← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 150

Sashe 22

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri Mommy ta rintse Idanunta Hawaye masu zafi suka zubo mata ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe kana yace.
“A lokacin sai mahaifinsa yace.
“In sha Allah a gaban idon ka nema Jameeluna ina zakaje”.
Sai yayi murumshi tare da sunkuyar da kansa murya a sanyaye yace.
“Wata ƙil kafin nan na tafi Marocco ko wata duniyar. Dan haka ga mata na zaɓawa Moddibo koda bayan bana nan Abba ayi ƙoƙari ahaɗa auren Moddibo da Khausar sai Abban sa yace to Meyesa kace haka sai yace wa Mahaifinsa shi dai yana fata kuma yana buri ahaɗa auren Moddibo da Khausar domin Moddibo yana ɓuƙatar Aure fiye dashi shiyasa ya fara yi masa zaɓin mata”.
A hankali Lamiɗo ya fesar da numfashi mai zafi kana ya cigaba da cewa.
“Sannan Marigayi Jameelu ya sanar da mahaifiyarsa maganar kana ya sanar da Kakar Moddibo maganar har ta kira Malam Arɗo ta sanar dashi maganar domin wasiyya ce alokacin yake cewa ayi ƙoƙari ayi auren cikin gaggawa domin Moddibo yana bukatar aure shiyasa yake so ayi kokari ayi auren cikin gaggawa koda baya nan babu wanda baisan da maganar ba sai Moddibo shiyasa shekaran jiya suka zo akan neman alfarma ga Uzurin da suka zo dashi”.
Sai kuma ya numfasa kana yaci gaba da cewa.
“Akan wasiyyar da yabari toh na faɗa musu lallai Nine mariƙin Khausar Kuma Khausar tamkar ƴa take awajena, saidai bani da iko da kuma ƴan cin da zan bada Auren Khausar garesu batare da izinin Yayan mahaifinta ba da kuma sahalewar kakarta”.
Gyara zama tayi tare da kallon Mommy da tayi sanyi hawaye na zuba daga idanunta numfashi ya fesar kana yace.
“Toh nace suje bayan kwanaki zasu jini, toh dana niyyata zamu je Jauro yaya muyi wa Hajja Nana bayani sannan mu faɗa mata wasiyya ne duk abinda ake ciki dama nace idan muka dawo zan faɗa musu”.
Kallonsa kawai Mommy take bako kyaftawa tana sake jin tsoron Allah Mabuwayi gagara Misali aranta cikin sanyin murya Abba ya cigaba da cewa.
“Kuma tunda kika ji Khausar ta furta haka wataƙil itama akwai abinda ta sani acikin wannan al'amarin”.

Dogon numfashi Mommy taja tare da fesarwa kana ta lumshe Idanunta hawaye masu zafi suka zubo ahankali ta sunkuyar da kanta cikin raunin murya tace.
“Allah sarki toh Ubangiji Allah ya jikansa da rahma idan al'khairi ne Allah ya tabbatar idan kuma ba al'khairi bane Allah ya sauya musu da mafi al'khairi”.
Jinjina kai Lamiɗo yayi tare da sauƙe numfashi kana yace.
“Yawwa Aysha yanzu kika gane addu'ar da zaki yi kenan, sannan kada kiyi fushi da Khausar fadan nan dakike yi bashi da amfani zama zakiyi da ita ki fahimci Meye dalilinta na fadar haka”.
Kai ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.
“Toh shikenan Insha Allah zan kiyaye”.

Sai da aka kira sallar azahar Lamiɗo ya fita ya tafi masallaci kana Mommy ta miƙe ta nufi sashenta tana shiga falon ta fara jiyo sheshsheƙan Kukan Khausar abakin ƙofar Bedroom ɗinta ta tsaya tare da ɗaga labulen ta kalli Khausar ba yabo ba fallasa tace.
“Idan kin gama kukan ki tashi kije kiyi al'wala kiyi sallah”.
Cikin sanyi ta gyaɗa mata kai kana ta miƙe tashiga toilet ta ɗaura al'wala ta fito Anutse ta gabatar da sallah.

Mommy ma na shiga Bedroom ɗinta ta ɗaura al'wala sannan ta gabatar da sallah.
Bayan Khausar ta idar da Sallah kai tsaye ɗakin Mommy ta nufa.

Acan ɓangaren Hajiya Lami kuwa zaune take akan kujera taji ƙa garin magani da tsamiya da kuma ruwan zafi ta kalli Samira dake zaune gefenta ta zabga ta gumi cikin sanyi tace.
“Gashi ki karɓi maganin kisha dama wannan yace sai da rana-rana zaki riƙa sha wanda kika sha jiya da daddare kuma dare-dare zaki sha”.
Karɓan kofin Samira tayi tare da tsira masa Ido ganin yanda ta tsirawa kofin Ido yasa Hajiya Lami cewa.
“Kisha mana”.
Cikin raunin murya Samira tace.
“Mommy nifa na jiya da daddare nan ma dana sha babu abinda ya ragu saima zubar ruwan daya ƙaru”.
Ahankali Hajiya Lami tace.
“Toh Sokuwa wataƙil ruwan ai zai zube ne ya gama ƙarewa idan ya gama zuba shikenan magana ya ƙare”.
Cikin raunin da tashin hankali Samira ta kalli mahaifiyar ta da Idanunta dake cike da ruwan hawaye kana tace.
“Toh Mommy ruwan fa da ƙarni da wari yake zuba yanzu ma bakiji yanda nake ƙarni ba?”.
Cikin tsinkewar zuciya ta kalli Samira sai kuma ta basar domin bata son bawa ƴartata tsoro amma baki ɗaya hankalinta ya tashi kar dai ƴarta ta samu wata matsala numfashi ta fesar tare da kallonta kana tace.
“Ni dai banji wani wari ba hancin kine dai da shegen jiye-jiye kina nan da hanci kamar na kule ke dai kisha magani tunda yace kisha na tsawon sati biyu kafin mu koma”.
Zare ido tayi cike da tashin hankali tace.
“Mommy har sati biyu kuma?”.
Kai Hajiya Lami ta gyaɗa kana tace.
“Eh saboda zaiyi tafiya so koda munje baza mu same shiba”.
Ajiyar zuciya Samira ta sauƙe tare da cewa.
“Toh bari in sha”.

Aɓangaren Naseer kuwa zaune suke afalon Mahaifiyar sa da Addarsa Hindu da kuma Mahaifiyar su Hajiya Kubra yayin da akwatuna ke jere agabansu cikin su sanye da Atamfofi, Leshuna, Shadda, English wear, Turaruka, Mayuka,Takalma.
Gyara zama Naseer yayi tare da kallon Addah Hindu murmushi ya sakar mata tare da ɗage mata gira ɗaya kana yace.
“Insha Allah Addah Hindu burina ya kusa cika”.
Murmushi tayi tare da jinjina masa hannu kana tace.
“Ƙwarai kuwa nan da ƙanƙanin lokaci ma kuwa”.
Gyara zama Hajiya Kubra tayi tare da kallon Naseer tace.
“Toh yanzu me yarage acikin kayan Auren nan ba asaba!?”.
Ajiyar zuciya Naseer ya sauƙe tare da cewa.
“Kayan Aure kam yanzu ai kusan an gama komai kawai yanzu gishiri da goro za asiya sai kuma sadaki i think suka ɗaine suka rage”.
Kai Addah Hindu ta gyaɗa tare da faɗin.
“Eh saura kayan rufi ba ahaɗa ba”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Toh badamuwa yaushe za akai?”.
Kallon akwatunan tayi kana ta kallesa numfashi ta fesar ta da sakin murmushi tace.
“Idan Allah ya yarda nan da sati za akai saura gyalullulka dana aika akawo min daga Kano basu iso ba tukunna”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Toh ba matsala sai sun iso”.

Bayan Moddibo da Abba sun idar da sallar Azahar Amasallacin Kofar gidan Abba kai tsaye gidan Ummi suka nufa bayan sun isa Moddibo yayi Parking suka fito daga motar kana suka tsaya daga coumpund ɗin Moddibo yayi sallama daga ciki Malam Ahmad ya amsa kana ya fito ganin Abba yasa ya faɗaɗa Murmushin fuskarsa tare da cewa.
“A'a Alh Bashir yau har da kaine agidanmu sannu da zuwa sannu da zuwa maraba lale ku iso mana”.
Kai Abba ya girgiza kana yace.
“A'a nan ma yayi”.
Ahankali malam Ahmad yace.
“A'a bakomai Abban Jameel mu shiga mana ai an zama ɗaya haba dai mushiga dan Allah”.
Murmushi Abba yayi cikin sanyin murya yace.
“Toh shikenan Nagode”.
Sannan suka nufi falon Ummi Asma'u dake zaune ta miƙe tare da yi musu Barka da zuwa kana ta koma kichen ta dauki Plate ta kawo musu ruwa da drinks da kuma Fruit ta ajiye masu kana ta Gaishe su cike da ladabi.
Ahankali Moddibo ya jingina bayansa da jikin kujera ya lumshe idanunsa baki ɗaya ya tsani garin Gembulan da jahar Taraba ji yake tamkar ana yayyafa nasa garwashin wuta ajiki baiƙi ace ko yaushe yana ɗaki baya fita ko ƙofar takashi ba.

Ummi dake Bedroom zaune kan Sallaya ta miƙe ta fito jin muryan Asma'u na gaishe da Moddibo kana tace.
“A'a Moddibo ne”.
Ganin Abba zaune yasa ta tsaya cike da Mamaki tace.
“A'a Alhaji Bashir”.
Cikin sanyin murya Abba yace.
“Na'am Fatima”.
Kallonta Malam Ahmad yayi sanye take da hijabi har ƙasa hannunta riƙe da Carbi cike da kulawa yace.
“Ki ƙara so mana ku gaisa”.
Kai ta gyaɗa tare da ƙarasawa ta zauna daga gefe.

Anutse Moddibo ya daga kai ya kalleta kana yace.
“Ummi ina yini”.
Kallonsa Ummi tayi ba tare data amsa gaisuwar ba tace.
“Babana jiya duk baka leƙoni ba”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Eh Ummi”.
Cikin sanyin murya tace.
“Kuma na kira wayarka baka ɗaga ba sai nayi tunanin ko kana bacci ne?”.
Kai ya girgiza tare da sunkuyar da kansa ƙasa yace.
“Kuma Ummi ban kulaba ban miss call ɗin ba”.
Jinjina kai tayi tare da fadin.
“Ayyah”, Kana suka gaisa.

Anutse Abba ya kalleta tare da cewa.
“Fatima ina yini”.
Ahankali ta gyara zamanta tare da faɗin.
“Lafiya”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ya muka ƙara ji da haƙuri”.
Lumshe Idanunta tayi kana tace.
“Haƙuri ya zama dole”.
Jinjina kai yayi tare da cewa.
“Toh Allah yajiƙan Jameelu Ubangiji ya masa rahama”.
Baki ɗayan su suka amsa da Ameen ya Allah.
Gyara zamansa yayi kana yace.
“Fatima kada ki yiwa Jameelu kuka ki tayi masa addu'a shine abinda ya dace kinji ko?”.
Kai ta gyaɗa tare da sunkuyar da kanta ƙasa tace.
“Insha Allahu bazan yiwa Jameelu na kuka bai Insha Allah zan ta binsa da addu'a”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Hakan yafi”.

Anutse ya gyara zamansa tare da kallon Moddibo da kansa ke ƙasa kana ya kalli Ummi da itama still Kanta ke ƙasa ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Dama nazo da Moddibo ne inne ma masa uzini awajenki”.
Cikin sauri ta ɗago kanta tare da Kallonsa tace.
“Izinin me kuma?”.
Numfashi ya fesar tare da cewa.
“Dama Abune da yashafi kasuwanci na acan Company mu na Marocco wanda Jameelu ne yake komai na Company nin toh kuma yanzu kin gani Allah ya dauke mana Jameelu”.
Cikin sauri Ummi ta lumshe Idanunta tare da gyara wuyan hijabinta.
Chapter 22 · 0% Book details