Sashe 75
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jiki na kerma gwaggo ta ɗebo ruwa ta yayyafa mata, dogon numfashi taja tare da tashi a birkice tana faɗin "Ina Jehan dan Allah karku mata wani abun, duk abun da zaku mata ni ku min, dan Allah marainiyar Allah ce" turus gwaggo ta tsaya murya na rawa tace "Me kika ce Maryam? Marainiya kuma Jehan ɗin ce marainiya?" Sai lokacin mum ta dawo cikin hayyacin ta jin muryan gwaggo, a hankali ta gyaɗawa gwaggo kai kafin tace "Eh marainiya" a ruɗe gwaggo tace "ban gane marainiya ba kimin bayani" dogon numfashi mum taja tare da saukewa a hankali, cike da tashin hankali ta fara magana "Eh Aunty A'isha, tun ranar da yan sanda suka ɗauki daddyn Jehan, bai jima da tafiya ba yamin massage a kan cewa ba yan sandan gaske bane suka ɗauke sa haɗin bakine, abokan hamayya ne suka shirya masa hakan, kuma kashe shi zasuyi dan haka mu gudu, mu tseratar da rayuwar mu dan a halin yanzu ma, sun ɗauki hanyar Niger da shi kuma tabbas kashe shi zasu yi dan hakan suka shirya addu'ar mu kawai yake buƙata san nan kamar yadda ya faɗa min mu gudu dan muma ba zasu barmu ba saboda ba iya takarar sa suke so ba har da dukiyar sa, shi yasa da Shitu yazo yace mu tafi ban musa ba naje na ɗauko mana kayan mu dan mu gudu, tun da already daddyn Jehan ya sanar da ni, shi yasa ban takura Shitu a kan ya faɗa min ina daddyn Jehan yake ba, dan banson jin yadda suka kashe shi" murya na sarkewa sai haɗe words gwaggo keyi tace "To waya ce miki sun kashe shi? Da zaki fara kiran Jehan marainiya" "Sun kashe shi Aunty A'isha, sun kashe shi, dan in kika lura da yanayin da Shitu ya shigo gida a ranar, duka da gindin bindiga ce fa a goshin sa, shi da yabi daddyn Jehan daga baya ma kenan, kin ga kenan shima Shitu kashe sa suka so yi Allah yasa ya kubce musu yazo ya kubtar da mu, ba dan haka ba da dukkan mu mun mutu" jin mum tace an kashe daddy yasa Jehan fasa ihu ta sulale kasa sumammiya.
Mum da gwaggo har suna haɗa hannu waje rungumo Jehan ɗin suna kiran sunan ta a rikice, shiru Jehan bata motsa ba, zaro ido mum tayi ta fara hawaye tana faɗin "Shi yasa naki faɗa muku tun da jimawa Innalillahi wa inna ilaihir rajiun dan Allah Jehan ki tashi" ita kam gwaggo ta kasa magana abubuwan sun haɗu sun cushe mata waje guda, ta rasa ina zata sanya rayuwar ta taji sanyi a ranta, kan ta sai sara mata yake duniya na juya mata wani irin duhu take gani yana gelmawa ta cikin idon ta wannan wace irinyar masiface, ita kuwa mum kokarin danne abun take dan bata son abubuwan su mata yawa ta samu matsala ko dan saboda Jehan zata yi kokari ta danne da ta kula da ita, sai dai abubuwan sun mata yawa ga rasuwar daddy ya dawo mata sabo ga ɓatan Rimsha yanzu kuma ga Jehan, ta yanke jiki ta faɗin.
Duk yadda mum ta kai ga son ta danne abun ta kasa nan take taji zuciyar ta na harbawa da karfi karfi kamar zai fasa kirjin ta ya fito waje, lokacin guda taji kan ta ya mata nauyi, wani irin duhun ta gani ya kilma mata a cikin idon ta, kamar fanka haka taga duniya na juya mata, idon ta ya fara ganin mata daddy na kiran ta, kan tayi wani yunkuri ta zube kasa rungume da Jehan a kirjin ta, ihu gwaggo tasa kamar zararriya haka ta bazama Kitchen ta É—ebo ruwa a kofi tazo ta zuba musu a kan su.
Dogon numfashi Jehan taja tare da sauke wa a hankali kafin ta fara kuka, yayin da ita kuma mum ko motsi bata yi ba, kara É—ebo ruwa gwaggo tayi ta zuba mata nan ma shiru ba ta motsa ba, jijjigata gwaggo ta fara yi tana kiran sunan ta, amma ina ko motsi bata yi ba, sosai Jehan ke kuka tana kiran mum yanzu ta bar ta batun daddy ta koma kiran mum dake gaban ta.
Sadiq yazo zai shiga gidan su Jehan dan yaje ya É—ebawa su mum ruwa kenan Yusuf ya kwala masa kira ta bayan sa, da sauri ya juya yana kallon Yusuf É—in "Yaya Sadiq ina zaka je? Kazo muje mu gaishe da Fadil yanzu kanin sa ke faÉ—a min wai ya samu karaya a kafa jiya da daddare a wajen hanyar sa ta dawowa gida" zaro ido Sadiq yayi yana faÉ—in "Allah sarki to kaje ina zuwa bari na É—ebawa su mum ruwa" to Yusuf yace tare da wucewa ya nufi hanyar gidan su Fadil, shi kuma Sadiq ya shige cikin gidan su Jehan.
Ganin gwaggo da Jehan na ta kuka suna kiran sunan Mum dake kwance a kasa bata ko motsi ne yasa Sadiq karisawa wajen da gudun gaske yana faɗin "Lafiya me ya same ta" tsabar ruɗu da tashin hankali Jehan bata san lokacin da ta riƙo Sadiq ba, cikin fitar hayyaci take faɗin "Dan Allah dirty boy ka taimaki mum ɗina karka bari ta mutu please" kasa motsawa Sadiq yayi saboda irin riƙon da Jehan ta masa gaba ɗaya yaji sa wani iri ta kashe masa jiki, ita kuwa sai jijjiga shi take tana kiran "dirty boy ka taimaki mum ɗina" sai da gwaggo ta janye Jehan ɗin daga jikin Sadiq ta rungume ta sannan Sadiq ya samu dama ya iya juyawa ya fice daga gidan, yaje ya kira ɗan sahu.
Har kofar gida mai a daidaita sahu yazo, Sadiq ya kira maman shi tazo ta taya gwaggo suka ɗauki mum suka sata cikin a daidaita sahun, gwaggo da maman Sadiq suka shiga a daidaita sahu suka riƙe mum ɗin, shi kuma Sadiq ya riƙe hannun Jehan dake ta faman kuka yace mata suje bakin hanya su tari wani a daidaita sahun subi bayan su tun da wannan ba fili, ba musu Jehan ta bishi sai kuka take kamar ranta zai fita,
Wani a daidaita sahu Sadiq ya tara musu suka shiga gidan baya, sai kuka Jehan keyi suka bi bayan su mum.
Ko da suka isa Hospital É—in an rasa wa zai biya mai a daidaita sahu kuÉ—in sa sakamakon babu wanda yake da kuÉ—i a jikin sa, ganin haka mai a daidaita sahu da ya É—auko su mum yace ya yafe musu, shi kuma wanda ya É—auko Jehan da Sadiq yace a'a shi da ba zai yafe ba kawai a biya sa hakkin sa san nema ya fito ba taimako ba, a wannan marra da wahalar rayuwa da jama'a ke ciki ko biyar ba zai iya yafewa wani ba saboda shi family man ne, sai zare ido Sadiq yake dan bashi da ko biyar, while su kuma su gwaggo sun shige da mum ciki Jehan ma tabi bayan su, sun bar Sadiq tare da yan sahu, sai faman sosa kai yake yana zare ido, ganin haka yasa É—an sahun da ya É—auko su mum ya biya wancan É—in, sai godiya Sadiq ke masa, yace "Kar ka damu abokina Allah dai ya bawa mara lafiyar ku lafiya, ai talauci bata hana ka taimaki wanda yafika bukata idan kana da hali, talauci ba hauka bane Allah dai yasa mu dace Allah ya mana karshe mai kyau" Amin Sadiq ya amsa dashi, sai zuba godiya yake har É—an sahun ya tafi.
Sai bayan É—an sahun ya tafine Sadiq ya tuna basu rufe gidan su Jehan ba sun bar ko ina a buÉ—e, sosai tashin hankali ya bayyana a kan face É—in sa kar a shiga a musu sata, da yar gudun sa ya shiga cikin hospital É—in dan yaje yaga halin da mum take ciki sai yazo ya koma ya rufe musu gidan.
Zaune a saman benci ya isko su gwaggo sun zaunar da mum suna zazzaune suma, cike da mamaki yace da manan sa "mama ina likitocin kuma? Ya baku shiga ciki ba" kamar maman Sadiq zatayi kuka tace "wai sai mun yanki kati, Jehan taje yanko mana" shiru Sadiq ya É—an yi kafin yace "To mama bari naje na rufe musu gidan dan mun ruÉ—e mun tafi munbar gidan ko ina a buÉ—e" zaro ido waje maman sa tayi tana faÉ—in "Kayi sauri babana innalillahi kash munyi ganganci Allah dai yasa ba baun da zai faru, Allah ya kau da idon masu dogon hannu kayi sauri kaje ka rufe musu" dai dai lokacin Jehan ta dawo tana faÉ—in "Wai katin sai da kuÉ—i" gwaggo ce tace "Ina ATM naki ki basu su cire mana" da sauri Jehan ta wuce face nata sanye da fake face tana faÉ—in "ATM É—in yana gida bari naje na É—auko" da sauri Sadiq yabi bayan ta dan yasan ba sanin hanya tayi ba, yayin da ita kuwa mum take ko mutuwa tayi ne oho ba wanda ya sani, gashi likitoci sunki kulata wai sai an yanki kati sannan su bi layi wajen ganin dr kafin ma a yanke musu hukuncin ko gado za'a basu ne ko magani.
A ɓangaren su Jehan kuwa a daidaita sahu Sadiq ya sake tara musu suka shiga suka koma gidan su Jehan ɗin.
Kai tsaye É—akin Jehan ta nufa, ba shiri taja birki tana ganin yadda a ka watsa musu É—aki an zubar mata da kayan ta dake cikin trolley dukka, har kayan dake cikin bayi ba'a bari ba an watsar, kasan cewar tana sauri ne yasa ta zura hannun ta cikin aljihun trolley É—in ta dake yashe a tsakar É—akin, ta É—auko ATM card nata, haka ta bar É—akin a watse ta nufi hanyar fita
Har ta kai bakin kofa sai ta juyo wai bari ta É—auki wayar ta, da mamaki sai bata ga wayoyin ba dukka biyu, daga nata har na Rimsha, kasan cewar sauri take yasa bata wani tsaya neman wayoyin ba ta wuce ta nufi bedroom na mum dan ta É—auko ATM card na mum ta haÉ—a da nata ko da kuÉ—in account nata ba zai isa ba, dan ba wani kuÉ—in kirki ya rage a account É—in nata ba.