← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 126

Sashe 114

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai gama tunanin sa ba muryan ta ta katse shi da cewa "Me yasa kayi shiru? Ka tsorata ne? To karkaji komai, amma dai ya kamata kasan wani abu guda, duk abubuwan da kayiwa Hanan jiya da daddare munyi audio recorded na voice naka, sannan duk wasu maganganu da kake mata a nan duk munyi recorded, dan kullun idan ka zo tana kunna karamar wayar ta tayi ta recording, so ina son ka sani idan ka sake dawowa cikin garin Katsina wlh sai na baza wannan recorded É—in wa duniya kowa yaji, kasan dai ba wanda bai san muryan ka ba ko? Dan kullun kuna hawa kaban mike kuyi ta shirgawa mutane karya, kowa ya sheda wannan É—an iskan muryan naka kamar na karuwar akuya, ka baro Abuja kana bin kauyuka kana lalata Æ´aÆ´an mutane, dan bakin iyaye na bin ka ko? To mu nan munfi karfin yaro sai dai baban yaro wato Salahuddeen Abubakar ina ga shine dai dai mu, wato yanzu kun dai na neman mata a manyan birane saboda gudun cututtuka, sai ku shiga kauye ku yau dari Æ´aÆ´an talakawa da sunan aure ku lalata musu rayuwa ku gudu ku barsu, wasu ma da ciki zaku gudu ku barsu, ayi ta haifan Æ´aÆ´an da basu da uba suna tashi cikin wahala da kuncin rayuwa, ba ilimin boko bare Arabic, da sun girma su zama yan shaye shaye dan ba ilimi, saboda ire iren ku zan zama yar sanda, duk sai naci Kutumar uban ku, na tarwatsa muku tunani yan iska banza" duk wannan magana tayi shine cikin harshen turanci

Tun da ta fara magana Farooq ya tsare ta da ido yake ta faman haɗiyar wahalallen yawu, sai zazzaro ido waje yake kamar wani ƙasurgumin munafuki, tunani yake wace ce Jehan, ai na kuma ta san shi farin sani haka, wayan nan tambayoyin duk ita ya dace yayiwa sai dai ba dama, dan cikin sa ya ɗuri ruwa, musamman da yaji sun yi recorded abubuwan da yayi ta faɗe a matsayin sa na kanin babban ɗan siyasa, idan wannan abun ya fita yake nan, gashi kuma ba wanda bai san voice na saba, wasu ma a media har tsokanar muryan nasa suke, saboda yana magana da sauri sauri kuma muryan tasa kamar na yar baby, irin munafukan muryoyin nan gare sa.

A ɓangaren su Sadiq da sauran yan anguwa kuwa, sun zubawa Jehan da Farooq ido, sun kasa kunne suna son jin me Jehan take faɗawa Farooq, sai dai basu samu damar ji ba, dan ƙasa ƙasa Jehan tayi maganar saboda ita da kan ta bata son fitina, bata son kowa ya gane wace ce ita, kuma da turanci tayi maganar.

A ruÉ—e Farooq ya shiga motar sa ya kunna, har lokacin yana kallon cikin idon Jehan yayin da itama take kallon cikin idon sa, sai dai Farooq ya kasa gane wace ce saboda fake face dake fiskar ta yasa bai gane wace ce ba, amma bashi da wani burin da ya wuce ya gane wace ce Jehan ai na kuma ta san shi, dan shi bai cika wani fitowa gidan Tv ba, sai dai ya taya yayan sa kanfen da muryan sa kawa, amma dai dayawan mutane sun san shi, sai dai ba kowa ya damu da fuskar tasa ba dan ba shi ne mai neman takarar ba yayan sane, tunani É—aya yake, ko ma wace ce Jehan makusanciya ce a gare shi dan wannan sanin da ta masa ba sanin wasa bane farin sani ta mi shi.

Ko uppan ya kasa cewa Jehan ya ja motar sa ya bar wajen yana tunanin ko dai kashe Jehan zai sa ayine, dan in wanna voice É—in nasa ta fita shikenan ya gama yawo yayan sa ma ba zai bar shi ba, da tuni fal ransa na ya zai yi da Jehan, ya zai yi ya kwace Audio sa dake hannun ta haka ya bar layin gaba É—aya tunani cike da ran sa, sai dai abun da bai sani ba ba wani recording da Jehan ta masa, kawai ta shirga masa karya ne dan ta ceci Hanan.

Bayan ya tafi ne Sadiq ya matso wajen Jehan, dan tana tsaye tana bin motar Alhajin da kallo har ya bar layin nasu.

"Jehan me kika ce masa haka, naga ya tafi da sauri kuma yana cikin tashin hankali har haka?" Cewar Sadiq, kamar jira Jehan take a mata magana ta juya da sauri ta wuce cikin gidan.

A zaure ta wuce su maman Sadiq sunyi cirko cirko suna leƙo abun dake faruwa, kai tsaye ɗakin maman Sadiq ta wuce, ta faɗa saman yar katifar maman Sadiq ta hau kuka kamar karamar yarinya.

Tashin hankali yau ga DPO Jehan tana kuka meke faruwa muje zuwa.

A tare Sadiq da maman sa suka biyo bayan ta, kusa da ita maman Sadiq ta zauna yayin da shi kuma Sadiq ya zauna ta bakin kofa, in da ya saba zama.

A hankali maman Sadiq ta shafa kan ta tana faɗin "Lafiya Jehan meke faruwa? Me ya saki kuka" ɗago wa tayi cikin kuka tace "Daddy na na tuna, Farooq ya tunamin da daddy na" ka san cewar su maman Sadiq sun san wace ce ita sai bata ɓoye musu waye Farooq ba da kuma abun da yake tsakanin su.

"Yayan Farooq yana ɗaya daga cikin abokan takarar daddy na, ya taɓa zuwa har gidan mu, sannan kuma akoi hotunan su a wayar daddy na sosai, na san Farooq nasan halin sa, duk yan gidan su na san su, da Farooq da yayan sa sun taɓa zuwa har gidan mu wajen daddy na" ta kai karshen maganar tare da sake fashe wa da kuka, sosai maman Sadiq da Sadiq suka shiga bata baki suna rarrashin ta, da kyar suka samu tayi shiru ta hakura.

Da sallama Hanan ta faɗo ɗakin da sauri taje ta rungumi Jehan, duk da zata girmi Jehan a shekaru amma sai tace "Aunty Nagode" shafa kan ta Jehan tayi murya a dashe tace "Ba komai Hanan" maman Sadiq ce ta tambaye su wai meke faruwa ne tsakanin Hanan da Alhajin nan, basu ɓoyewa maman Sadiq komai ba suka sanar da ita, sosai ta musu addu'ar kariya daga sharrin zina sai amsawa da amin suke.

Sannan Jehan da Sadiq suka fito suka nufi asibiti, dan maman Sadiq tace musu anyiwa mum aiki cikin nasara, amma har yanzu bata farfaÉ—o ba likitoci sunce zuwa gobe da safe zata farfaÉ—o, tun safe maman Sadiq na asibitin sai shabiyun rana ta dawo gida.

A tsakar gida suka wuce baban Sadiq da amarya, baban Sadiq yana zaune saman kujera yana tsinkewa amarya ganyen alayyaho zatayi musu miya, sosai Jehan ke jin haushin baban Sadiq kamar ta shake sa ya mutu kowa ya huta, wani kato da shi sai ya rinƙa biyewa yar amaryan nan tana sashi abubuwa kamar ƙaramin yaro.

Amarya da baban Sadiq É—in har suna haÉ—a baki wajen cewa "Sannun ku" ko kallon su Jehan bata yi ba ta wuce, shi kam Sadiq mamaki ne yake hana shi amsa sannun nasu, Allah sarki Sadiq bawan Allah bai saba ba, sai yaga abun kamar a mafarki.

Sunyi Sa'a suna fita suka sami taxin suka hau zuwa asibiti.

Mu koma muje mu leƙa su Umaisha wato gidan Abbi mu dawo sai muga ya jikin mum.

💞KADUNA💞

Sai karfe 4 na yamma sannan su Umaisha suka dawo gidan, ba laifi Aunty ta samu sauki sosai da sosai, taji kwarin jikin ta saboda ruwan da aka kara mata

suna shiga Palo Umaisha ta wuce bedroom nasu, ita ma Aunty nata bedroom É—in ta wuce, tana mai godiya ga Allah sanan tana yiwa Umaisha addu'ar fatan alkhari da fatan Allah ya tsare ta da tsarewar sa.

Umaisha na shiga bedroom nasu wayar ta ya fara kara, dogon tsaki taja kafin ta kalli Aafia dake baje saman gado tayi ɗai ɗai tana barci, a ƙule ta ɗauki wayar kamar zata sa ihu dan haushi.

Shiru tayi bata yi magana ba, shima Akil É—in shiru yayi bai yi magana ba, almost 5mins suna manne da waya a kunne ba wanda yace da É—an uwan sa uppan, da dai taga bashi da niyar yin magana sai tace "Hello" shiru yayi kamar ba zai amasa ba "Hello ina jin ka, kayi maganar da zakayi pls" ta sake faÉ—a tana hararar É—akin nasu kamar Akil É—in take gani a zahiri

Cike da wannan izzar nasa yace "Lallai dole na koya miki hankali har ni zaki cewa kina jina nayi magana na ba, tom ki shirya gobe zan yiwa Nigeria diran mikiya, da safiya ina garin Kaduna, kuma ina sauka ki sani gidan mijin ki zaki wuce" shiru tayi kamar bata ji me yace ba, yana sane tana jin sa sarai amma taki yin magana, katse kiran yayi zuchiyar sa na tafasa ji yake tamkar ya ganshi a gaban ta yanzu, ya karya ta ya zauna kuma yayi jinyar kayan sa, yana bala'i kaunar ta sosai, sai dai baya É—aukan raini ko kaÉ—an, shiyasa duk wani maganar da zai mata da umarni yake maganar.

Ita kuwa yana katse kiran tayi wurgi da wayar saman gado tana faÉ—in "Dan wahala kawai, Allah ya kai mu goben in ga karshen rashin kunyar taka, yaro man kaza, gobe zan diro Nigeria ina zuwa zan É—auke ki, eyee to sannu Sulman dan ba zance Abbi ba sai dai ince sannu baban Abbi" ta kai karshen surutan rashin kunyar nata tare da wucewa toilet dan tayi wanka, tun safe bata yi wanka ba, tana fama da Aunty a asibiti ti.
Chapter 114 · 0% Book details