← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 126

Sashe 121

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Hajiya ta gama mata wanka tsab ne ta ɗaura mata towel suka fito suka nufi bedroom ɗin Jelly ɗin, sosai Hajiya baiwar Allah ta mata kwalliya mai kyau ta sanya mata kaya dogon riga abaya wanda yaya Nawid ɗin ta ya sayo mata, sannan ta feshe ta da turare mai kamshi, tsab ta koma kamar ba ita ba, ta dawo asalin Jellyn daddy, riƙo hannun ta Hajiya tayi suka fito palo.

Saman sofa ta zaunar da ita tace "Ki zauna kiyi kallo bari nayiwa Abbon ku girki kinga yau a part namu yake kuma yamma yayi" make kafaɗa Jelly tayi ta turo baki tana faɗin "Ni a'a zan biki kitchen na taya ki aikin nima" Hajiya zatayi magana Nawid da ya fito yanzu yace "Ai gara duk wani aiki da zaki nayi Ummi ki rinƙa yi tare da ita ko zata koyi wani abun arziki tun da kinga mace ce kuma ba yarinya bace nan gaba kaɗan sai aure" jin abun da Nawid yace yasa Hajiya tace eh yana da gaskiya dan haka sai ta kama hannun Jelly suka wuce kitchen tare

Aiki Hajiya ta fara yi, tana yi tana nunawa Jelly komai dalla dalla, sai gyaɗa mata kai Jelly keyi kamar mai gane duk abun da Hajiya ke faɗe, alhalin ba abun da ke shiga kan ta, miyar steew sukayi ko in ce Hajiya tayi dan Jelly kam tana tsaye a gefe tana ganin duk abun da Hajiya ke sakawa a cikin miyar, ta zuba ido tana kallon yadda Hajiya ke saka su carry kaɗan kaɗan a cikin miyar, ji take kamar taje ta karɓa robar carry ɗin ta bulbula dukka cikin miyar dan ita bata son harka da karanta so take taga ana bulbula komai yaji sosai

Bayan Hajiya ta tabbatar miyan yayi ne sai ta sauke dai'dai lokacin kuma ruwan shinkafa data É—aura a gefe É—ayan gas É—in ya fara tafasa, store ta nufa tana faÉ—in "Bari na É—ebo shinkafa" shiru Jelly tayi bata amsa ba

Hajiya na shiga store Jelly ta É—auko goran plate wash wani omo ne na wanke wanke, dan taga Hajiya ta saka su curry black pepper da sauran su, kuma taga kaÉ—an kaÉ—an Hajiya ta saka, ita kuma bata son harkan abu kaÉ—an tafi son dayawa shiyasa Hajiya na shiga cikin store ta É—auko goran plate wash dake kusa da pots da Hajiya ta wanke yanzu, dan a tunanin ta shima kayan haÉ—in miyane

BuÉ—e miyar tayi ta zuba mai É—an yawa sannan ta gauraya miyar, ta mayar da plate wash É—in ta ajiye a in da ta dauko, ta É—auko ledan gishiri shima ta zuba ta É—an kara su carry da duk wani abu da Hajiya ta sa a miyar, jin Hajiya na zuwa yasa tayi saurin gauraya miyar ta mayar ta rufe tana jin daÉ—i ta zuba abubuwa dayawa dan ita bata son har abu kaÉ—an tafi son taga komai yaji sosai zam zam.

Koda Hajiya ta dawo bata wani lura da Jelly ba kawai ta ci-gaba da aikin ta, har suka kammala, da Hajiya tazo zuba abincin a cikin warmers data buÉ—e miyar taga ya É—an canza kala amma da yake hankalin ta baya wajen tana sauri mangariba yayi zataje tayi wanka dan Abbo ya kusa dawowa hakan yasa ta zuba abincin kawai ta kwasa suka wuce palo

A saman table ta jere komai sannan tace Jelly ta zauna bari taje tayi wanka, ba musu Jelly ta koma ta zauna saman sofa tana tunanin ko dai ta É—auko su curry É—in nan ne ta kara dan kamar wadda ita ma tasa yayi kaÉ—an, sai sake sake take a zuciyar ta ita kaÉ—ai, har Hajiya tayi wanka ta fito tace taje tayi alwaya suyi Sallah

Ba musu ta tashi ta nufi toilet nata ta É—auro alwalar ta kamar yadda Hajiya ta koya mata sannan ta fito ta zo sukayi Sallah tare da Hajiya a palo.

Sai bayan sallar issha sannan Abbo da Nawid suka shigo, wanka sukaje suka fara yi first kafin su zo saman table su zauna, Hajiya ita tayi serving nasu dan tace bata son masu aiki ita take komai da kan ta.

Abbo shi ya fara kai abincin bakin sa, a É—ari ya tofoshi waje har yana kakarin amai, zaro ido Hajiya tayi tana tambayar menene a ruÉ—e da hannu ya mata nuni da ta É—anÉ—ana abincin taji dan ya kasa magana abincin har É—aye fatar baki yake saboda gishiri da plates wash da kuma su carry da Jelly ta banka a ciki yayi yawa over yana É—aye harshe

Nawid kam tun da yaga haka sai ya fasa kai abincin bakin sa ya mai da ya ajiye, Hajiya kuma É—aukan spoon tayi ta É—eba abincin ta kai bakin ta, a sukwane ta fito da shi waje tana salati, ita kam Jelly dama tun da suka zauna ta fara cin naman kasa hankalin ta baya kan su kwata kwata, sai bayan ta cinye cinyar kazar ne ta É—auki spoon ta É—ebo shinkafar da labcecen miya ta kai bakin ta

Wani ihu ta fasa wadda yasa Hajiya da Nawid miƙewa suna kokarin gudu, shi ma Abbo ya tsorata da ihun sai dai bai miƙe ba.

Rai a ɓace Nawid yace "Ke baby me haka?" Abbo ne ya daka masa tsawa "Haba Nawid me ta maka zaka mata wannan tsawa haka?!!" Zaro ido waje Nawid yayi yana mamakin abun da Abbon yayi, Abbo bai taɓa yi masa tsawa ba ko da wasa, hakan da yayi yanzu ya kara ɗarsa zargin sa a zuciyar Nawid ɗin, ita kan ta Hajiya sai da tayi mamaki a wannan karon Abbo bai taɓa yiwa Nawid tsawa ba sai yau

Abbo kuwa ganin Hajiya da Nawid sunyi mamaki ne yasa yayi saurin basar da maganar da cewa "Ku tashi muje restaurant kawai muci abincin tunda wannan kam dai ya tashi aiki, sannan Nawid kai kuma ka dai na yiwa baby tsawa baka ganin tana cikin ciwo ne?" Shiru Nawid yayi yana tunanin yadda zan binciko me Abbo'n sa ke nufi da Jelly, dan yasan ba haka kawai zai rinƙa yin wayen nan abubuwa a kan taba, Nawid ba yaro bane a kalla zai kai 26 years a duniya gashi da saurin fahimtar abubuwa

Ganin sunyi shiru basu da niyar tafiya ne yasa Abbo ya miƙe yana faɗin "Muje ko?" Jiki ba kwari Hajiya ta wuce bedroom nata tana faɗin "Bari na ɗauko mayafi" to kawai Abbo yace suka wuce waje shi da Nawid ita kuma Jelly tana zaune tana cin namar gazan ta, dan tun da ta saka shinƙafar a bakin ta tayi wannan ihu daya razana su Hajiya sai ta ci-gaba da cin namar ta kawai bata ma san da su Hajiya sun tsorata ba.

Jim kaɗan Hajiya ta fito sanye da mayafin hannun ta riƙe da mayafin Jelly, zuwa tayi ta sanyawa Jelly mayafin sai faman figar nama Jelly keyi, riƙo hannun ta Hajiya tayi suka bi bayan su Abbo, motar Nawid suka shiga shi yaja su suka tafi zuwa restaurant ɗan cin abinci, sai mamaki Hajiya take, me ya samu abincin da ta girka.

To masu karatu mu leƙo Daular mutuwa mu dawo

👹DAULAR MUTUWA👹

Sosai duna yake aiki a kan yadda zai samu ya kuɓutar da Rimsha daga ɗakin duhu na Queen, baba da Mustapha kuwa sun dukufa sai addu'ar fatan nasara suke masa, Ayla da Kausar ma ba'a bar su a baya ba, sosai sukewa Rimsha addu'a a zuciyar su dan ba daman kiran sunan Allah a baki, amma fa sosai Ayla ke kuka duk lokacin da ta keɓe ita kaɗai sai tayi kukan rashin Rimsha, yan kwanakin kalilan da sukayi da Rimsha sunyi sabo sosai wadda rabuwar su abune mai matukar wuya wadda zai yiwa ko wannen su balai ciwo, Ayla akoi ta da hakuri ga kirki da son mutane shiru shiru bata da hayani ta.

Allah sarki Ayla baiwar Allah ko ya akayi tazo daular mutuwa ita kuma oho, sai dai ku kasance da alkalamin princess Teema dan ita kaÉ—ai ce zata warware muku komai sannu a hankali, ammafa akoi cakwakiya, yanzu wasan zai fara.

To masu karatu kuma sai ku taya Rimsha'n ku da Addu'a kuyiwa duna addu'ar fatan nasara na barku lafiya, gobe idan Allah ya kai mu The beginning zai kare sai ku shirya, yanzu wasan zai fara bye sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu..

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞

TRIPLET'S💞

💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)

*GargarÉ—i*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_

WhatsApp me for more information 09162620621

Episode 42-43

💞KADUNA GIDAN ABBI💞

Tun da Abbi ya ɗauko daddyn Jelly Aafia ta ɓata rai alamar bata ji daɗin zuwan sa gidan ba, dan shi ba fita zai yi ba yana gida ko da yaushe, idan kuma yana gida basu isa su fita da shigar da suke soba, zai takura musu lallai su saka hijabi idan kuma suka ki zai sanar da Abbi in suka masa rashin kunya kuma sun san Abbi uban su zai ci a kan ɗan uwan sa

sai faman hararar dad Aafia take, ji take kamar taje ta shaƙe sa dan haushi, shikuwa dad sai faman jan su a jiki yake da wasa da dariya wai ko zai samu raɗaɗin ciwon rashin Jelly ya ragu masa a zuciyar sa, sai dai bai samu haɗin kan Aafia ba domin ko magana ya mata ciki ciki take amsawa ɗan gara Umaisha ma tana amsa masa da gimamawa a matsayin sa na bappan ta kuma a matsayin baba ta ɗauke sa.
Chapter 121 · 0% Book details