← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 126

Sashe 17

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A ɓangaren jehan kuwa gudu gudu sauri sauri ta shiga gida babu ko sallama tun daga kofar gida take kwalawa mum kira da sauri mum ta fito daga cikin kitchen tana tabayar ta lafiya take kwala mata kira haka da sauri gwaggo dake zaune saman tabarma a tsakar gidan ta miƙe tana faɗin "Jehan are you okey?" A ruɗe Jehan tace "Mum yanzun nan kafin na shigo na haɗu da wancan dirty boy ɗin shi da wani dirty boy ɗan uwan sa kuma wancan ya gane ni har ya kira sunana da na daddy" waro ido waje mum tayi tana kokarin yin magana gwaggo ta riga ta da cewa "What? Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun what are we going to do now?" shiru mum ta ɗan yi kafin tace "Jehan as from today kar ki sake fita ko ina just stay at home" gwaggo ne tayi saurin taran numfashin mum da cewa "Hakan yayi daman duk cikin ku nice face na bai zama popular ba so zan rinƙa zuwa cefene da sauran su" girgiza kai mum tayi tana faɗin "A'a Aunty A'isha hakan kuma ba zai yiwu ba gaskiya dole dai mu samo mafita batun kije ki rinƙa yo mana cefene da kan ki kam bayyi ba" "Mum why not na rinƙa using face mark to?" "Gaskiya Aunty A'isha munyi ganganci tun farko da muka manta da waye mu, muka saki face namu ga kowa muka bar Jehan tana zuwa in da ta ga dama lokacin da take so" jinjina kai gwaggo tayi cike da tashin hankali da damuwa tace "Maryam ina ganin Jehan ta rinƙa using face mark ko kuma mu sai mata face na roba da zata ɓatar da kamanin ta ko ya kika gani?" Jinjina kai mum tayi tana faɗin "Duk yadda kika yanke yayi" dawo da kallon ta gwaggo tayi kan Jehan tace "Go and wear face mask and go to market buy fake face" cikin sauri Jehan ta wuce cikin ɗaki, ta buɗe trolley ta ta ɗauko face mark ta sanya ta fito ta wuce ta fice daga gidan ta nufi kasuwa, tana fita sukayi karo da Sadiq zai shiga gidan nasu ko kallon in da yake ba tayi ba ta wuce yana ce mata sannu ko kallon sa ba tayi ba ta wuce murmushi yayi shi ko kallon ta ma yayi daɗi yake ji tsayuwa yayi ya suba mata ido tana tafiya har sai da ta kurewa ganin sa san nan ya wuce ya shaga gidan bakin sa ɗauke da sallama zaune ya isko gwaggo a saman tabarma a tsakar gida ita kuma mum ta koma cikin kitchen dan ci gaba da aikin ta saman kujerar da Jehan ke zama ya zauna yana faɗin "Ina wuni gwaggo?" Da fara'a gwaggo ta amsa da "Lafiya ya kake ya gida ya maman ka" "Lafiya Lou Alhamdulila ina mum?" "Tana kitchen" gwaggo ta bashi amsa "To bari na jirata magana nazo muyi da ita ne" jinjina kai gwaggo tayi ba tare da ta sake magana ba mum na kitchen bata san da zuwan Sadiq ba yana zaune shiru ita ma gwaggo na zaune shiru har Jehan ta dawo hannun ta riƙe da leda kasan cewar kasuwar nasu bai da nisa da gida kuma ta hau abin haka ne wato mashin shi yasa tayi sauri dawowa ba ko sallama ta shigo gidan ganin Sadiq zaune saman kujera da take zama ne yasa taja guntun tsaki ta wuce kusa da gwaggo ta zauna tare da kwanto da kan ta saman cinyar gwaggo tana faɗin "My gwaggo I'm tired" shafa curly hair ta gwaggo tayi tana kokarin yin magana mum ta fito daga cikin kitchen tana faɗin "Har kin dawo Jehan?" Gyaɗawa mum kai tayi ba tare da tayi magana ba "A'a babana yaushe kazo" kasa yayi da kai yana murmushi "Yanzu nazo mum ina wuni" da fara'a mum ta amsa masa tare da karisowa wajen ta zauna gefen gwaggo saman tabarma "Mum daman ina son yin magana da ke ne idan ba damuwa" ba tare da ta kalli in da yake ba hankalin ta na kan Jehan tace "To babana in taso muje gefe ne?" Girgiza mata kai yayi yana faɗin "A'a a nan ɗin ma yayi" "To ina jin ka" nan Sadiq ya kwashe yadda sukayi da Nasir akan kidnaping da yake son Sadiq yayi join na shi ya sanar wa mum san nan ya ɗaura da cewa "Naga ku kunyi karatu kuna da ilimi boko da na islamiya shi yasa nake son ki bani shawara shin yin hakan abune mara kyau ko kuma dai kamar yadda Nasir ya faɗa ba laifi hakkin mu zamu ansa" cike da tashin hankali mum tace "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunallahu wani'imal wakil haka fa mutanen nan suke amfani da wayan da basu yi karatu ba kuma talakawa masu neman na abinci su cucesu su lalata musu duniyar su da lahiran su kayi kyan kai babana da kazo ka tambaya da wani ne yaji kuɗi haka zai faɗa halaka wa iya zubilla ni yanzu gashi ban isa da zuwa police station ba kuma bamu da hujjan report na shi da mun sa an kama shi wan nan babban laifi ne babana, wadda idan aka kama mutun yana aika tashi kashe shi ake har lahira shawaran da zan baka a rayuwar ka kawatsar da duk wani aboki kayi rayuwan ka daga kai sai ɗan uwan ka san nan da kai da ɗan uwan naka duk ku rinƙa zuwa idan kun samu time Aunty A'isha ta rinƙa koya muku karatun Arabic har ma da boko dan ku fita cikin duhun jahilcin nan jahilci babban ciwo ne babana, babban bala'i ne jahilci yanzu ba yace maka zai dawo gobe ba idan yazo kace ya kara maka lokaci karka nuna masa kayi maganar ma da wani kuma karka nuna masa bazaka ansa tayin nasa ba idan kayi kuskuren nuna masa hakan tofa zai iya maka wani illar koma ya kashe ka dan gudun karka tona masa asiri a kama sa kabi da taka tsantsan kana ja masa rai duk lokacin da ya kawo maka maganar kace yayi hakuri kai ma kana son sana'ar amma ya ɗan kara maka lokaci a haka har ka rabu da shi san nan idan yazo anguwar nan ka rinƙa ɓuya karka na bari kuna haɗuwa kowani lokaci karkuma karinƙa gudun sa sosai har yazo ya gane In Sha Allah hukuma zata kama shi" da sauri Sadiq yace "Hukumar da bata da adalci bata wani yi mana Aiki basa son gaskiya bayan masu kuɗi kawai suke bi" girgiza kai mum tayi kafin tace "A'a babana falyakul Kairan auli yasmut karka haɗa hukuma dukka ka musu kuɗin goro ba dukka suka taru suka zama ɗaya ba akoi na kirki kamar yadda a ko ina akoi na kirki da na banza suma hukuma haka suke idan kayi Sa'a ka haɗu da na kirki zaka ji daɗi, kuma zancen gaskiya hukuna na iya bakin kokarin su wajen ganin su gudanar da aikin su yadda ya dace wani lokaci abun ne yake fin karfin su amma suna kokari bance akoi wayan da basa aikin su yadda ya dace ba sai dai kasani su mutane ne ba Mala'iku ko aljani ba dole suna da a jizanci irin na ɗan adam wan nan shi ne kawai" ta kai karshen maganar tare da yin shiru tana kallon Jehan shiru wajen yayi ita dai gwaggo ta kasa magana saboda ganin abun take kamar a mafarki ita kuma Jehan bata ma san me suke cewa ba ta lumshe dara daran idon ta har barci ya fara ɗaukan ta can kome ta tuna tayi saurin waro dara daran idanun nata waje tana faɗin "Gwaggo this dirty boy he know everything about me because that stupid guy that talked about me is his friend they are together the time that the guy talked about me and dad" kallon Sadiq gwaggo tayi tace "Sadiq kasan wace ce Jehan yanzu ko?" Kasa yayi da kan sa kafin yace "Eh gwaggo" "Okey to kabar maganar iya tsakanin mu" jinjina kai yayi san nan ya miƙe yana faɗin "Mum Nagode sosai kuma zan yi yadda kika ce In Sha Allah" murmushi mum tayi san nan tace "To shike nan Allah yasa mufi karfin zuciyar mu" Amin ya amsa da shi san nan ya fice daga gidan miƙewa mum tayi ta nufi kitchen "Maryam ina son muyi magana a kan issue da Sadiq ya kawo yanzu" cewar gwaggo "To Aunty A'isha mu bari sai dare yanzu bari na ƙarisa girkin nan tukun nan" shiru gwaggo tayi bata sake magana ba ita kuwa Jehan barci ya ɗauke ta kan cin yar gwaggo.

💞💞💞💞💞💞💞💞
KADUNA
Chapter 17 · 0% Book details