Sashe 59
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna isa wurin ɗaya daga cikin hadiman ya ja mishi kujera, ya zauna, bisa umarnin Sheykh Jabeer way’annan hadiman suka ci gaba da shirya, shirin da ya bayyana cikakken kwarjininsa me burgewa.
“Masha Allah.”
Ibraahim ya fad’a lokacin da kwararrun hadiman nan suka nad’a masa kyakkyawan farin hirami me ratsin adon sky blue akansa, da yayi matuk’ar k’ara bayyana kwarjininsa, still suka gyara mushi zaman tattausan farar, alkyabbar da taji ado, me d’auke ido da jan hankali, wacce tana da faɗi kuma a buɗe take, tabbas zan iya cewa Modibbo bai tab’ayin kyau irin na yau ba, domin shi kansa ya shaida hakan, saboda tsananin kyaun da yayi, Sheykh Jabeer da Kuma Ibraahim murmushi kawai suke idan sun kalleshi.
Kyakkwawan takalmin sarauta light blue aka sanya masa aƙafarsa, wanda shiya ƙara cika adon nasa, domin harda adon bit din gold ajikinsa, ahannunsa kuwa wani tsadadden agogon gold suka d’aura masa, wanda cikinsa ke d’auke da tambarin masarautar tasu ta Mouley.
Murmushi Ibraahim ya sakeyi, wanda hakan yasa Modibbon ƙanƙan da idanunsa, cikin sanyi da taushin muryar da taza me masa d’abi’a yace.
“Wai Ibrahim duk wanna murmushin na menene?”
Murmushi Ibraahim din yayi, yana me gyara masa zaman takalman ƙafarsa yace.
“Duk wannan murmushin da shigar taka ta musammance, yau din rana ce ta farinciki Yah Aleey, yau da za’a gabatar dakai awajen dangin mahaifinka, yau kowa zai san da zamanka, ni gani nake kamar masu shiryakan ma basa sauri.”
Ya ƙare maganar yana sake kallon tattausar alkyabbar dake jikin Ya Aleey’n nasa, wacce Sheykh Jabeer ke k’ara gyara masa zamanta.
Aransa yake yaba baiwar kyau kwarjini had’i da haiba da Allah Yayiwa Aleey’n.
Abayyane kuwa cewa yayi.
“Masha Allah,
Sheikh Jabeer kuwa cikin kulawa yace.
“Fatabarakallahu fiy ahasanil khali kiyn.
Allah Ubangiji ya albarkaci rayuwarka, ya kareka daga sharrin mugun mutum da aljan, ya kuma tsareka daga sharrin idanun al’ummar da zasu kalleka, ka shiga da addu’a, Ubangiji na tare dakai akoda yaushe.”
Amin Ya Allah, Jabeer bin Jabeer dake shigowa ya amsa.
Shi kuwa Modibbo Cikin dai ɗaurewar kai da har yanzu ya ke ciki ya gyaɗa mishi kai.
Yayinda Ibraahim kuwa, tsananin kyaun da Yah Aleey’n yayi duk ya gigitashi, hakan yasa shi zaro wayarsa kirar iphone 14pro max ya shiga daukarsa hoto, yana me sake yaba kyawun da yayi, koda ya kammala yi musu hoton falo ya fito, nan ya iske Dr. Jameel da kuma Zakareeya suna zaune cikin shiga ta al'farmar da alama suma sun gama shiryawa, ganinsa yasa suka miƙe tsaye, sai kuma suka juyo jin motsin su Modibbo kusan a tare sukace.
“Wow masha Allah, lallai jini baya ɓuya”.
Suka ƙare mgnar suna matsowa kusa da Modibbo.
Shi kuwa Ibraahim da sauro ya nufi inda za’a gudanar da taron, yana zuwa cikin babban falon taron masarautar tasu kuwa ya tararda wajen acike maƙil, ƴan uwa duka sun hallara kowa da kowa nasu na nan, iyaye, kakanni dama jikoki harda ƴaƴan jikoki, babban falon ya cika maƙil, yayinda acan gefe kuwa wurin da aka warene waje na musamman na zaman amarya da ango zasu zauna a tsakiya.
Sai kuma gefen su Didi dake zaune tare dasu Lalla Hafsa da Lalla Khadija sai sauran matan Abualeey da yaransa.
Ibraahim na shigowa Rahma ta miƙa da sauri tazo nufoshi tana fad’in.
“Yah Ibraahim, har yanzu baku gama ba, duk an fitofa ku ake jira, dangi duk sun zak’u dason ganin Yah Aleey.”
“Yanzu zamu shigo, nazo duba yanayin wajen ne.”
Ibraahim ya amsa yana me shakan daddad’an kamshin turaren wutan dake hannunta, wanda hayakinsa ke tashi acikin kasko.
Cikin sassarfa kuma ya juya, domin yiwa Modibbo da kuma Kakansu Sheykh Jabeer jagora.
A falon ya samesu cikin jin daɗin yace.
“Bismillah mufa ake jira”. Ya faɗa tare da tsayawa gaban Modibbo, yayinda Sheykh Jabeer kuwa yake gefen damanshi, Zakariyya kuma da Dr Jameel a gefen hagunshi
Kana suka fito cikin Corridor da zai sadasu da falon.
Dr Jameel a hankali ya ɗan ja baya ya koma cikin falon da suka fito ɗin sabida ganin kiran Babynshi.
Amsa kiran yayi tare da maida ƙofar ya rufe.
Su Zakariyya kuwa basuma kula ɗaya komaba.
Sabida Hadiman da suke zagaye dasu.
Tafiya suke a hankali cikin ƙasaita da Kuma nutsuwa, haɗi da tsananin jinin sarautar dake gudana acikin jinin kowannensu, musamman Modibbo, wanda yake jin kansa acikin wani irin yanayi na daban.
Tsantsar girma yake ji, haɗi da zumma da ƙasaitar da bai tab’a jin kwatan kwacinsa ba, haka suka nufo babban falon dake cike da dangi da y’an uwa.
Acan side din da Khausar take kuwa, jakadiya ce da kanta tare da Lalla Salma wato mahaifiyar Zakariyya, suka rik’o Khausar din wacce ta zama tamkar wata flower saboda tsabar kyau, kamshi kawai take bazawa me tsuma zuciya.
Lalla Salma da takejin Kaunar Khausar har cikin zuciyarta ne ta ɗan sunkuyo da kanta daidai saitin kunnen Khausar din tace.
“Ki yawaita ambaton sunan Allah a bakin ki har muje mu dawo, Ubangiji Allah Ya kareki daga sharrin masu sharri, Allah ya tsareki ya kuma kauda idon mak’iya daga gareki, Allah Yasa ki shiga cikin zuri’ar mu da k’afar dama, alfarmar annabi da al’qur’ani, kiyita adduan Allah ya tsareki da fuskantar k’alubalen da surkuwarki ta fuskanta lokacin da ta shigo ahalinmu, Allah ya miki al'barka ya dauwa mar dake cikin farinciki.”
Da “Aameen” ta amsa cikin ranta, yayinda a fili kuwa jinjina kanta kawai tayi, tanajin matar ta kwanta mata arai, saidai tambayar azuciyarta take wai shin menene ke naɗe cikin tarihin Modibbo waye shi, meyasa innayi ta koma dashi can? Me hakan yake nufi haka tai ta jerawa kanta tambayoyi?
Tambayar da bazata samu amsarta ayanzu ba.
Ahaka suka ci gaba da tafiya Jakadiya da kuma Lalla Salma na rike da ita, sai kuma Hadimai dake biye dasu abaya, hadi dasu Asmau Asiya da kuma Dije.
Sassanyan busar sarewa me tsananin dadin jine ya cika kuwannuwan way’anda ke zaune a falon, kasancewar isowar su Modibbo, wanda hakan yasa duk idanun mutanen dake wajen ya koma kansu.
“Masha Allah, fatabarakallahu fiy ahasanil kali kiyn.”
Shine abunda ke fitowa daga bakin tarin mutanen dake wajen, saboda yanda Modibbo yayi matukar kyau had’i da k’awatuwa, tsananin kwarjini da haiba sun bayyana akan kyakkywar fuskarsa, da tayi kama dana mahaifinsa sak, sarautar zalla yau ita ta bayyana kanta ajikinsa.
Yayinda wasu daga cikin mutanen wajen kuwa, suke raba idanunsu wajen kallonsa shida Ibraahim, saboda tsananin kamar da sukeyi da juna.
Ayau fuskokin da yawa daga cikin masarautar ya cika da farincikin da har ya kasa ɓuya.
Cikin tsananin jin dadi suke wasu dayawa ke fitowa suna rungumar Modibbo, wanda tsananin kwarjininsa ya haifar musu da soyayyarsa me tsanani.
Cikin sauri Innayi ta nufi inda suke tare da fara ware wannan sandar nan da take ajiye dashi da ƴan silalla, ware sandar ta farayi daga cikin furen da aka naɗeta.
Tana isa wurin ta tsaya gaba Modibbo tare da miƙa mishi sandar, shi kuwa Modibbo cikin tsananin mamaki da kaɗuwa ya ware idanunshi a kan fuskarta murya cike da mmki yace.
“Yah Salam wa nake gani a gabana ni Aliyu”.
Murmushi mai cike da farin ciki innayi tare da kamo hannunshi ta danƙa mishi sandar kana tace.
“Innayinka ce a gabanka ba kama bace, nice nan Modibbo nazo maka da tsaraba mafi daraja a gareka tare da rakiyar masoyanka”.
Ta ƙare mgnar tare dayi mishi nuni da inda su Abban Jameel Malam Arɗo Bappa Jimeta Lamiɗo Haiydar, suke zaune.
Cikin sauri ya dawo da ganinsa kan Innayi tare da cewa.
“Yah ilahi Abba harda Lamiɗo da kuma Malam Arɗo”.
Sai kuma ya kalli inda ta nuna mishi tana faɗin.
“Harda Umminka ma ba”.
Wani irin amintaccen numfashi ya fesar lokacin da kwayar idanunsa suka sauƙa kan fuskar Ummi, yalwataccen murmushi ya sakar mata, sai kuma ya kalli Innayi da tuni ta juya ta nufi wurinsu Ummin sai kuma ya kalli Hajia Bunayyah, tabbas ya ganeta a fili yace.
“Toh ita kuma me haɗina da ita?”.
Sai kuma ya maida kallon sa kan Haiydar dake mishi murmushi a hankali yace.
“Harda Haiydar”. Shi kuwa Haiydar cikin jin daɗi ya kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Kai Masha Allah Abba kalli yadda Modibbo yayi kyau, kai shigar sarauta akwai kyau”.
Murmushi kawai Lamiɗo yayi dan ya fahimci cewa shima Haiydar jinin sarautar ne ya motso.
Shi kuwa Modibbo bisa jagorancin Sheykh Jabeer da kuma Ibraahim Zakariyya da Jabeer bin Jabeer ne yasa yake biye dasu zuciyarsa fal tarin tambayoyi kana da mamakin ganin su Innayi musamman kuma Lamiɗo barma ace ta Bappa Jimeta da baisan shiba.
Ahaka har suka isa wajen da zasu zauna, Sheykh Jabeer na riƙe da hannunsa.
Saidai kasancewar a tasu al’adar ango baya bazai zauna har harsai amarya ta ƙaraso hakan yasa koda suka iso wajen zaman tsayawa sukayi, yayinda tuni Fadawa suka zagayesu tare da ware tabka-tabkan rigunansu sukayi musu ƙawanya.
Suna tsayuwa kuwa suka soma jiyo, wani daddaɗan busa sarewa, me ɗauke da sassanyan kirarin da akayita da harshen larabci da marabta baƙi.
Wanda hakan yasa gaba ɗaya idanun ya koma saman steps din dasu Khausar ke takowa, domin tuni anfara shelan zuwan amarya.
Jin hakane yasa fadawan nan kuma janye rigunansu, tare da zagayawa suka koma bayan kujerar da aka ƙawata dan zaman ango da amarya, yayinda wasu kuma duk suka rusuna ƙasa.