← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 150

Sashe 60

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa Modibbo kasancewar yana fuskarta ta inda suke tahowanne yasashi saurin ware idanunshi a saman lips enshi yace.
“Asma'u?”. Yayi mgnar da ko Ibraahim dake gab dashi baijiba, cikin son fahimtar me ke faruwa ya kuma kalli Asiya sai kuma ya maida idonsa kan Asma'u dake sakin murmushin, shi kuwa idon shi ya maida ƙasa tare da fara kallo su daga ƙasa.
Ahankali suke taka kan stairs din da yasha red carpet me masifar kyau da ƙawa yayinda kan ko wanne step akwai Hadimai gefe da gefe suna riƙe da kaskon turaren wuta.
Asmau ce ke gefen damanta yayinda Asiya kuwa ke gefen hagunta, sai Dije dake gefen Asma'u.
Sai kuma wata ƴar matashiyar Haɗina dake bayanta wacce ita ke riƙe da mayafin da aka sanya mata akanta, wanda saboda tsabar tsawonsa har jan ƙasa yake yi.
Sunyi matukar kyau da burgewa, hakan yasa duk aka maida kallo kansu.
Tafiyarta me tsananin jan hankali da ma’ana, haɗi da tsananin ƙawatuwar da shigar nata shiya sanya Modibbo dake tsaye zuba mata ido, duk da cewar baya iya ganin fuskarta, amma tsananin annurin da take fitarwa ya cika masa ido, yayinda takun da takeyi me kama da tafiyar ɗawisu ya tsaya masa arai, domin yanajin tamkar ya taɓa sanin me wannan tafiyar, tabbas ya taɓa ganin irin tafiyar.

Jin ana shelar amarya ta iso tare da fara zuba kirari.
Amarya Fatima Zahra mata a gidan Aliyu Youseep Mouleey.
Da sauri ya rumtse idanunsa da ƙarfi dan so yake ya nazarci kalaman.

“Amaryar kuma? Toh amaryar waye? meyasa naji ana kiranta da matarta, wace matarta kuwa? me suke nufi? Yaushe aka aura min ita? Toh ma wacece ita? Shin wai su waɗannan me suke nufi dani? da zasuyi ta juya min rayuwa suna sarrafa min abinda basu nemi izininaba". waɗannan tambayoyin su suka cika zuciyarsa da ta samu kanta cikin tsananin ruɗani.
Shin me ake nufi dashi ne? me sukeson maidashi? wani irin aurene wanda akayishi babu saninsa? Bare sahalewarsa, toma uban waye yace musu shi ya shiryawa aure a wannan taƙin.
Ya kuma yiwa kansa tambayar yana me tsareta da idanunsa, duk da cewar baya iya ganin fuskarta saboda mayafin da aka sanya mata.
Ji yayi kansa na wani irin juyawa zuciyarsa kuma na bugawa da ƙarfi, so yake ya buɗi bakinsa ya cewa Sheykh Jabeer shifa kada a liƙa mishi wata jarabar amman ina ya gaza sabida ruɗanin da yake ciki.

Sun Khausar kuwa ahankali suka ƙaraso cikin parlorn, wasu daga cikin Hadiman dake ta hidima ne suka nunawa Asma'u Asiya da Dija, wajan zaman da aka tanada musamman domin su, haka yasa cikin nitsuwa su Asma'u suka nufi wurin zamansu, yayinda Hadiman kuma duk suka zube a ƙasa.
Yayinda su Lalla Salma kuwa suka nufo da ita wajen dasu Modibbon ke tsaye.
Da sassarfa Rahama ta taso ta biyo bayansu.
Lalla Salma ce ke rike da Khausar yayinda kowani taku ɗaya da sukeyi na kusanto inda Modibbo yake.
Hakan ke kara duk’unzuma tunanin Modibbo, wanda yakejin abubuwan suna zuwa masa awasu yanayi na daban.

Dab dashi Lalla Salma ta kawo Khausar din, tare da sakin hannunta, da sauri Rahma ta ƙaraso hannunta rik’e da wani babban glass bowl wanda cikinsa ke d’auke da kyakkyawan furanni masu fitar da sassanyan k’amshi.
Cikin tsananin farinciki ta soma watsa musu furen, Lalla Salma kuwa matsowa kusa dashi tayi, tare da ɗan ranƙwafowa ahankali tace.

“Abisa al’ada Aleey kai zaka buɗe fuskar amaryar taka ka juyata ta fuskanci family inka su ganta da kyau, kayi Bismillah ka bud’e fuskarta, idan ka juyata an ganta sai ka riƙe hannunta ku zauna bisa kujerar nan ka tabbatar kun zauna da bisimilla.”

Cikin sauri ya kalleta hadi da kallon Ibraahim dake gefensa na dama, sunkuyar dakai Ibrahim yayi kana cikin yin kasa da murya yace.
“Dan Allah Yah Aleey kayi abunda Lalla Salma tace, kada kayi abunda za muji kunya, kar kayi abunda zaisa mutane su fara tunanin babu abunda ka sani adangane al'adun masarautar da ake tunani za’a damƙa maka ragamarta a hannunka, kayi hakuri dan Allah Yah Aleey!!”

Ya k’are maganar cikin magiyan, da yasa Modibbon juyawa ya kalli Didi da ta tsura masa ido.
Sai kuma ya ɗan juya idonshi ya kalli Innayi wacce itama kallon nasa take, tare dayi masa alama akan yin biyayya.

Idanunsa ya dan lumshe tare da shakan numfashin dake kokarin kwace masa sabida tsanantan bugun da zuciyarsa keyi.
Cikin bada umarni Sheykh Jabeer ya ɗan matse hannunsa dake cikin nasa, kana ya ɗan rongofo tare da faɗin.
“Kayi abinda ya dace, umarnin kakarkace macen da tasha wuyan rainonka tsawon shekaru, kana kuma fata ne da burin mahaifiyarka data raini cikinka tsawon wata tara da kwana tara, sannan burin mahaifinka kanan”.
A hankali ya buɗe lumsassun idanunsa lokaci da yaji zuciysrsa na bashi umarni.
“Buɗe kaga wacece?”. ji yake wani abu na fusgarsa, batare da sani ko shiryawa hakan ba, sai ji yayi hannayensa na motsi, duk da karkarwar da suke.

Ganin haka yasa Rahma dake bayan Khausar ɗan turo Khausar din tare da cewa.
“Yes my Aunty jeki kusa da mijinki ya buɗe mana fuskarki mu ganki”.
Sai kuma ta ɗan ƙara ɗan tureta kaɗan da kafaɗarta, wanda haka yasa Khausar da zuciyarsa ke buga lugude tara-tara ta ɗan yi motsi kaɗan da yaɗan ƙara kusancinsu da Modibbo.

A hankali ya ɗan ɗago hannunsa, yatsunsa biyu yasa gefe da gefen mayafin nata ya kamo tare da d’an d’ageshi sama, yanajin zuciyarsa nayi masa wani irin duka uku uku.
Yana janye mayafin kuwa kyakkyawar fuskarta na bayyana.

Cikin wani irin baƙin al'amari ya zazzaro idanunsa cike da kad’uwa had’i da mamakin ganin fuskar Khausar, wani irin masifeffen kasalane ya rufe mishi jiki da zuciya, a take kuma yaji wani irin abu mai masifar sanyi ya tsoki ƙahon zuciyarsa, kana a take ya kuma jin wani irin abu daya harba daga tsakiyar maɗigan kansa, ya game dukkan sasanjikinsa, har zuwa kan babbar yatsarsa, wani abu me kama da mamaki, hadi da mutuwar jiki ne suka lullubeshi lokaci d’aya.
Bak’on yanayi me kama da zazzafar bege da bai tab’a jiba ya lullube dukkan jikinsa, dake wani irin tsuma.
Hadi da sanya masa wani yanayi na kaucewar tunanin.
Wanda ya sashi bud’e hannayeshi tare da ware tattausar al'kyabbar dake jikinsa.
Wanda ganin hakan yasa Rahma ɗan ƙara tura Khausar, kasancewar takalmin da ta sanya me tsinine hakan yasa ta tafiya garesa batare da ta shiryawa hakan ba.

Shi kuwa Modibbo wani irin mataccen numfashi yaja tare da fesar da sassayan numfashi mai dogon sauti.
Kana ya yayi mata Kekkyawan masauƙi a ƙirjinsa tare bata cikekkiyar kariya
da yalwatacciyar alƙyabarsa ta hanyar bata wani irin kyakkyawan runguma, me ɗauke da ma’anoni masu tarin yawa, da yafi kama da tsananin shauki hadi da zallar kewa da bege.
Rungumeta yayi tsam a cikin jikinshi ya mannata da ƙirjinsa da ƙarfi har yakai ga suna iya jiyo ɗumin jikin junansu wanda kuma tuni yayi mata garkuwa da yalwatacciyar Al'kebbar jikinsa mai cike da ni'imtaccen ƙamshi.
Lib Khausar tayi a jikinshi tare da shaƙan numfashi daya wadatu da ƙamshin turaren jikinsa wasu irin tagwayen numfarfashi take fesarwa tare da lafewa a jikinshi da kyau tamkar mai tsoron kada a janye mata shi haka nan takejin tamkar a barta ta rayu a kunshi a haka har gaban abadan haka yasa ta liƙe lip a jiki nai.

Shi kuwa Modibbo a hankali ya lumshe idanunsa tare da laso gefen lip inshi sama,

Yanayi ne na musamman a garesu, daya sanya su lumshe jujjuya kwayar idanunsu a tare, musamman ita Khausar da taji ya lulluɓeta da alkyabbarsa.
Wata duniya ce ta daban me shiɗarwa suka lula.
Cikin wani irin aminci da salama Modibbo ya ɗan sunkuyo kanta kaɗan tare da kawo bakinsa dai-dai saitin kunnenta.
Cikin sarƙafeffiyar muryarsa me kama da raɗa,cikin tsananin sanyi, ta yanda ita kadai zata iya jiyoshi atausashe yace.

“I miss you my trouble maker. I really miss you my trouble student.”

Wow gaba ɗaya falon ya kacame da tafi da sowa.
Sai kuma sarewar da ta karaɗe falon.

Ummi kuwa wani irin amintaccen numfashi ta fesar.
Yayinda Didi kuwa tayin ƙasa da kanta tana sakin murmushin.
Su Lamiɗo da Malam Arɗo kuwa duk ƙasa sukayi da kansu cikin konciyar hankali.
Haiydar kuwa wayarshi ya zaro tare da fara musu video, hakama Rahama.
Yayinda tuni kuma masu ɗaukar hoto suka fara kebta musu.

Zakariyya ne ya ɗan zunguri kafaɗar Modibbo da tashi kafaɗar tare da cewa.
“Kai Jinin Mouley a tsakiyar mutanefa kuke, ka ritsa yar mutane kamar zaka maidata cikin ƙirjinka”.
A can sama ya jiyo muryar Zakariyya wanda ya sashi buɗe idanunsa a hankali.
Hango Lalla Khadijah da wasu mata a ƙalla su bakwai ne ya ɗan sashi sassauta rungumar da yayi mata.
Tare da ɗan jan baya kaɗan.
Fuskashi ya ɗan tsuke tare da kara ronƙofo da kanshi a hankali yasa bakinshi dai-dai iunnenta murya can ƙasa yace.
“Toh yau dai burinki ya cika ai, na ruggume ki, hankalinki ya kwanta tunda kinji ɗumin jikina ko? Kin samu abinda kikeso ko”.
Mui-mui tayi da bakinta
Kara matseta ya ɗanyi tare da cewa.
“Rashin kunya zakiyi minko”.
Baki ta ɗan tura tare da cewa.
“Ni ka sakeni”.
Ɗan haranta yayi tare da cewa.
“Kece ai kike riƙe dani mayya uwar son jiki, tashi min a jiki Mage”.
Da sauri ta ɗan janye jikinta kaɗan.
Dai-dai lokacin kuma Khadijah suka iso.
Kusan a tare suka fara yi musu wani irin....!

*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N 09097853276 in tura miki abinki ki karanta cikin salam ba tare da kin karanta na Allah ya isaba*

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 16*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Chapter 60 · 0% Book details