← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 126

Sashe 103

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan take James ya sha jinin jikin sa, dan kuwa yasan me Romeo ke wa mamaki, kwata kwata ya macen da ina yake shiyasa ya harbe kwalaben, kuma yasan wanna horo ne mai wahala, dan sai da yayi wata biyu yana koya kafin ya iya, dan ma yana da ƙwaƙwalwa da basira shiyasa yayi saurin iyawa.

Cikin sauri ya kawar da kan sa daga kallon Romeo ya fasa zaman da zai yi ma, dan dama yazo ne ya sanar da Romeo zai je party a New York kuma ba zai dawo ba sai gobe karsu neme sa, a zahirin gaskiya kuwa Meeting na su na criminals zai je.

A nitse ya sanar da Romeo zai je party, shiru Romeo ya masa har lokacin bai É—auke blue eyes nasa daga kan James É—in ba, ganin haka yasa James ya sauka daga wajen ya nufi hanyar fita daga wajen yana faÉ—in sai ya dawo, cikin sauri Michael yace "wait for me I want to go to White House so mu fita tare kawai" shi dai Romeo ido kawai ya zuba wa James yana kokarin fahimter wani abu, tunani yake ai na James ya iya wanan harbi haka

Kasan cewar baya yi musu tambayoyi a kan abun da ya shafe su, sai yayi shiru bai tambayi James É—in ai na ya koyi har bi ba, idan ya ga wani abun da bai masa ba a tattare dasu bincike kawai yake da kan sa gani, baya tambayar su, har suka fice daga wajen bai dai na kallon suba.

Sai bayan sun tafi da jimawa sannan ya miƙe ya bar wajen shi ma, ya koma cikin gida.

Michael kuwa, suna fita kai tsaye white house ya wuce, dan yau yace bari ya kaiwa president ziyara, tun daga bakin gate bodyguard da sojojin dake tsaron white house suka fara sara masa, ko kallon in da suke bai yi ba, da wata Winter Sports Hat nasa da yansa a kan sa, saboda yawan gashin kan sa, sai hat É—in tayi masa katuwa a kai.

Kai tsaye cikin ya wuce bai bi ta kan kowa ba, da fara'a President ya tare sa, sai turɓune fuska Micheal keyi kamar wadda aka sa shi zuwa dole, shiko president sai daɗi yake ji, saboda murna ya rasa ina zai sa Michael, saboda kaunar da yakewa GAR ne ya shafi su Michael, yana son family William jacop sosai, kasan cewar kakan su Romeo jacop Roshan babban ɗan siyasa ne kafin ya mutu, shiyasa suke da damar shiga ko ina a kasar ba wata shamaki sai ma girmamawa da suke samu daga manya manyan yan siyasa masu tasowa yanzu.

Wata dankareriyar diamond watch mai bala'i kyau da tsada president ya É—auko ya bawa Michael kyauta, first time da Michael ya cire diamond watch na su na Triplets ba barci zai yi ko wanka ba, kuma ya cire ne dan ya sanya wanda president ya bashi, saboda ya nunawa president yaji daÉ—i.

Sosai president yaji daÉ—in abun da Michael É—in ya masa, na cire diamond watch na su na Triplets da yayi ya sanya wadda ya ba shi, sosai agogon tayiwa Michael kyau kamar dan hannun sa a kayi ta, sanya diamond watch nasu na Triplets yayi a aljihun jacket nasa ya bar na president É—aure a hannun sa, suka ci-gaba da hira kamar wasu friend, bayan kuma president ya kusa jika da Michael, amma saboda son da yake musu, sai ya zama kaman friend nasu idan suka zo wajen sa.

Shi kuwa James kai tsaye wajen taron su ya nufa, a in da zasu gudanar da taro cikin dajin palace, a nan zasuyi taron, manya manyan criminals uban nin gidan su James sun hallara, sun zauna sai hira suke suna jiran saukowar sauran jiga jigan ogannin nasu, sai a fara taron.

Shi kuwa Romeo yana kwance saman lallausan katafaren gadon sa, yayi kwanciyar rigingine ya tasa system a gaba yana bawa yaran sa dake shirin tafiya yaki umarni, sai faman lumshe dara daran blue eyes nasa yake kamar mai jin barci, ga daddaÉ—ar kamshin air freshener da sanyin Ac dake ta faman tashi a bedroom É—in nasa, gaba É—aya wutar É—akin nasa ya kashe farin wutar ya kunna sky blue, sky blue light É—in ba karamin karawa É—akin nasa kyau yayi ba, abun gwanin ban sha'awa da É—aukar hankali.

A ɓangaren TGA kuwa, sosai wayan nan kwari suka masa illa, dan kuwa a kan gaban sa suka matsa wanna tsiyar, wajen ya kunbura sosai yayi jawur kamar jini ne a ciki, duk jarunta irin na soja sai da TGA yayi kuka, saboda ciwo a irin wanna waje ba karamin abu bane, yana da zafi sosai over, Allah sarki bawan Allah ko wando baya iya sawa saboda azaba, ga sanyi Ac amma duk da haka sai daddy ya kunna rechargeable fan ya kawo masa sai tin gaban nasa yana shan iska saboda azaba, shi kaɗai kwarin suka yiwa irin wanna lahani mai muni sosai haka, duk wannan hali da TGA ke ciki Romeo bashi da matsani dan yana can ya nitsa cikin aikin da yake.

Mu leƙa Jehan mu dawo

💞KATSINA💞

Yau ya kama Monday, tun 8 na safe a ka shiga da mum ɗakin da za'a mata aiki, while ita kuma Jehan ta shirya tsab cikin wata dakakkiyar atamfan ta super wax mai bala'i kyau ɗinkin riga da skit, kayan sun zauna a jikin ta sosai, sunbi shape ɗin coca colan ta sun mata ɗas, kasan cewar bata son ɗankwali ma bare hijabi hakan yasa ta ɗauki ɗan karamin Malaysian hijab ɗin ta pink color tare da takalmi pink color, ta ɗauko jakar ta suwaga shi ma pink color ta fito tsakar gida, ba karya duk da cewa fake face ne a fuskarta ba ƙaramin kyau tayi ba sai kamshin sauran perfume da ya rage mata take.

Kai tsaye kitchen ta nufa wajen maman Sadiq, suka gaisa sanna maman Sadiq ta mata addu'ar fatan fara aiki a Sa'a, yar murmushi tayi ta amsa da amin sanna ta fito daga kitchen É—in da sauri saboda hayaki.

Tana fitowa sukayi karo da Sadiq yana kokarin shiga kitchen ɗin, ɗan baya kaɗan tayi tana faɗin "Good morning" zuba mata ido yayi yana kallon ta yana mai kara jin kaunar ta a ransa, tab lallai ita kuwa Jehan babu wani abu wai shi soyayya a ranta, bata san shi ba, kuma bata da wani ra'ayi a kan soyayya, ita da namiji da mace duk kallon abu guda take musu, namiji baya gaban ta, maza basu isshe ta kallo ba, kai har matan ma ita a wajen ta basu isshe ta kallo ba, bata taɓa kawo wani abu wai shi tunanin aure ma a rayuwar ta ba, a nata wautan har ta mutu dasu mum ɗin ta kawai zata yi rayuwa.

Ganin Sadiq ya zuba mata ido ne yasa ta raɓa gefen sa zata wuce, cikin sauri yace "Jehan dan Allah ki koma ki cire kayan nan ki sanya uniform da suka baki karki ja su hana ki aikin nan, kuma kinga dai akoi bashin kuɗin aikin mum a kanki ta wanna aikin ne kawai zaki iya biyan bashin da ake binku, to dan Allah karkiyi sanadin rabuwar ki da aikin nan kar kiyi wani kuskuren da zasu kore ki daga wanna aiki" ba tare da ta kalle sa ba, a takaice tace "I can't wear this uniform" girgiza kai Sadiq yayi kafin yace "Kiyi hakuri ki sanya jehan" cike da izza tace "Babu wanda ya isa ya zaɓa min abun da zan yi a rayuwa ta, ba zan sanya wani banza uniform nasu ba, ai ba sayata sukayi ba da zasu ce abun da suke so zanyi, ni Jehan babu wani da ya isa ya min iko da rayuwa ta bayan dad and mum, ko gwaggo lallaɓani take in tana son nayi abu, so kayan nan nayi niyar sawa babu kuma wadda ya isa ya sanya na canza" ta kai karshen maganar tare da sa kai ta nufi hanyar fita daga gidan.

Dawo da kallon sa Sadiq yayi kan maman sa dake tsaye a cikin kitchen ta zuba musu ido tana kallon ikon Allah "Ina kwana mama?" Ya faÉ—a yana sunkuyar da kai, dan yaji kunya ashe mama na tsaye tana kallon sa yadda ya zubawa Jehan ido, da fara'a maman sa ta amsa masa.

Bayan sun gaisa ne ya mata sallama ya wuce yabi bayan Jehan, sai addu'a mama ke musu da fatan alkhari, yana amsawa da amin amin ya wuce.

A ɓangaren Jehan kuwa tana fitowa wajen gidan tayi karo da baban Sadiq yana shigowa, ko kallon in da yake ba tayi ba ta wuce, zata wuce shi ne yace "Sannun ki yarinya" yauwa kawai tace masa ta wuce tana ɗaure fuska kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, dan haka kawai taji ta tsani baban Sadiq ɗin nan bata son shi, kawai tana masa karane saboda Sadiq.

Jehan uwar dirama ta koyawa baban Sadiq da amarya hankali, yanzu amarya har gaishe da su Maman Sadiq take da safe, kuma yanzu sun É—an samu zaman lafiya da fitinar amarya, ta daina takurawa kowa dake gidan, ta shiga hankalin ta da kyau saboda tsoron aljanu, wanna shine idan baka yi sharan masallaci ba kayi na kasuwa, duk iskancin ka akoi baban ka.

Jehan zata wuce ta nufi bakin hanya ne, sai taga Hanan zaune gaban murhun gawayin ta na tuyar awara ta kifa kai da gwiwa tana kuka, da kamar ba zata kula taba zata wuce dan ita ba mai shiga harkan mutane bane, idan kuma ka kuskuren shiga nata harkan sunan ka sorry, dan Jehan ba sauki.

Kasan cewar Hanan yarinya ce so silent bata da hayaniya kuma bata neman magana hakan yasa Jehan ta matso kusa da ita tare da dafa kafaÉ—ar ta tana faÉ—in "Ke lafiya kike kuka haka?" Yar firgigit Hanan tayi tare da É—ago kan ta idon ta sunyi jawur kamar jini saboda kukan da tasha, "Subhanallah lafiya kikayi irin wannan kuka haka?" Cewar Jehan tayi maganar tana tsugunnawa kusa da Hanan É—in, dai dai lokacin Sadiq ya fito.
Chapter 103 · 0% Book details