Sashe 93
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Manya manyan karafuna Romeo ya sanya su ɗagawa masu bala'i nauyi, haka ya sanya jibga jibgan sojojin sa suka ɗaura musu wayan nan mayun karafuna a kan su da kuma hannayen su, sannan Romeo ya sanya su suyi tsayuwar sojoji, idan sukayi kuskuren sakin karfe ɗaya, to fa a kafar su zai faɗa musu, sai ya musu daga daga da kafa, saboda nauyin sa da girman sa, sai ya fashe musu kafa tsab, haka suka hakura suka riƙe karfen nan da iya karfin su na karshe, gashi Romeo yace tsayuwar 1h zasuyi a wajen, tuni Michael ya fara kuka, wi, wai, wi, kamar ƙaramin yaro, har da majina, ya saki ɗan karamin bakin nan nasa yana zubar da yawu ga majina ga hawaye, gwanin ban tausayi, shi kuwa James sai haɗa zufa yake amma bai yi kuka ba, kasan cewar ya samu ire iren wannan horo daga wajen ogannin sa.
Romeo ganin kukan Michael na neman É—aga masa yankali ne yasa ya É—auko Bluetooth ya sanya a kunnen sa, ya mai da kan sa kan screen É—in wayar sa, ya daina kallon su, shi kuwa Michael sai kuka yake ya kasa shiru.
Gaba É—aya tausayin Michael ya hana James samun nitsuwa, ji yake kamar ya sanya sojojin dake kewaye da su suna gadin sun nan, su ansa karafunan Michael su kara masa, su bar Michael ya koma ya zauna ya huta, sai dai kuma bai isa yayi hakan ba kasan cewar Romeo ne ke basu horon da kan sa.
Masu fi 30mins da fara tsayuwar ba, jikin Michael ya fara kerma, ya kasa tsayawa waje guda, kan kace me ya fara tangal tangal, gashi kuma idan ya faÉ—i kasa karafunan nan suka danne sa, sai dai wani ba shi ba dan mutuwa zai yi, Romeo kuwa ya sanya Bluetooth a kunnen sa hankalin sa na kan waya, bai san meke faruwa ba, su kuwa sojojin basu isa suyi wani abuba idan ba Romeo ne ya basu izini ba, koda kuwa faÉ—uwa Michael zai yi ba su isa su tare sa ba sai dai in Romeo ya basu izini.
Tafiya gaba ɗaya Michael yayi zai zube kasa, kamar wani walkiya haka Romeo ya miƙe ya tarosa yayin da wayan nan jibga jibgan sojojin suka ansa karafunan hannun sa a sukwane, rungume Micheal Romeo yayi, da kyar da kyar Michael ke mumfashi, nan take jikin sa yayi ya ɗau zafi over kamar wuta, sai kerma jikin sa keyi kamar ba lafiya ba, da hannu Romeo yayiwa sojojin nuni da su karɓi karafunan hannun James karya faɗi shi ma, a sukwane suka karɓawa James ɗin, da Romeo yayi niyar idan suka gama part two zasu wuce part three, dan yana son ya horasu da kyau, sai dai kuma ina hakan ba zai yiwu ba saboda Michael.
Cak ya É—auki Michael saman kafaÉ—ar sa suka wuce cikin gida, da kyar James ke jan kafa yabi bayan su, sai faman haÉ—a zufa yake yaji wuya sosai.
Saman katafaren bed nasa ya kwantar da Michael ya fara duba sa, yana mai jin ba daÉ—i a ran sa, James kuma bedroom nasa ya wuce dan yaje yayi wanka ya huta.
Mu leƙo Nigeria mu dawo
💞NIGERIA💞
A ɓangaren Hajiya da Jelly kuwa, Hajiya dai taga ikon Allah iya ganin idon ta, dan kuwa duk in da taje sai Jelly ta bita, taki yarda ta zauna ita kaɗai, har toilet idan Hajiya ta shiga sai Jelly ta bita, Hajiya na son tayi wanka amma ba hali dan kuwa Jelly dai taki yarda ta zauna ita kaɗai, ko abinci Jelly bata ci da hannun ta sai dai a bata a baki, daga karshe dai Hajiya da taga ba zata iya da Jelly ba sai ta kira ɗan ta Nawid da kuma Mijin ta a waya dan suzo ko zasu san yadda zasu yi da Jelly.
Ko da Nawid yazo sai cewa yayi, zai zane ta da bulala, nan fa Jelly tace ba'a haifesa ba ,dan kuwa tsayawa tayi ta riƙe kugu tace wlh in dai ya daketa sai ta rama, har ya zaro belt zai fara zaneta Hajiya ta dakatar da shi ta hanyar ce masa "Haba Nawid bakaga bata da lafiya bane? Dan Allah ka bita a hankali, kasan yadda nake son yarinyar nan kuwa, kasan yadda nake son ya mace kuwa, kai ka ɗai gare ni, ina burin samun ƴa mace Allah bai yi ba sai yanzu Allah ya bani kace kuma zaka takura mata, a'a ni na kira kane kawai dan kazo ka tayani lallaɓata ta zauna nayi wanka" zaro ido Nawid yayi yace "Haba Ummi ni da nake cewa idan ta samu sauki, miƙata wa hukuma za muyi dan su nemo iyayen ta" girgiza kai Hajiya tayi tana faɗin "Tab lallai Nawid, ai wannan yarinyar marainiya ce dan kuwa kaga a kan titi take yawo na bugeta, kuma wlh ko da ma ba marainiya bace dole iyayen ta su bani ita, dan ina son ta ba zan iya rabuwa da ita ba, kana ga yarinya kamar yar india tab, ni ai har na hango auren ka da ita" kasan cewar Nawid ya san halin Ummin sa, da bala'i son ƴaƴa mata hakan yasa yayi shiru kawai ya zuba mata ido tana ta fama lallaɓa Jelly, kamar wata yar Baby har da ce mata "my baby ki zauna ko idan na fito wanka zan goyaki muje muyi wasa" mamaki Nawid yake Jelly ta haukata masa uwa lokacin guda, girgiza kai kawai yayi ya fice daga ɗaki haushi kamar ya shaƙe Jelly.
Haka Hajiya ta rinƙa lallaɓa Jelly har Abbon Nawid ya dawo, suka haɗu sai lallaɓa Jelly suke, dan shima Abbo Jelly ta tafi da shi, lokaci guda yaji kaunar yarin yar a ransa, sai dai shi kauna na daban yake mata.
Da kyar Jelly ta yarda ta aminci suka zauna tare da Abbo a cikin bedroom É—in, Hajiya ta wuce toilet da sauri dan taje tayi wanka.
Sai kallon Jelly Abbo yake, ya kasa cire idon sa daga kallon ta, ita kuwa sai faman turo baki take, ita kaÉ—ai tana kunkuni, sai wani cool murmushi Abbo ke sakewa yana kallon face É—in ta, dan turo wannan É—an bakin nata da take ba karamin tafiya da shi take ba, ji yake kamar ya jawota jikin sa.
Haka Hajiya ta fito ta same su, Hajiya na fitowa Jelly ta miƙe ta rungume ta tana faɗin "Ke bakin ga wannan mutumin ba sai kallo na yake yana min dariya" ko kaɗan Hajiya bata damu ba, dan tasan shi ma Abbo yana bala'i kaunar ƴaƴan mata, dan haka sai tace "Sunana Ummi ba ke ba, shi kuma sunan sa Abbo baban ki ne, kin ji ko? Idan ya kalle ki ya miki dariya kema ki masa, zai ji daɗi, dan yanason farincikin yarsa" yar dariya Jelly tayi tace to, sannan ta saki Hajiya ta koma kusa da Abbo ta zauna tana murmushi
a ɓangaren shi kuma Abbo, gaban sa sai dukan uku uku yake lokacin da Jelly ke faɗa wa Hajiya yana kallon ta, ya san halin Hajiya da bala'i Kishi zata iya fara ruwan bala'i, sai dai kaunar da take wa ƴaƴa mata yasa bata kawo komai a ranta ba, kuma a tunanin ta Jelly bata da lafiya duk wani abun da zata faɗa kawai shirmene.
Tab akoi fa cakwakiya gidan su Nawid, dan da alama shi dai Abbo ya faÉ—a muje dai zuwa
ÆŠaukan kayan ta Hajiya tayi ta koma cikin toilet dan shiryawa, saboda su Jelly suna É—akin, shiryawa tayi tsab cikin wata dankareriyar shadda milk color É—inkin doguwar riga, tasha aiki daga sama har kasa.
Bayan ta gana shiri ne ta fito ta riƙo hannun Jelly suka wuce Palo, miƙewa Abbo yayi ya biyo bayan su.
Saman sofa suka zauna Hajiya ta fara ƙoƙarin koyawa Jelly wasu abubuwan, irin su yadda ake gaida mutun da kuma matsayin su a wajen ta, na iyayen, sai kuma yadda zata rinƙa zama da mutane da yadda zata yi wanka da kan ta da sauransu, ba wani abun da Jelly ke ɗauka, Hajiya ke zancen ta kawai, shi dai Abbo da yaga abun nasu bana karewa bane sai ya miƙe ya musu sallama ya wuce office na sa, daman Hajiya ta kira shi ta sashi ya dawo.
Sai faman surutu Hajiya take wai tana yiwa Jelly bayani a kan yadda zata zauna a gidan, ko word É—aya bai shiga kunnen Jelly ba, bare kuma kanta, a wanna hali wata budurwa ta fito daga É—aya daga cikin part dake cikin palon, kallo É—aya zaka wa yarinyar kasan yar duniya ce ta bugawa a jarida, dan wasu shegun riga da wando ne a jikin ta sun matseta, duk wani halitta dake jikin ta ya bayyana, ta zuba attachment a kai kamar wata dodanniya, ga wani uban glass da ta maka a ido kamar wata roka da glass, abun ba kyan gani wai an yi kwalliya
Kai tsaye hanyar fita daga palon yarinyar ta nufa, ko sannu bata cewa Hajiya ba kamar ma bata san da zaman ta a wajen ba
Kwatsam idon ta ya sauka kan, Jelly dake zaune sai faman turo baki take, a hankali matashiyar budurwan ta sauke glass É—in fuskar ta ta É—an kalli Jelly from head to toe na yan wasu mintoci kafin nan ta mai da glass É—in ta fice daga palon, tana tafiya tana juyowa ta kalli Jelly tana wani lashe baki kamar tsohuwar mayya.
Ganin yarinyar yasa Hajiya ta kara zawa Jelly kunne a kan babu ruwan ta da yan gidan nan, dan basu da mutunci a cewar Hajiya, sai dai abun da Hajiya bata sani ba shi ne, Jelly fa bata jin ma me take faÉ—e hankalin ta na kan Tv dake kunne sai faman turo baki take.
Kai jama'a me kuke tunanin zai faru a gidan Hajiya baban Nawid, hmmm muje zuwa amma dai akoi show
Mu leƙo Rimsha mu dawo
👹DAULAR MUTUWA👹