← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 150

Sashe 17

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Moddibo kuwa yana shiga falonsa ya maida ƙofar ya rufe, kana ya zame tare da zama aƙasan daɓas ya jingina bayansa da jikin ƙofan Falon lokaci ɗaya yashiga kokuwa da numfashinsa dake ƙoƙarin ɗauke wa.
Atake wani irin azabebben kuka mai gunji ya kufce masa cikin raunin murya da tsantsar tashin hankali ya shiga furta.
_“Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha Ya wadud³ ya zul'arshil Majeed ya fa'alillima yurid As'aluka bi izzatil lati layura wa mulki kallazi la yurad Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n_”.
Cikin wani irin tashin hankali ya cigaba da karanta duk wata addu'a da tazo bakinsa.
Kana wani azabebben kuka mai sa rawan jiki ya sake kufce masa lokaci ɗaya wani masifaffen zazzaɓi ya rufe sa cikin kiɗima ya fara zantukan zuci. Aransa yace.
Innalillahi Wa'inna ilahi rajiu'n. Shin wannan wace irin Masifa ce? wani irin rayuwa ce take fukantoni! sannan inane tushena.
Ko-ko dai da gaske ne kalmar wannan matar gskyace, cewa bani da asali.”
Sai kuma ya rumtse idanunsa da ɗan karen ƙarfi.
Tare da fara ƙanana mgn a saman lips dinsa dake tsuma.
“Hahhhh da ƙamshin gaskiya acikin kalaman matar nanfa, domin da inada tushe da asali da tuni Innayi ta kaini garesu sannan ta nuna min tushena shin da gskene kenan bata hanyar aure sunnanr Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama aka samar da niba Yah salam.”
Sai kuma ya fara mgn cikin rawan murya.
“Ya Ubangiji Allah kada kasa zargina da zatona na tsawon shekaru ya tabbata ta wajen furucin wannan matar.”
Ya ida mgnar tare da kife kansa bisa guiwowinsa.
Domin shi akaran kansa ya daɗe yana tunanin wataƙil shi ɗan shegene shiyasa Innayi bata taɓa faɗa masa Asalinsa ba kuma bai taɓa ganin wani saba dangi na gefen uwa ko uba, ya kuwa san bazai taɓa yiwuwa ace kab duniya bayi da wani ɗan uwa ko ƴar uwa da za'ace nase sai dai in har shi ɗin ɗan Shegen ne, shiyasa Akullum yake tsoron tambayarta wanene shi domin kada yaji abinda zai tarwatsa masa ƙwaƙwalwarsa da kuma lissafin sa sabida tsoron hakanne yasa baya bincike kan tushensa sabida shi kansa ya fara zargan lamarin.
Lumshe Idanunsa yayi hakan ne ya bawa hawayen ciki damar kwaranyowa da masifar zafi suka zubo masa, cikin ransa yace dama nasani dole irin wannan ranan zai zo ranan da wasu mutane zasu fuskance mu gaba da gaba su tuhumi nagartata. sannan su kirani da shege idan har basu samu gamsasshiyar amsaba. Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.

Hajja Nana kuwa Afusace ta fita daga gida tare da buga Murfin gate din tana zuwa ta buɗe motar tashiga tana wani irin huci na tsananin ɓacin rai da takaici kallon Baffa Jimeta tayi kana tace.
“Mu tafi baki ɗaya mutanen cikin wannan garin basu da hankali basu san abinda suke yiba”.
Cikin sanyin murya Baffa Jimeta yace.
“Subhanallah Hajja Nana kada kice haka kada kiyiwa baki ɗaya mutanen garin nan kuɗin goro sam hakan be cancantu ba”.
Harara ta watsa masa kana cikin fushi tace.
“Rufe min baki kaja mota mutafi bana son maganar banza”.
Kai ya gyaɗa kana yayiwa motar key suka bar kofar gidan kai tsaye hanyar Jauro yaya suka nufa.

Anutse Malam Liman ya juya tare da kallonta kana cikin sanyin murya yace.
“Kiyi haƙuri Hajja Nana ita rayuwar nan na duniya komai sai da haƙuri ake fuskantar sa, abinda fa hakuri bai warware saba tofa rashin haƙuri ba zai warware saba, dan Allah ki kwantar da hankalin ki koma menene Khausar tayi yarinya ce bazaki sa shi amizani da zai tayar miki da hankali har haka ba”.
Cikin sauri Hajja Nana data tsirawa madubi ido ta juya ta kallesa kana cikin fushi tace.
“Wai Ni Khausar zata dubi tsabar Idona tace bata son Aliyu”.
Anutse Baffa Jimeta dake driving ya dan juya tare da kallonta kana cikin sanyin murya yace.
“Toh Hajja Nana menene aciki dan Khausar tace batason Aliyu ainima kaina bazan yiwa Khausar auren dole ba, duk da cewa Aliyu ya kasance ɗana amma bazan tauyeta in Aura mata shi adole ba tunda bata son shi”.
Afusace Hajja Nana ta buga masa tsawa tare da faɗin.
“Rufe min baki me kake nufi kenan?”.
Ahankali ya sassauta muryarsa cike da girmamawa yace.
“Hajja Nana kiyi haƙuri ki gafarceni Idan har abinda zan faɗa zai ɓata miki rai, amma abinda nake nufi a aura mata wanda take so.”
Sheƙeƙe Hajja Nana ke Kallonsa da Idanunta dake cike da Masifa cike da iko da kuma Izza tace.
“Wannan ne kuma baku isaba ba'a haifi wanda ya isa ya ƙaddamar da wannan abin ba”.

Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauƙe tare da kallon Baffa Liman daya tsirawa titi idanu kana ya sake sassauta muryarsa tare da cewa.
“Dan Allah Hajja Nana ki gafarceni Ayiwa yarinya abinda take so”.

“Bafa ku isa ba”.
Ta faɗa a taƙaice.
Kai Baffa Jimeta ya gyaɗa batare da yace Uffan ba ya cigaba da Driving.
Ahankali Malam Liman ya sauƙe Ajiyar tare da juyawa ya fuskanci Hajja Nana da kyau kana yace.
“Adda Hajja to dan tace batason Aliyu shine hankalin ki ya tashi haka?”.
Sake baki Hajja Nana tayi tare da cewa.
“Au don ne ma kake cewa, wato baka ɗauki abinda muhimmanci ba, wannan ɗin bai kai hankalina ya tashi bane?Sannan ma wanda tace tana so ɗin dama ace mutum me tushe ne da asali to ai da sauƙi”.
Dogon numfashi Malam Liman yaja tare da sauƙewa kana yace.
“Toh waye ne tace tana son din ne?”.
Dogon tsaki Hajja Nana taja tare da yin ƙwaffa kana tace.
“Wai wani Malamin Makarantar sune, Moddibo ne ko Momodu ne ohon mata, wannan yaron dai da Malam Arɗo yaje dashi Jauro yaya ashekarun baya sannan akwanakin baya muka je muka sameshi agidan Malam Arɗon tofa wai shi take so”.
Jinjina kai Malam Liman yayi alamun ya gane.
Ita kuwa cike da takaici ta cigaba da cewa.
“Toh Jikan wannan Ƙawar tawa Innare, kuma sanin kanku ne tunda nasha baku labari cewa babu wanda yasan asalinsu, sannan babu wanda yasan tushen su a iya binciken da nayi a iya sanin su da nayi muke zuwa Makka tare yaron nan ɗan shegene”.
Cikin sauri Baffa Jimeta dake Driving ya juya ya kalleta jin furucin daya fito daga bakinta.

Harara ta galla masa kana ta cigaba da faɗin.
“Ɗan shegene bashi da asali ɗane da aka haifeshi ta hanyar zina ta ƙazantacciyar hanya, shin taya zamu haɗa alaƙar aure dashi kalen ya lalata mana sunan zuri'a asamu abin faɗa aciki.

Girgiza kai Malam Liman yayi kana ahankali ya juya da fuskarsa gareta ya fuskanceta sosai yace.
Um-uhum kiyi haƙuri Addah Hajja kada ranki ya ɓaci”.
Girgiza kai tayi tana huci tace.
“Ai dole raina ya ɓaci Liman”.
Gyara Alkyabbar sa yayi kana yace.
“Dan Allah kiyi haƙuri amma kada ki sake aibanta yaron, domin koda maganar ki hakan take, sam bai da ceba duk da cewa kin bada hujjarki akan cewa shi shegene, tofa koda ya kasance shegen ba laifinsa bane, laifin Iyayensa ne da suka haifesa ta hanyar zina”.
Tallafe kunci Hajja Nana tayi tare da tsira masa ido babu keftawa, Malam Liman kuwa cikin sanyin murya da son nusar da ita ya cigaba da cewa.
“Sannan babu inda Shari'a ta hana Auren wanda aka haifesa ta hanyar zina.
Shari'a bata haramta Aurensa da Khausar ba, bai haramta ba a musulunci sai dai idan har akwai wani na ƙasu atare dashi wanda yake aikatawa shine zai zama lalura, sannan dan Allah irin wa'annan kalaman idan zaki furta su ki rinƙa tauna su saboda suna da nauyi”.

Atsawace ta kallesa kana tace.
“Liman Karka fara yimin wannan wa'aze wa'azen'kan nan masu sauya ra'ayi mutum”.
Cike da ladabi malam Liman ya sunkuyar da kansa ƙasa kana yace.
“Dole ne in fara yimi ki wa'azi, domin kada ki faɗa cikin furucin da zai kaiki ga fushin Ubangiji”.
Salati ta rafka tare da riƙe haɓa kana tace.
“Ikon mai duka Fadar gaskiyar ne zesa in fada cikin fushin Ubangiji, ko kuma yana da Uban ne ai tun yana jariri yana cikin tsumma da ka gani kasan cewa ƴarta ce ko ɗanta ya haifo shege ya kawo mata shiyasa ta gudu dashi saboda abin kunya yau tsawon shekara talatin harda ɗoriya kenan bata da wata ƙawa sama dani amma koni bansan tushen suba, bansan asalinsu ba sannan bansan daga ina suke ba”.
Girgiza kai Malam Liman yayi kana yace.
“Kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki amma. Duk da haka Addah Hajja baki da hujjar shegan tasa”.
Cikin sanyi ya cigaba da yi mata nasiyya yana nuna mata kuskuren abinda take amma firrr Hajja Nana taƙi sauraronsa. Baffa Jimeta kuwa Uffan bai sake cewa ba har sukayi nisa da tafiya.

Ɓangaren Moddibo kuwa wani irin zazzafan zazzaɓi mai zafin gaskene ya lulluɓe sa wanda gaba ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa.
Innayi dake tsaye ɗaki ma baki ɗaya jikinta rawa yake sai Safa da marwa take daga ƙarshe ta zame ta zauna kana ta fashe da kuka cur-cur-cur tamkar ƙaramar yarinya cikin Muryan kuka tace.
“Bansani ba Aliyu bansan wannan abin zai zame maka tabo ba acikin al'amuran kaba, bansan zai zame maka na ƙasu da kuma abin nunawa acikin al'amuran kaba Aliyu”.
Cikin tsanananin tashin hankali da tarin damuwa take maganganu tana zubar da hawaye.
Chapter 17 · 0% Book details