Sashe 97
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan'nauyan ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe sai kuma ta juya ta kalli Hajja Nana dake cewa.
“Sai kuma ki rasa inda zaki je sai garin mu”.
Murmushi Innayi tayi kana tace.
“Eh saboda lokacin da aka kawo Didi ƴar Nigeria ce jahar Adamawa sheik Jabeer ya kasance Aminine ga Sarki Mohammed Aliyu Mouley shiyasa suka haɗa Auren ƴaƴan su.
Shiyasa dana tashi na tafi Nigeria naje na zauna ta yankin dake magwabtaka da yankinsu kuma shiyasa nake hana Modibbo zuwa Adamawa, sai a sace yaje sau ɗaya nanma da naji nai ta kuka haka yasa yayi min alƙawarin bazai sake zuwaba Marocco ma nice ke hanashi zuwa da tuni yazo, niko nasan duk wanda yasan iyayensa to dole in ya ganshi gane ɗansune”.
Murmushi kawai Didi keyi tana sake jin ƙaunar Innayi aranta ta yanda ta riƙe mata amanar ɗanta ta kuma bashi tarbiyya.
Innayi kuwa idanunta akan Hajja Nana ta cigaba da cewa.
“Daga nan kuma ban san meya faruba a masarautar Mouley bayan tafiyata ba”.
Numfashi suka sauƙe kowa yana sake jinjina girman ikon Allah aransa da yanda al'amarin ya kasance kana suka haɗa baki wajen cewa.
“Ikon Allah rabo nefa.
Rabon Aurensa da Khausar ne ya jasu”.
Amintaccen murmushi Didi ta Saki kana tace.
“Aikam Al'amarin Ubangji ya wuce wasa sai godiya”.
Sai kuma ta ɗan kalli Innayi tare da cewa.
“Bayan tafiyarku da wata biyu Sarki Muhammad Mouley ya rasu, kana a ranar Unclee Haroon ya cika shekaru biyu a karagar mulki ƙanin Abualeey kenan. kasancewar jinyar Abualeey gaba gaba kawai takeyi, to shekarunsa huɗu a kan mulki yayi haɗari shida Baban Jameel da kuma Mamin Jameel ɗin.
A lokacin Yusuf ɗinshi ƙaramine, haka yasa dole aka bawa Unclee Yazidu. Shekaransa ɗaya rak bisa mulki, a lokacin kuwa wannan dokin Rinƙas yana tsaka da ƙuruciya, abin mamaki dokin nanne ya kasheshi har lahira a tsakiyar fada, bayan rasuwarsa aka ɗaura ƙaninsa Zarid, shima shekararsa ɗaya dokin ya kasheshi irin kisar da yayiwa ɗan uwansa zuwa lokacin kuma Allah ya bawa Abualeey sauƙi duk larurar dake tare dashi haka yasa akace shi zava maidawa mulki, shi kuwa yace shi baya buƙatar mulki a lokacin jinyar ɗan uwansa shine a gabanshi mu kuma Alhamdulillah an haifi Ibraahim an raine shi lfy haka yasa,
Yace a bawa ƙanin Zarid Isman abin mamaki ba yadda ba'ayu da isman ya karɓi mulkin nanba fir yace shi baya so, da aka matsa mishi sai cewa yayi kawai shifa bazaiyi mulkinba tunda sauran yayunsa duk wanda aka bawa mutuwa yakeyi, kawai sai ya rinƙa faɗin duk abinda sukayiwa Abualeey yace sune suka so haukatashi kuma sune suke kashe mun yarana uku duka, kuma sunema suka kashe mahaifinsu daga nan ya zama mahaici yanzu haka shi yana raye ko yaushe yana tsakiyar fada ranar da Aliyu yazo ma Allah ne ya tsaresa dan Aliyu da dokin ya kashisu dan shi ya kashe mahaifiyarsu ma Lalla Adir tohfa haukacewarsa da sirrinsu da yake ta tonawa ne yasa muka gane cewa Rinƙas yanayi mana faɗa da magautanmu ne, duk da ƙanensu mata da suka haɗa uban su dai kamar ba a'lamun cutarwa haka yasa aka matsawa Abualeey akan ya amshi mulki.
bisa dole dai, ba don yasoba aka sake daurashi kan mulkin Alhamdulillah yanzu dai masarautar Mouley babu wasu bayyanannun magauta sai dai ɗan abinda ba'a rasaba wanda tsoron yasa suka bari daga forko dai tsoron Allah bai sa sun tubaba, sai tsoron rinƙas da yasa suka rusuna amman zuwa yanzu sun gane cewa Allah shine abin tsoro zuƙata sun tsarkaka ko nida abokan zamana bamu da wata matsala asalima Gimbiya Sahra ita ke shirya komai na Khausar saidai ita batama taɓa haihuwaba sai ta ukun mu kuma ƴaƴanta duk matane, ta hudun kuma ƴaƴanta yarane amman ita duk mazane mu dai Alhamdulillah”...
Sai kuma duk suka sauƙe nannauyan numfarfashi Khausar kuwa ido cike da alamun bacci da ciwon ta lumshesu
Dai dai lokacin kuma Dr Eshaa da Lalla Hafsat suka shigo wacce bisa duk kan alamu tayi mata bayani.
Shogowan sune yasa suka rufe maganar tare da yi mata sannu da zuwa amsawa tayi tare da gaishe su cike da ladabi.
Cikin kulawa ta zauna kusa da Khausar tare da ɗan shafa gefen fuskarta.
“Sannu Allah ya sauƙa”.
Amin Ummi da Didi suka amsa.
Hajia Bunayyah kuwa baki ta taɓe a ranta tace.
“Allah shi ƙara”.
Ita kuwa Dr Isha cikin kulawa ta muƙawa Didi
Magunguna tare da faɗin.
“Lalla Hafsat tamin bayani, a bata magungunan tasha yanxu In Sha Allah duk wani zugi ko zazzaɓi da ciwon kai zata daina jinshi”
Amsa Didi tayi tare da fara ɓalla kana tace.
“Ai yanzuma kuwa zan bata”.
Gyaɗa kai Dr Isha tayi tare da sallamansu ta fita.
Didi kuwa maganin ta bawa Khausar tasha kana ta miƙe tabi bayan Dr Isha da bata tsaya duba ko Khausar ta samu rauni ba, dan tasan ko ta samu rauni tsumin tsarin masarautar da turaren wutan zasu haɗeta...
Acan Falon Didi kuwa Dr Jameel ne ya bawa Moddibo magunguna kana ya koma gefe yana amsa kiran da aka masa daga asibitinsu.
Ahankali Moddibo ya miƙe ya nufi ƙofar da sai kashi Side ɗin su, dai-dai lokacin kuma Didi ke dawowa daga Side ɗin su Khausar.
Kallonsa tayi tare da cewa.
“Ina zaka je?”.
Cikin yanayin zazzaɓin da yake ji ya fesar da numfashi kana ya motsa laɓɓansa tare da cewa.
“Zanje In kwanta ne”.
Tsayuwarta ta gyara kana tace.
“A'a muje dai kaje kaci abinci tukunna”.
Ba musu ya gyaɗa kai kana ya nufi dining tana biye dashi zama yayi tare da ɗan rumtse idanunsa.
Gefensa ta zauna kana tayi serving ɗin sa,
Sai kuma ta kalli Dr Jameel tare da cewa yazo suci abinci.
A hankali Modibbo ya kalleshi jin yana cewa.
“Didi Azumi nakeyi”.
Kai Modibbo ya ɗan jinjina dan zuwa yanzu dai ya fara gamsuwa da sauyawar Dr Jameel, musamman yadda ya dage da azumi dan daƙushe sha'awarsa.
Ita kuwa Didi kai ta jinjina sannan ta sawa kanta suka fara cin abincin, yana ganawa ya miƙe.
Da sauri tace.
“ina kuma zakaje, kasha maganin ne?”.
Dai-dai lokacin Dr Jameel ya iso wurin kujera yaja ya zauna yana cewa.
“Eh Didi yasha”. Sai kuma ta juyo ya kalli Modibbo tare da cewa.
“Amman fa kamar ba zazzabin kawai ke damunsa ba na lura yana yawan miƙa kamar wanda jikinsa ke masa ciwo, bini bini ya dafe ƙugunsa”.
Da sauri Didi ta miƙe tare da turawa Dr Jameel ɗin womers ɗin abinci gabansa kana tayi cikin falon dan tasan ba ƙaramin aikin Dr Jameel bane yayi ɓaram-ɓarama, a gabanta haka yasa ta ma mance yace yana azumi.
shi kuwa Modibbo wani irin harara ya rabkawa Dr Jameel tare da cewa.
“Ace mutum shi bakinsa baya iya shiru”.
Murmushi Dr Jameel yayi tare cewa.
“Na lura baka taɓa sanin maceba, da alamu jiya kuma kayi yaƙin fatauci shiyasa ƙugu da jinyoyi suke ciwo, ah aini da na ɗauka kai kam ba abinda zakayi da mace yadda kake wasu abu kamar waliyi, shine tun ba'aje ko inaba kaje kai ta karya ƙugu ka kwashi Gara, yanzu kuma jiki magayi dan na lura baka sararawa yar mutaneba”.
Sai kuma yayi saurin dage kansa tare da sakin kara jin yadda Modibbo ya kaiwa bakinsa bugu.
Dariya ya fashe dashi tare da bin Modibbo da ido kana ya dawo tsakiyar falon.
A hankali ya nufi Side ɗin sa saboda wani irin bacci da yake ji ga zazzaɓin ya fara masa yawa alamar maganin ya fara kokawa da Zazzaɓin yana shiga ya kwanta bisa 3 sitter...
Jakadiya kuwa kai tsaye ɗakin Tarihin Masarautarsu takai ƙyallen budurcin Khausar.
anan aka ajiye wannan frame ɗin kana ta ɗauko sanda da Jigidan Zinare mai tambarin Masarautar Mouley sai chain na ƙafa shima na Zinare ne kuma munduwa mai tambarin Masarautar, da dai wasu kaya masu masifar kyau da ɗaukar hankali kai tsaye sashen Didi ta shiga kana ta kalli Didi dake zaune kan 2sitter daga ƙasa Carpet ta zauna tare da faɗin.
“Yawwa Didi gashi an gama haɗawa”.
Sanyayyan Murmushi Didi tayi hakan ganin abin sai ya tuna mata da lokacin da aka kai mata nata cikin sauƙe ajiyar zuciya tace.
“Toh shikenan mu tafi mu nunawa Niyna daga nan mu tafi da ita”.
Miƙewa Jakadiya tayi suka nufi Side ɗin Niyna daga nan kuma suka shiga sashin abokan zamanta suka nuna musu kana suka wuce wurinsu Ummi.
Hajja Nana, Innayi da Hajja Umma suka samu azaune suna hira.
Yayin da Ummi Khausar Asma'u Dije da Asiya ke bedroom.
Zama Didi sukayi kana suka sa aka kira su Ummi,Hajiya Bunayya,Aunty Ruƙayya, Aunty Hajara duka suka fito falon Jakadiya ce tayi musu bayanin cewa.
“Ga wannan Sandar amma yanzu dai an nuna muku ne saboda tabbacin cikekken tukuicin da aka samu daga Masarautar Mouley ce”.
Wani irin farin ciki ne ya mamaye baki ɗaya ilahirin zuciyoyinsu saɓanin Hajiya Bunayya da take jin wani sabon kunci da tashin hankali aƙahon zuciyarta.
Jakadiya kuwa cike da alfahari ta cigaba da cewa.
“Kuma yanzu za'a sake mai dashi cikin karagar masarautar tarihin gefenta sai sanda aka samu ɗa namiji ya cika Shekara ɗaya ranan za'a mallaka mata sandar ahannunta saboda sandar shine zai nuna shaidar Lalle gadon Masarautar a ɗakinta yake”.
Cike da matsanancin farin ciki Innayi tace.
“Alhamdulillah abinda ake ƙi dai shi ya tabbata in Allah yaso Sarauta dai tana nan ta tabbata a ɗakin Lalla Didi”.
Niynah kuwa murmushi take tare da faɗin.
“Alhamdulillahi burin magauta bai cika ba”