← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 126

Sashe 100

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa Abbo yayi, yayi kwanciyar rigingine yana fiskantar Jelly, ya zuba mata ido yana ta kallon ta daga sama har kasa, yana son taɓa ta yana kuma tsoron kada ta masa ihu ko ta tashi Hajiya daga bacci, dan yasan halin Jelly sarai ba'a mata abu tayi shiru, kana mata abu da ɗumi ɗumin sa zata faɗa wa Hajiya ba ɓata lokaci, tunani ya fara yi ya zai yi, dan shi gaskiya yana matikar son Jelly, sai kallon ta yake ita kuma tana kwance ta rintse ido amma ba tayi barci ba, dan ga idon nata nan sai motsi suke, wutar ɗakin a kunne yake dan Jelly bata zama a ɗaki sai da wuta a kunne, tana tsoron duhu, wani lokaci sai tayi barci hajiya ke zuwa ta kashe mata wutar, amma fa idan ta tashi cikin dare, to akoi dirama dan ihu take kamar zatai hauka, da kyar ake lallaɓa ta ta mai da barci, ta hanyar kunna mata wutar ɗakin.

Ahankali ya kai hannun sa zai taɓa ta, sai kerma hannun nasa keyi kamar mazari, ya kasa taɓa ta, yana son taɓa kuma yana tsoron tsiwarta, sai dai abun da bai sani ba, yanzu Hajiya tace duk abun da Abbo da Nawid suka ce mata tayi to tayi shi, kuma ita Jelly duk abun da Hajiya tace tana yin sa ba ɓata lokaci, sannan in dai Hajiya tace tayiwa wani biyayya tofa kome zai mata ba lallai ta faɗa wa Hajiya ba, tun da Hajiyar ce tace tayi.

Haka Abbo yayi ta kokarin taɓa Jelly yana tsoro, har barci ya ɗauke Jelly, haka ya zauna ya zuba mata ido yana ta kallon ta, yana kara jin haunar ta a ransa.

Sai wajen 1 na dare sannan barci ya ɗauke sa, yau kasan cewar Hajiya ta rigasu yin barci, sai Abbo bai ce ta tashi ta kai Jelly bedroom nata ba, dan shima hakan yake so Jelly ta rinƙa kwanciya kusa da su, shi yasa ma baya wani damuwa wajen sa Hajiya ta koya mata kwana ita kaɗai a ɗaki, shine ma mai kara injiza abun, da Jelly ta fara cewa bata so, sai ya wani ce a'a a barta tun da bata so kar a wani takura mata, shi ya fara kawo shawarar tun da tana tsoron kwanciya ita kaɗai to su rinƙa kwanciya da ita sai tayi barci su ɗauke ta su mai da ta bedroom nata, insert of ya sanya Hajiya ta koya mata kwana ita ɗaya, sai ya kara dagula komai dan shima yana ra'ayin hakan. A ranar dai a ɗakin su Jelly ta kwana.

Mu leƙo Rimsha mu dawo

👹DAULAR MUTUWA👹

Yanzu dai ba laifi shakuwa ta shiga tsakanin Rimsha da duna, sai dai ita Rimsha tana biye masa ne kawai bisa umarnin baba na cewa ta biye masa har Allah yasa ya musulunta imani ya ratsa shi ya daina shan jini da sauran su, wannan dalilin yasa take biye masa, yanzu har zama take suyi ta hira, yana mata tambayoyi a kan addinin Musulunci tana bashi amma with her confidence, dan ita ma tana burin ya shiryu ya musulunta ya dai na duk wani abun da yake ya koma ga Allah, sai dai kullun in zata bashi amsa a kan addini, sai Queen ta shaƙe ta, tayi ta fama har sai duna ya taimaka mata, kasan cewar shi ma irin sune, da jikin sa ya haɗu da nata kaɗan, tofa dole su sake ta.

Yauma kamar kullun suna zaune saman bencin duna suna hira, shi kuma yana zaune daga É—an gefe da su, saman wata kujera da ya bayyanar da ita da tsafin sa, yanzu baya zama kusa da su sosai a É—an gefe yake zama, saboda sun faÉ—a masa a addinin musulunci ba'a yin haka, saboda son da yake wa Rimsha yasa yake girmama addinin ta da kuma dokokin addinin nata.

Sai hira suke ita da su Ayla cikin nishaɗi, yau basu je wajen baba ba, sun zauna wajen, zuba musu ido kawai duna yayi yana kallon yadda Rimsha ke ta murmushi kyakkyawan dimple nata yana lotsawa gwanin ban sha'awa hakan ba karamin kyau yake karawa face nata ba, daman abu huɗu zuwa biyar ne a face ɗin Rimsha da yafi ɗaukan hankali duk wanda yayi ido huɗu da ita, na farko wayan nan kyawawan dara daran sleeping eyes ɗin nata farare kal kamar audiga, ba karamin tafiya da imanin ɗan adam suke ba, kasan cewar idon nata yayi daban, sai ka tara mutane sama da dubu baka samu biyu masu irin wanna idon ba, shine babban abun da yafi jan hankali mutane a face nata, na biyu kyakkyawan dimple nata, idan tana murmushi ko tana magana, ko baka son ta sai ka tsaya ka kalleta, saboda dimple ɗin nan, ba karamin kyau yake kara mata ba, ɗan siririn open teeth, dake tsakanin hakwaran ta da suke farare kal a baya amma yanzu saboda da hannu take brush babu brush hakan yasa hakwaran nata suka rage haske, amma still suna da hasken sai dai ba kamar lokacin da suke tare da daddyn su ba, abu na huɗu ɗan bakin ta, wow idan tana magana abun sai wanda ya gani, laɓɓan ta na sama design of heart ne ga bakin nata ɗan karamin dashi launin pink color kamar wadda ta sanya lipstick, hancin nan nata har baka ɗan siriri kamar karas Masha Allah, ga bakin saje kwance a gefen kumatun ta.

Sai hiran su suke duna ya tsare su da ido, can kome ya tunan ya miƙe yazo ya tsugunna a gaban ta, tare da zuba mata ido a hankali yace "Me yasa idan kuna magana kuke yawan sanya Annabi Muhammad? Waye shi?" Dawo da kallon ta kan face nashi tayi cikin nitsuwa tace "Shi ne Babban abun soyuwa a gare mu, kuma shine annabin karshen da baba ya faɗa maka ranar, duk wani cikakken musulmi yana son Annabi Muhammad" "eh nasan kuna son shi kam dan baku magana ɗaya biyu baku kira shi ba" yar murmushi Rimsha tayi kafin tace "Saboda son da muke masa ne yasa har a zamanin baya kafin yazo duniya ya samu takwara dayawa, sosai jama'ar zamanin da kafin yazo suka masa takwara" zaro ido duna yayi kafin yace "To bai zo ba kuma ya akayi suka san shi har suka masa ta kwara? Waye ya faɗa musu sunan shi da har zasu masa takwara? Bayan ni nasan sai an haifi yaro ake sanin sunan da za'a sa masa" ɗan kawar da idon ta tayi daga kallon sa kafin tace "Annabi Muhammad (SAW) an san shi ne tun kafin a ganshi, kuma an sanshi ne tun kafin a haife sa, domin yazo a littafai da dama, sunan sa ya bayyana a littafai irin su attaura, injila, zabura, so already wayan nan littafai sun bayyana zuwan sa da sunan sa da yanayin da zai zo, da kuma in da zai bayyana, waye shi da sauran su, shi yasa jama'a suka rinƙa masa takwara saboda son da suke masa, muma yan zamanin yanzu muna kaunar sa fiye da rayuwar mu, ni kullun cewa ma nake da azamanin sa a ka haifeni dana more" shiru duna ya ɗan yi kafin yace "Kwarai kuwa na san kuna son shi, nima shaidane dan kuwa akoi wata mata dana taɓa shanyewa jini a kasuwa, lokacin na riƙeɗe na dawo kamar yadda kika ganni yanzun nan, na shiga cikin mutane, a kasuwa na ga matar tana sai da kaya, kawai naji ina son shanye jinin ta, to lokacin akoi wata waƙa da ta kunna suna faɗin annabi kwarai kasan gaibu, na kasa manta wannan wakar ita kan ta matar na kasa mantawa da ita, ban san ya akayi ba ita ce mutun na farko dana taɓa shan jinin ta dana kasa mantawa, bayan na sha jinin nata sai naji ban ji daɗi ba, har yanzu na kasa mance ta" jinjina kai Rimsha tayi har idon ta ya kawo ruwa saboda tausayin matar a hankali tace "Baka kyau ta ba, amma dai karka ɗauka abun da suke faɗe a wakar gaskiya ce, domin Annabi bai san gaibu ba, dalili kuwa shi da bakin sa yace bai san gaibu ba, a lokacin da sayyidina Abubakar ya tambaye sa yaushe za'a tashi kiyama, sai yace wa sayyidina Abubakar sanin gaibu sai lillahi shi bai sani ba, Allah ne kaɗai ya san ranar tashin Al kiyama, kaga kenan idan da annabi yasan gaibu da muma mun san lokacin da za'a tashi kiyama dan da zai faɗa wa sayyidina Abubakar, shi kuma zai ruwaito mana hadisai, abu ɗaya ne yasa mutane ke ganin kamar annabi yasan gaibu, shine mafi yawancin lokaci Allah yana masa wahayi mala'ika Jibril yazo ya faɗa masa Allah ya bawa wanna sahabi aljanna, ko kuma Allah ya saukarwa wannan sahabi wata ni'imar, to idan mala'ika ya isar masa da wanna wahayi, shi kuma sai ya sanar da Sahabban sa, hakan yasa mutanen mu na yanzu suke ganin kamar annabi yasan gaibu tun da yana faɗin abubuwan da basu kai ga faruwa ba, kamar dai yadda ya bayyana Allah ya baiwa su sayyidina Abubakar aljannan tun suna raye, shi yasa rashin fahimter ce kawai da mutane ke samu, mafi yawancin mutane suna kan dai dai bisa nasu fahimter, basu kauce hanya ba kawai basu fahinci abun dai dai bane"

hannu ya kai zai shafi kumatun ta, sai kuma ya fasa, cike da kaunar ta yace "To ni dai gaskiya addinin ku yana burgeni, ta in da kuma yake burgeni in da akace matar ka kai kaɗai zaka taɓa ta ba wanda zai taɓa maka ita, wannan abun yamin daɗi sosai, addinin akoi tsabta sosai, kinga a baya zamu kwanta da duk macen da muke so, kuma ina da tabbacin kafin mu wasu sun kwanta da ita, hakan tsam ba tsari, ace mace ɗaya maza dayawa suyi ta kwanciya da ita abun ba ɗaɗi, amma addinin ku yayi hani da wanna gaskiya naji daɗi kuma na jinjinawa addnin nan naku" cool murmushi ta saki taji daɗi duna ya fara yaba addinin musulunci, da alama ya fara hawa kan hanya ma dai'dai ciya hakan ba karamin farinciki ya sanya su ba, dukkan su har da su Ayla.
Chapter 100 · 0% Book details