← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 150

Sashe 102

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗankwalin abayar kanta ta cire ta miƙa masa karɓa yayi yana ɗan buɗawa.
Baki ta tura tare da cewa.
“Ai wannan ma bashi da nauyi bari In ɗauko maka ɗan kwalin Less”.
Saurin riƙo hannunta yayi ganin ta yunƙura yace.
“Ainima wanda nake saki kike kaɗewa bana Less bane kin manta?,Na Uniform ne na Uniform kuma be kai wannan kauri ba”.
Baki ta tura tare da faɗin.
“Toh ka kaɗe”.
Cikin tsira mata idanu yace.
“Ina idan na kaɗe zakiyi shiru?”.
Gira ɗaya ta ɗage cikin jin dadi tace.
“Eh mana kai dai ka kaɗe na gani”.
Murmushi yayi kana yace.
“Toh ki share hawayen ki”.
Ba musu ta sanya hannunta ta share hawayen yayin da take sakin murmushi tana tuna yanda take jin azaba ahannunta idan ta kaɗe sai kuma ta ɗan ɓata fuska da faɗin.
“Toh kaje ka kaɗe mana”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh muje”.
Kallonsa tayi da kumburarrun idanunta tace.
“Ina?”.
“Muje mana kiga yanda zan kaɗe”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Ok”.
Hannunta ya riƙe suka shiga bedroom ɗin kana suka wuce Bathroom.

Bocket ya jawo ya sa ɗankwalin kana yasa ruwa.
Juyawa yayi ya kalleta tana tsaye bakin ƙofa tana murmushi kuma har zuwa lokacin tana sauƙe ajiyar zuciya na kukan da tayi amma kuma fuskarta ɗauke da murmushi ya lura kaɗe ɗankwalin zai sata farin ciki ganin itama yau ta samu ƴanci zata sashi aiki cikin langwaɓar da kai ya kwaikwayi muryarta yanda take roƙon sa abaya yace.
“Ayyah Yah Mu'allim a kiyi haƙuri mana In cire rigar jikina kar in jiƙe”.
Ka faɗa ta maƙe kana ta tura bakinta tace.
“Ai kaima lokacin da kake sani kaɗewa harda hijabi ma ajikina da kuma Uniform ɗina haka kuma nake kaɗewa”.
Sake langwaɓar da kai yayi tare da narkar da murya yace.
“Kenan yanzu bazan cire Jallabiyar ba?”.
Kai ta gyaɗa tana murmushi tace.
“Yesss Of Course kayi ahakan”.
Ta ƙare maganar tana cilla girarta sama fuska ɗauke da murmushin mugunta.
Kai ya gyaɗa tare da tsugunnawa ya matso ɗankwalin acikin bokitin”.
Cikin sauri ta wani tura baki tace.
“Ai ba'a matse ɗankwalin sosai kaɗan ake matsewa”.
Ta faɗa tana karasa shiga cikin Banɗakin abakin Bathtub ɗin ta zauna shikam cikin wani irin yanayi na musamman ya fara kaɗe ɗankwalin na farko, hammm ya ja numfashi sabida sanyi ruwan daya watsu a jikinshi,
sai kuma ya kaɗe na biyu kana ruwan ya watsu a fuskarsa sake kaɗewa yayi Still ruwan ya sake watsuwa afuskarsa tuni sajensa ya jiƙe.

Ido ta tsirawa Sajensa tana sakin murmushi Allah ya sani sajensa na masifar yi mata kyau musamman yanzu da fuskarsa ta jiƙe da ruwan sai ƙyallin sajen keyi murmushi kawai take tafi kowa sanin yanda zaiji a hannayensa idan ya kaɗe.
Moddibo kuwa sau bakwai ya kaɗe sai kuma ya tsugunna zai mayar cikin Bokitin.
Cikin sauri ta kamo hannunsa tace.
“Wallahi sai ka sake kaɗewa ai bai bushe ba”.
Lumshe idanunsa yayi tun lokacin da hannunta ya sauƙa kan nasa jin tsikan jikinsa na tashi saboda laushi da kuma santsin hannunta haka nan ya tsinci kansa cikin wani irin farin ciki da shauƙi da kuma nishadi ɗan marairaice fuska yayi kana yace.
“Toh shikenan”.
Sai kuma ya ƙara uku kafin ya kalleta yace.
“Toh yayi In tsoma”.
Cikin jin daɗi ta gyaɗa masa kai sake tsomawa yayi ya matse zuwa lokacin baki ɗaya Fuskarsa ta gama jiƙewa har ruwan na ɗiga tal-tal-tal kana gaban Jallabiyarsa ma ya jiƙe ahaka dai har ya tsoma sau biyar ya kaɗe sai kuma ya ajiye ɗankwalin acikin Bokitin ya riƙe ƙugunsa tare da cewa.
“Wayyo Allah ƙuguna”.
Still sajensa na ɗigar da ruwa til-til-til.
Dariya ta ƙyalƙyale dashi harda dafe ciki.
Tsayawa yayi yana kallon yanda dimples ɗin ta ya lotsa da kuma yanda fararen haƙoranta suka bayyana suna sheƙi duk da cewa ga yanda fuskarta yayi ja da kuma idanunta suka kumbura cikin ƙyalƙyala dariyar tace.
“Madallah ka dai ji yadda nake ji. Allah ya ƙara ai nima haka nake ji kuma wallahi saura arba'in da biyar”.
Ta ƙare maganar tana mishi signal ɗin daya sashi jin wani irin fitinenne abu na zirya daga tsakiyar kansa har zuwa tafin sawun shi.
Karya kai yayi tare da langwaɓar da murya yayi kalar tausayi kamar yanda da take masa yace.
“Dan Allah Malama kiyi haƙuri arage min yawansu yayi yawa hannuna ciwo yake”.
Cike da farin ciki ta kuma fashewa da dariya kana ta miƙe ta riƙe ƙugu tace.
“Haka nake ji kaima kayi”.
Sai kuma ta zuba wa sajensa idanu tana kallon yanda ruwa ke cigaba da ɗiga tal-tal-tal.
A hankali yasa babbar yatsarsa na hannunsa na dama ya kwantar da gashin giransa tare da zira mata idanu.
Ganin ta kifi tafin hannunta kan sanjeshi tana ɗan katse ruwa tare da cewa.
“Bari in gogema maka ruwan”.
Sai kuma ta ƙare maganar da yin murmushin da zuba idanunta kan sajen da kyau.
Ya lura batama sanin lokacin da take kai hannunta kan sajenshi, ganin yadda ya tsira mata idonsa ne yasa tai saurin janye hannunta.
Shi kuwa Modibbo cikin wani irin fitinenne flenings ya ɗan sake matso ɗan kwalin Abayar ya sake kaɗewa dake ta miƙe tsaye tana kusa dashi haka yasa ruwan ya jiƙata.
A tare suka saki ajiyar zuciya.
Ita kuwa gira ta kuma ɗaga mai tare da cewa
“Ya akayi?”.
Cikin fitinenniyar murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Zaki kasheni“.
Murmushin mugunta tai tare da cewa.
“Ba wani mutuwa sai wuya dai, ci gaba, tunda ban mutuba in sha Allah kaima bazaka mutuba”.
Cikin narke fuska yace.
“Uhmmm bayan wuya kuwa zamsha daɗi ba“. Sai kuma ya sunkuya ya cigaba da kaɗewa har yayi na takwas Kallonta yayi tare da faɗin.
“Wayyo Didi na hannuna ciwo Allah hannuna zogi yake min Minha”.
Dariya ta ƙyalƙyala kana tace.
“Allah ko goma baka yiba kuma sai ka ƙara”.
Juyawa yayi ya fuskanceta kafin yace.
“Kiyi haƙuri ni koma me kike so ki sani amma banda kaɗe ɗankwalin nan yana da wahala”.

Ware Idanunta tayi tace.
“Kaima haka kake yimin ba haka kake sani ba dan haka kaima sai kayi,yau kam sai kayi”.
Yana yarfe hannu yace..
“To ai nayi amma arage min kingani kin ninka min yayi yawa ki bari sai gobe In ƙarasa,in yaso yau inyi 25 gobe inyi 25”.
Ɗan shiru tayi kamar mai nazari sai kuma tace.
“Toh kayi 25 ɗin, kayi na yarda”.
Shafa sajensa yayi tare da cewa.
“Kuma nima ai ashirin nake saki”.
Ƙugu ta riƙe kana tace.
“Toh aini laifina kaɗan ne”.
Kwaikwayon maganar ta yayi yace.
“Toh nima ki bari idan na sake miki lefin sai ki sani”.
Da sauri tace.
“Zaka sake laifinma kenan?”.
Cikin sauƙe numfashi yace.
“Yess sosai ma kullumma kuwa,bai kema kullum sai kin maimaita laifi dan haka nima banyi alƙawari bazan ƙaraba”.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Wlh komawa zanyi”.
Sai kuma ta kalleshi jin yana cewa.
“Kiyi haƙuri wasafa nake, wanda nayima na tuba ki yafemin”.
Cikin jin dadin cewa yau ita kesa Moddibo irin punishment ɗin da yake sata kuma yanayi harda ƙaramar murya yake mata cikin jin dadi tace.
“Toh ka kaɗe, Ka kaɗe”.
Kai ya gyaɗa kana yasa ita kam dariya ta cigaba dayi yayin da yake jin wani irin farin cikin ganin murmushin ta da kuma yanda idan yace ya gaji take dariya yasa duk kaɗewa ɗaya sai yace.
“Wayyo hannuna”.
Ita kuma sai ta fashe da dariya ahaka dai har akayi ashirin tana ƙyalƙyala dariya kamar ba ita ke kuka ba yanayin yanda ruwan ke sauƙa a fuskarta sai ya zama fuskar ta wanku fes juyawa tayi kan abin alwala ta wanke fuskarta sai ta juya ta kallesa lokacin daya kade na 25 yana ƙoƙarin maida bocket ɗin inda ya dauka tare da sanya ɗankwalin acikin kana yace.
“Wayyo Hannu na ya mutuuuuu”.
Dariya ta sanya tare da faɗin.
“Nima haka nakeji duk randa aka sani kaɗe ɗankwalin nan na koma ko rubutu bana iyawa sai dai Haiydar ya min kaima yau kaji yanda nake ji”.
Juyawa tayi ta nufi hanyar fita.
Da sauri ya tsaya gabanta yace.
“Toh Ni yanzu ko rigana ma bazan iya cirewa ba gashi duk ya jiƙe ki taimaka min ki cire min”.
Kafaɗa ta maƙale tace.
“Um-um nima ai idan ka sani da kaina nake cirewa kacire ka gani kaima idan zaka iya ka dai ji yanda nake ji”.
Cikin langwaɓar da kai yace.
“Toh shikenan”.
Sai kuma ya tsugunna ya kamo ƙasa Jallabiyar ahankali ya zaro tare da faɗin.
“Wayyo hannuna”.
Cikin sauri Khausar da takai bakin kofa zata fita ta juya jin maganarsa dariya ta ƙyalƙyala dashi.

Yana cire Jallabiyar ya saƙale ahanga dake ban ɗakin.
Ita kuwa ahankali ta zubawa sajensa dake ƙyalli ido sai kuma ta maida idanunta kan gashin ƙirjinsa dake kwance luf-luf.
Ahankali ya matsa kusa da ita.
Yayinda ita kam baki ɗaya idanunta na kan ƙirjinsa.
Yana isa jikinta ya janyota kana ya rungumeta aƙirjinsa yana saki wani sanyayyan ajiyar zuciya kanshi ya cusa tsakanin wuyanta da kafaɗarta a hankali ya kai bakinsa saitin kunnenta yace.
*“Minha vidaa* Kin huce ko? Kinji daɗi kinsa mijinki wahala?”.
Kai ta Jinjina tace.
“Eh amma dai zaka ƙarasa saura guda 25”.
Cikin sauƙe numfashi ya shaƙi ƙamshin ta yace.
“In dai zakiyi dariya kaɗewan zai saki farin ciki ko guda dubu kike so zanyi miki *Minha vidaa*”.
Lumshe idanunta tayi.
Shikam ahankali ya riƙa cusa yatsun ƙafansa ƙarƙashin ƙafanta wanda yasa dole ta daura tafin ƙafan ta akan rumfar ƙafansa yana jin haka ya manna kanta da ƙrjinsa ahankali ya fara ɗaga ƙafansa yana takawa har suka fito yana tafiya da ita, ɗin yaja ƙofan ya rufe...
Chapter 102 · 0% Book details