← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 150

Sashe 64

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin yanayin kaɗuwa, mamaki, Al'ajabi ta fara takowa har ta isa gaban Dr Jameel ta tsaya cikin sarkewar murya ta furta.
“Yah Jameel”.
Kallonta Moddibo yayi tare da girgiza kai yace.
“A'a Asma'u”.
Cikin ficewar hayyaci ta ɗaura hannunta akai tare da faɗin.
“Ummiiii kizo ga Yah Jameel”.
Sai kuma tayi baya luuu idanunta sukayi sama.
Cikin wani irin sauri Dr Jameel da tun time data kira sunansa ya zuba mata idanu yana kallon ƙiranta da kuma yanda Ubangji ya ƙawata surarta, lokaci ɗaya yaji wani irin yanayi da bai taɓa jin makamancin sa ba akan ko wacce irin mace da yake mu'amala da ita karon farko yaji wani irin tsarkakekken soyayyar ta ya mamaye masa zuciya.
Azabure ya nufe ta ganin saura kaɗan takai ƙasa ya tallafota jikinsa ta faɗa kan ƙirjinsa asume.
Faɗawa jikinsa da tayi yasa ya koma baya ya faɗa kan kushin ya zauna, hannunsa yasa ya tallafo fuskarta sai kuma ya ɗaga kansa ya kalli Moddibo kana yace.
“Suma fa tayi”.

Cikin Sauri Moddibo ya riƙe tsintsiyar hannunta cikin yanayin damuwa yake faɗin.
“Asma'u”.
Ina tuni ta samu kallon Ibraahim yayi kana yace.
“Ibraahim ka miƙo min ruwa”.
Dr Jameel kuwa kallon Moddibo yayi cikin wata kasalalliyar murya gami da shauƙi yace.
“Ya dai kake shiga hurumin daba naka ba, ya ina matsayin Dr sannan ta suma ajikina kake cewa amiƙo maka ruwa”.
Wani kallo Moddibo ya mata tare da watsa masa harara kana ya buga masa tsawa da faɗin.
“Kai Mahaukacin ina ne ya yarinya zata suma sannan ka tsaya kana maganar sai huruminka wani irin hurumi kake dashi a kanta, idan zakayi abinda zata farfaɗo kayi ka wani maƙale yarinya atsakanin cinya haukane akan ka”.
Kallon Moddibo yayi tare da juya idanunsa kana yace.
“Kamar ya kake cewa haukane akaina Ni naga matar Aure”.
Cikin tsawa da hararansa Moddibo yace.
“Koma yayane yanzu kayi abunda yarinya zata farfaɗo”.
Ahankali Zakariyya ya tsugunna kansa tare da bubbuga kumatunta yana kiran sunan da yaji Moddibo na kiranta da.
“Asma'u³”.
Hannunsa Dr Jameel ya janye kana ya ture gefe tare da cewa.
“Dakata Zakariyya nasan kai Likita ne amma wannan ba hurumin ka bane Saboda wannan hiruminane”.

Alalace Zakariyya ya banka masa harara tare da faɗin.
“Mayen banza mayen wofi, wato daga ganin Yarinya itama ka ɗaura ƙolafacinka da kwadayin ka akanta”.
Araunane ya ɗago kansa ya kallesu baki ɗaya cikin yanayin gaskiya da gaskiya yace.
“Wallahi ban kalleta da idanun da nake kallon sauran ƴan matan da nake mu'amala dasu ba, na kalleta ne da wasu irin idanu masu matuƙar daraja domin ita mai darace da mutunci”.

Tsaki Moddibo yayi cikin hasala da abinda Dr Jameel keyi ya karɓi goran ruwan da Ibraahim ke miƙa masa ya watsa mata afuska amma bata farfaɗo ba.
Langwaɓar da kai Dr Jameel yayi tare da faɗin.
“Dan Allah kar ka jiƙamu Ni nasan yanda zanyi in farfaɗo da abuna”.
Moddibo kuwa cikin mamaki ya zubawa Dr Jameel idanu yana kallon ikon Allah da karfin hali.

Cikin lumshe idanu Dr Jameel da har zuwa lokacin yake rungume da Asma'u ya sunkuyo da kanta.
Da wani irin azabebben sauri Moddibo ya riƙe ka sa fuskarsa babu walwala yace.
“Wallahi kada ka kuskura, Idan ka yarda ka kuskura Ni nasan abinda zanyi maka hauka ne akan ka? Ko kuma kayi tunanin itama irin ƴan matan da kake rayuwa dasu ne da zakayi ƙoƙarin kai bakinka kan nata?”

Hannunsa biyu ya haɗa kana yace.
“Dan Allah kayi haƙuri Moddibo na rantse da Ubangijin daya busa min numfashi bana kallon wannan Baiwar Allah Asma'u amatsayin matar da zanyi lalata da ita”.
Sai kuma ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa kana ya cigaba da cewa.
“Idanuna suna kallonta ne amatsayin matar Aurena, kuma uwar ƴaƴana wallahi bawai kissing ɗin ta zanyi ba ya kuke maidani kamar Bunsurune zanyi ƙoƙarin dawo mata da numfashinta nefa”.
Still babu walwala atare da Moddibo ya gyaɗa kai kana yace.
“Ok”.
Dr Jameel kuwa cikin lumshe idanu ya sunkuyar da kansa kanta kana ya ɗaura bakinsa kan hancinta yana hura mata numfashi.
Asma'u kuwa ahankali taja wani dogon numfashi tare da faɗin.
“Ummi wallahi Yah Jameel ɗin mu bai rasuba ga Yah Jameel ɗin mu na ganshi da rabshi”.
Sai kuma ta buɗe Idanunta ganinta kwance acinyar Dr Jameel cikin sauri ta yunƙura ta zauna tare da faɗa wa kansa ta rungumesa yayin da take kuka mai tsuma zuciya kana tace.
“Yanzu dama Yah Jameel baka mutu ba, aka kawo mana gawar wani akace ka mutu?”.
Kasa ƙara sa Maganar tayi saboda yanda kuka yaci ƙarfinta kana kallo zaka san daga ainihin zuciyarta maganar ke fitowa.

Lokaci ɗaya tausayin ta ya mamaye baki ɗaya ilahirin zuciyar Dr Jameel hannu ya ɗago da niyyar rungumeta.
Da sauri Moddibo ya buge hannunsa.
Shi kuwa Dr Jameel zafin bugun da Moddibo ya masane yasa shi saurin mayar da hannunsa yana yarfawa sai kuma ya kalli fuskar Asma'u dake cigaba da kuka yace.
“Asma'u Wayyo Allana Yayanki zai kashe Ni kafin komai ya kankama”.
Moddibo kuwa ahankali ya kira sunanta cikin girma da kamalada da zame mata matsayin babban wanta kana jagoro kuma uba yace.
“Asma'u”.
Ahankali ta juya ta kalli Moddibo sai kuma ta maida kallonta kan Dr Jameel ta sake rungumesa.

Ganin haka yasa Moddibo saurin fin cikota daga jikin Dr Jameel ya tsaidata sai kuma yace.
“Zo ki zauna anan”.
Ya faɗa tare da zaunar da ita akan Kujeran cikin yanayin nutsuwarsa da tuno yadda J ɗinsa ke killacesu da basu kariya akan kamilallun mazama bare irin Dr Jameel a hankali yace.
“Asma'u ki buɗe ido ki kalleni da kyau”.
Idanunta ta buɗe da tuni hawaye suka kwaranya ta kalli Moddibo.
Cikin fesar da numfashi ya gyara zamansa tare da cewa.
“Wanene Ni awajenki?”.
Cikin raunin murya tace.
“Yah Moddibo Yah Jameel”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Menene matsayina awajenki?”.
Still idanunta na zubar da hawaye tace.
“Tamkar uba kuma tamkar Yaya Jameel”.
Zazzafan Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.
“Toh kiyi haƙuri da abinda zan faɗa miki, Dr Jameel ba J ɗina bane mai kama dashi ne kawai, nima nashiga irin yanayin da kika shiga lokacin dana fara ganinsa”.
Kai Asma'u ke girgiza wa tare da cewa.
“Wallahi Yah Moddibo ban yarda ba Yah Jameel ne”.
Cikin rauni ya kira sunanta da faɗin.
“Asma'u”.
Ahankali ta ɗaga ido ta kallesa cikin sanyi Murya yace.
“Na taɓa yi miki ƙarya ne?”.
Cikin wata raunatacciyar murya ta girgiza masa kai tare da cewa.
“Yah Moddibo baka taɓa yimin ƙarya ba, amma wallahi bazan yarda da abinda kake faɗa ba”.
Ta ida maganar tare da miƙewa ta nufi Corridor data shigo tana gudu tana cewa.
“Ummi Ummi”.

Ahankali Moddibo ya koma ya zauna tare da ɗaura hannunsa duka biyu ya dafe kansa.
Ya tabbar kafin Asma'u ta yarda cewa wannan ba ɗan uwanta bane za'a ɗauki lokaci.
Sai kuma ya ɗaga kansa tare da kallon Dr Jameel dake ƙoƙarin binta yana kiran Asma'u asanyaye yace.
“Ka dawo ka zauna saboda bazata saurareka ba.
Wallahi Ni kaina zuciyata bata gama yarda min cewa ba J ɗina bane kai.
Kawai jikina da zuciyata tana gamsuwa da cewa Kai ba J ɗina bane”.
Sai kuma ya lumshe idanunsa da yake jin ruwan hawaye na tsats-tsafowa kana ya cigaba da cewa.
“Saboda yanayin lalacacciyar ɗabi'ar da kake yi na tabbatar kuma babu abinda zaisa Ummi, Asma'u,da Bashir su yarda cewa ba kai bane J sai In har sun fuskanci mummunan ɗabi'unka da halayyar ka da yanayin ka na neman mata shine kaɗai zaisa su yadda”.
Sai kuma ya sanya bayan hannunsa tare da goge hawayen da suka saƙƙo asaman kuncinsa kana ya cigaba da faɗin.
“Saboda J ɗina Amintaccene mai Aminci mai kamala ne mai mutunci ne, kuma tsarkakekkene bai kasance yanayin makamancin ɗabi'unka ba”.

Tunda Moddibo ya fara magana jikin Dr Jameel yayi bala'in sanyi, ganin maganar da Moddibo keyi daga ainihin zuciyarsa ke fitowa kana yana jin magan-ganunsa nada muhimmanci da kuma ƙarfi kana yana ganin yana da yaƙini da gamsuwa.
Cikin mutuwar jiki ya koma ya zauna karo na farko arayuwarsa daya fara jin tsananin ƙyamar kansa da kansa akan ɗabi'unsa na neman mata.
Lokaci ɗaya ya riski kansa da wani mummunan tsinkewar zuciya saboda har ƙasan ransa Allah ya jarabcesa da son wannan yarinya daya gani wacce ake kira da Asma'u.
Wacce ita kuma take masa kallon ɗan uwanta wanda zuwa yanzu ya fahimci komai nasa yana mata kama da ɗan Uwanta ne daya rasu.
Hakanan ne yasa zuciyarsa ya cika da tsoro da taraddadi anya Moddibo zai lamunce abashi Auren Asma'u ayanda yake nuna tsananin ƙyamarsa akan halayyarsa na zina...

Kansa ya riƙe da hannunsa duka biyu kana ya furta.
_“Astagfirullah wa'atubu ilaik”_.

Moddibo kuwa cikin sanyi jiki ya juya ya kalli Zakariyya dake cewa.
“Moddibo muyi alwala muyi sallah ana kiran Sallah”.
Kai suka gyaɗa kana suka miƙe sukayi al'wala kana nufi masallaci alayi ɗaya sukayi jam'i koda suka idar da Maghriba basu dawo gida ba saida akayi Isha'i kana suka dawo.
Suna dawowa suka samu an shirya musu komai na a binci dining....
Chapter 64 · 0% Book details