← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 126

Sashe 106

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren shi kuma Abbo yayi saurin cewa kar a kai ta school ne dan baya son a kai ta makaranta wani wadda ya santa ya ganta ya gane ta har yaje ya faɗa wa iyayen ta, suzo su ɗauke ta ba tare da ya bayyana mata soyayyan sa ba, dan yasan in dai iyayen ta suka ɗauke ta tofa ko zai mutu ba zasu bashi auren taba, shiyasa yake son su barta a nan har lokacin da zai bayyana mata soyayyar sa.

Duk kan su dai kowa da abun da yake tunani, ita kuwa Jelly sai faman cin nama kaza take bata ma jin abun da suke faÉ—a, zancen su baya shiga kunnen ta.

Har su Abbo suka gama cin abincin su Jelly bata sani ba, tana can duniyar naman kaza, ta mance da su ma zaune a wajen.

Lokacin da ta gama cin naman ta, ta ɗago kai sai taga table ɗin wayam babu kowa, turo baki tayi ta miƙe ta wuce bedroom nata, dan yanzu ta ɗan kara sakin jiki tana iya zama a bedroom ɗin nata ita kaɗai.

Shi kuwa Nawid tunani fal ransa game da Jelly, haka ya shirya ya tafi office, Abbo kuwa ko ajikin sa sai wani daɗin ma yake ji, Hajiya Turai baiwar Allah da zuciya ɗaya ta riƙe Jelly har cikin ranta tana mutuwar kaunar Jelly, bata wani tunanin mugunta ko wani abu wa Jelly, haka zalika a nata tunanin Abbo ma a ƴar cikin sa ya ɗauki Jelly bata kawo komai a ranta ba, shiyasa idan yana yiwa Jelly wasu abubuwan bata damuwa, kuma duk hukunci da ya yanke a kan jelly bata taɓa damuwa, sai tace ai yar sace yana da damar yanke mata duk hukuncin da ya ga dama.

A ɓangaren daddyn Jelly kuwa, bawan Allah duk ya fita hayyacin sa, duk wanna murmushi kullun dake kan fuskar nan tasa ta kau, ya sauya kamar ba shi ba, ya zama so silent ko magana bai cika yi ba, sai in zai sayi wani abun, tun ranar da Jelly ta ɓata bai sake zuwa company ba har yau, Engineer Muhammad Imam ke kula da company yanzu, daddyn Jelly yana gida, yace ba zai sake zuwa ko ina ba har sai Jelly ta bayyana, saboda ɓatan Jelly har jini sai da aka kara masa, yayi baki ya rame sosai, sai manya manyan idon sa irin nata zaka gani a face nashi, saboda ramar da yayi har kasusuwan wuyar sa sun bayyana sosai, ya sanar da su Zuwaira duk wanda yazo neman sa suce baya nan, hakan yasa baban Muneer yazo neman sa yafi sau a kirga baya samun sa, dan kuwa su Zuwaira ce masa suke daddyn Jelly baya nan kuma basu san in da yake ba, idan ya kira wayar sa a kashe kasan cewar daddyn Jelly yaki gyara wayar tasa da ta fashe, kuma yaki gyarawa ne saboda Imran, baya son ya hana Imran rubuta Exam da zai yi da kyau, baya son jefa shi cikin damuwa, sai dai kuma abun da daddy bai sani ba, rashin samun su a waya da Imran bai yi ba yafi jefasa cikin tashin hankali fiye da komai, Imran ya shiga damuwa sosai a kan ko lafiya number bappan sa bata shiga, damuwar har tana nema tayi affecting nasa, baya wani karatu sosai, bai da aiki sai tunanin Jelly da daddy, yau saura 2 weeks dai dai su gama komai su dawo gida Nigeria, sosai shima Imran ɗin yayi rama saboda tunanin wani hali bappan sa da matar sa Jelly suke ciki.

Ba Imran kawai ba har Irfan da Akila sun shiga damuwar lafiya number bappan su bata shiga, shikam Akil daman ko number bappan nasa bai da shi bare ma yasan tana shiga ko bata shiga, ko number bappan sa kuma sirikin sa wato Abbin su Umaisha shima bai da shi, number Umaisha kawai gare sa.

Yau ne Abbi ya shirya tsab zai je Kano ya duba lafiya number daddy bata shiga, dan Irfan da Imran sun dame shi a kan yaje ya duba musu meke faruwa dasu Jelly, tun karfe 10 na safe ya fice yayiwa Aunty sallama yace ta sanar da su Aafia idan sun tashi barci.

Abbi na tafiya tamkar ya tafi ne da lafiyar Aunty, nan fa ta fara laulayin ciki wadda bata san tana da shi ba, tun fitan Abbi take ta faman amai a tsakiyar palon kasa, dan kuwa ta raka Abbi kofar palo ta masa Addu'a ya tafi ne ta juyo zata dawo, nan fa amai yace bata isa ba, tana kokarin gudu ta haura sama amma ina yaci karfin ta shi ne ta zauna a tsakiyar palon kawai tana tikar amai É—in, kamar zata amayar da kayan cikin ta dukka, shi kuwa Abbi bai ji lokacin da ta fara amai É—in ba, ya shiga motar sa ya tafi.

Sautin kakarin amai É—in da take ne ya tashi su Aafia daga barci, daga su sai kayan barci suka sauko palon kasa, sai faman tura baki suke

Tun basu karisa sauko wa ba Aafia tace "Kutumar uban can, ke Halima dan jahila ce ke sai ki zauna a tsakar palo kinawa mutane amai dan ki samu amai É—in muma ko? To wlh baki isa ba" Umaisha kuwa wucewa tayi ta kwata saman sofa tana faÉ—in "Amma gaskiya Aunty baki kyauta min ba, ina barci na kawai zaki tashe ni, gaskiya wanna zalunci ne, idan ma amai É—in ne kije toilet naki kiyi mana amma sai kizo tsakiyar Palo, dan rashin hankali" tsawa Aafia ta dakawa Umaisha "Ke dallah ki mana shiru!! ba wani zancen adalci a nan yar iska dai iskanci ne yasa ta fito palo ta fara amai É—in nan, kuma ni nasan da biyu tayi shi, kin san wanna amai É—in da take wlh da alaman ciki gareta, shine ta fito ta nuna mana idan zamu mutu mu mutu to ba zamu mutu ba, zaki yabawa aya zakin ta" ta kai karshen maganar tare da wucewa fuuu ta haye sama ta koma É—akin su, aunty kuwa ji take kamar ran ta zai fita, cikin ta sai murÉ—a mata yake, duk abun da su Aafia ke faÉ—e ko kaÉ—an baya shiga mata kunne dan ta fara fita a hayyacin ta

Umaisha na zaune tana kallon ta, sai da taga da gaske Aunty na kokarin sume wa a wajen sanna ta miƙe da gudu ta haura sama tana kiran Aafia a kan tazo ta taimaka mata su kai Aunty asibiti, nan fa Aafia ta murje idon ta tace bata san wanna zance ba, ita ba ruwan ta da wata aunty, Auntyn ta mutu ma idan ta ga dama.

Sosai Umaisha taji babu daɗi abun da Aafia tayi, da sauri ta dawo palo, tazo ta riƙo aunty da kyar suka nufi waje, taje ta buɗe kofar motar ta gidan baya ta sanya aunty, ta shiga gidan gaba, babu ko ɗankwali a kanta daga ita sai kayan barci haka taja motar suka nufi hospital

Ita kuma sarauniya Aafia tana É—aki tana faman neman layin Rufee dan ta sanar mata Aunty na da ciki ya zasu yi.

Tayi Sa'a kuwa ta samu number Rufee a buÉ—e, kira É—aya Rufee ta É—auka, cike da kunan rai Aafia ta sanar mata da abun da ke faruwa na Aunty na da ciki, tun bata tabbatar da gaskiyar cikin ne ko ba shi ba, kai tsaye tacewa Rufee ciki ne,

Duk da rasuwar amal da akawa Rufee bai sa ta saduda ta koma ga Allah ba, haka ta ɗaura Aafia kan mummum shawara "Kina jina Aafia idan muka haɗu gobe a School zan baki wani magani sai ki zuba mata a abinci, cikin nata zai zube Shikenan" ita kuwa Aafia Allah sarki Rufee ta juya mata kwakwalwa, da murnan ta ta amsawa Rufee da to, tana kokarin katse kiran ne Rufee tace "Aafia ya batun Alhajin nan fa, kin ga next week zamu kammala Exam" shiru Aafia ta ɗan yi kafin tace "Okey idan mun fito class na karshe ranar da zamu gama Exam kenan, irin karfe biyun nan sai mu haɗu da shi, amma fa ba zan wuce 1 hour ba dan a ranar yaya Irfan zai yi diran dare kasar nan, kinga kuwa idan yaya Irfan ya dawo babu zancen fita ko kuwa hira a School, dan bincike yake wani lokaci muke da class yaushe kuma zamu fito class, kuma kinga ma next week zamu gama Exam idan muka gama ba zai taɓa barin mu mu fita zuwa wani waje ba tun da ba school, ko shopping sai dai ya kai mu da kan sa, haka yake ya cika takura shiyasa bana son ya dawo" yar tsaki Rufee tayi kafin tace "To shikenan zan faɗa wa Alhajin ba komai hour ɗayan ma yayi ai" daga haka sukayi sallama Aafia ta haye saman gadon tayi kwanciyar hankali kwance tana tunanin yadda cikin Aunty zai zube

Yayin da ita kuma Umaisha ke ta fama da Aunty a asibiti, dan an karawa Aunty ruwa da kuma alluran zazzaɓi, dan sunce akoi zazzaɓi a jikin ta, yar aikin da Abbi ya kawo itace tazo ta goge wajen da Aunty tayi amai ta gyare wajen tsab.

Wanan kenan abun dake faruwa a gidan Abbi bari mu leƙa Daular mutuwa mu gani meke faruwa a can.

👹DAULAR MUTUWA👹

Lokacin da su Ayla suka tashi daga sumar da suka yi, sun sha kukan É—aukan Rimsha da akayi kamar ransu zai fita, baba da Mustapha ne suka yi ta basu hakuri, da kyar sukayi shiru, yayin da shi kuwa duna da kyar Queen ta yarda ta bashi ruwan tsafi su Barbushi suka bashi yasha kafafun sa suka koma kamar da, da farko Queen taki bashi ruwan tsafin nasu a cewar ta bata ga amfanin duna a gidan ba, sai da su Barbushi suka ta rokan ta sannan ta yarda ta ba shi, yana sha kuwa kafafun sa suka dawo dai dai, ya dawo bakin aikin sa wajen su Ayla kenan.
Chapter 106 · 0% Book details