron video sa ta fita wa duniya, tun jelly bata iya gane daddyn ta na cikin damuwa har tazo ta fara ganewa, duk in ta tambaye sa sai yace mata ba komai, haka ta ci-gaba da hakuri, gashi su biyu suke rayuwar su sai Nana da Zuwaira masu aikin su, yan uwan maman Jelly suna zuwa time to time, iyayen Mahaifiyar Jelly sunyi sunyi a kan daddyn Jelly ya auri kanwar Hajiya Umaima wato mum ɗin Jelly amma yaki yadda yace shi baya so, ba zai iya rayuwa da kowa ce mace ce ba, dan shi gani yake ko kan kanwar Hajiya Umaima ɗin ma ba zata iya kula masa da Jelly ba, yafi son ya kula da kayan sa shi da kan sa, shi yasa ya zaɓi suyi rayuwar su su buyu, ko hutu baya barin Jelly taje wajen family maman ta baya son komai ya raba ta da gida in ba school ba.
*Washington DC*