Sashe 41
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin sanyi da son ƙarfafa mata gwiwa Asma'u tace.
“Insha Allah ba zaki taɓe ba Ummi ma tayi farin ciki da wannan auren kowa kin sashi afarin ciki Insha Allah Ubangiji zai dawwamar miki da farin ciki agidan Auren ki”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Khausar ta sauƙe kana yace.
“Ni dai zanyi wannan al'amarin saboda Yah Jameel ne kuma na yarda zan jure duk kan ƙunci, Haranta, Cin fuska, Tozarci, Cin zali da duk wani salon wulaƙanci da Moddibo zai min saboda cika burin Yah Jameel”.
Asma'u kuwa kai ta girgiza kana tace.
“Insha Allah ma ba zai miki ba da yardan Allah ba zaki ƙuntata ba rayuwa ba zata miki ƙunciba tunda Mommy ta sanya Albarka aciki komai zai tafi dai-dai”.
Ta ida maganar tare dasa hannu tana share mata hawaye murmushi tayi ko kaɗan bata son ganin hawayen Khausar cikin son ƙawar mata da damuwarta tace.
“Keda kike amarya wayasan amarya da kuka kuma amaryar ma ango mai tsada matar Yah Moddibo?”.
Harara Khausar ta watsa mata da jiƙaƙƙun Idanunta da Eyelashes ɗinta suka sake zara-zara dasu sai kuma ta tura baki tace.
“Ba wata amarya amarya ko kuma wahalalliya dai!?”.
Dariya Asma'u tayi kana tace.
“Ba wata wahalalliya amarya dai”.
Cikin sanyi Khausar tace.
“Hmmm Asma'u Ni dai hankalina atashe yake ina tsoron Moddibo bansan wani irin zama zamuyi ba”.
A dai-dai lokacin kuwa Samira Sani ce, da Amina ke waya tana gaya mata batun auren MODIBBO DA Khausar, Ya Salam wannan labarin ya girgiza Samira, haka yasa bta cilla wayar bisa gado ma tare da ta katse kiranba.
Da gudu ta nufi ɗakin Hajia Lami, tana shiga ta ganta zaune bakin gado da waya a kunne tane cewa.
“Haba dai Hajia Bunayyah wanne irin aure kuma, innalillahi ya za'a mana haka muna nan muna shiri mun rasa nitsuwa dan jawo hankalin wannan yaro kuma azo ace wannan shegiyar yarinyar ya aura, ya zasu fito mana a bazata”.
Sai kuma ta katse wayar tare da ruggume Samira da ta faɗa jikinta tana kuka wui-wui tare da cewa.
“Mommy shike nan ni kam nayi batam ɓaka tamtam, ni ba budurcinaba, ni ba Modibbo ba, ni ba lafiyata ba ni da zunubin zina da boka, ga ruwa mai wari da ke bibiyata”.
Ta ƙare mgnar da fashewa da matsanancin kukan da yasa Hajia Lami ruggume mata cike da takaici ta fara lallashinta.
Acan Falon Lamiɗo kuwa kallon Mommy dake zaune gefensa yayi ahankali ya sauke ajiyar zuciya kana yace.
“Ɗazun Alh Bukar suka zo maganar Amina da Naseeru to kuma har angama magana anbawa Naseer Amina since Ashirye suke nan da kwana goma suke so dan Ashirye suke”.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“A'a Masha Allah Abu yayi kyau Allah yasanya al'khairi”.
Anutse Lamiɗo ya gyara zamansa kana yace.
“Toh kuma tunda sakaranar yazo abakin gaba kawai za ahaɗa da ɗaurin bikin Khausar”.
Saurin Kallonsa Mommy tayi Asanyaye tace.
“Mai martaba da sauri haka?”.
Kallon yanda tayi da fuska yayi kana yace.
“Toh ke Meye damuwarki aciki?”.
Cike da damuwa tace.
“Toh Babu abinda muka shirya wa bikin nan fa”.
Numfashi ya fesar kana yace.
“Toh na saki ne ko kuma nace kishirya ne?,Ko cokali bansa ki siyawa Khausar ba kibar min ƴata Ni zan mata komai”.
Ya ƙarasa maganar cike da kara, mutuntaka, da kuma dattako.
Cike da kunya da jin daɗin karansa Mommy tayi murmushi kana tace.
“Nagode Allah yasanya musu al'khairi duk abinda kace haka za ayi”.
Murmushi yayi kana yace.
“Haka nake son ji ke dai ki sanya Albarka acikin wannan al'amarin”.
Jinjina kai tayi cikin sanyin murya tace.
“Allah yasanya alkhairi”.
*Morocco*
Cikin fushi Dr Jameel ya watsa wa Moddibo Harara kana yace.
“Haka kawai zaka zo kana takura min rayuwa dan bansa ankore kaba?”.
Cikin wani irin yanayi Moddibo yace.
“Korana?,Kasa akoreni J ni kake cewa zaka kora?J Bismillah in baka koreni ba baka amsa sunan ka Jameel ba”.
Afusace Dr Jameel yaja hannun farkarsa yace.
“Mu tafi Baby”.
Cikin sauri Moddibo yabi bayansa kafin ya fita tuni Dr Jameel yashiga mota, Cikin sauri yashiga motarsa zaiyi reverse yaga wasu motoci biyu sun taresa dole sai anja daya daga ciki kafin ya samu ya fita Dr Jameel kuwa tuni yaja motarsa ya tafi.
Da sauri Moddibo ya fito daga motarsa yace.
“Waye wannan yazo ya tare min mota ta ina zan fita”.
Dai-dai lokacin mamallakin Motar yazo cikin sanyin murya yace.
“Ayyah Bawan Allah kayi haƙuri na ajiye mota abayan naka banyi tsammanin zan daɗe ba abu kawai zan karba”.
Uffan dai Moddibo bai ce da mutumin ba yashiga motarsa yaja ya tafi sannan Moddibo ya shiga nasa yaja ya fita sai dai ba motar Dr Jameel ba labarinsa gefe da gefen Asibitin ya zagaya amma koda wasa baiga alamunsa ba.
Komawa yayi da niyyar shiga asibitin security suka hanasa duk yanda yaso shiga sunƙi barinsa cikin takaici ya juya akalar motarsa kai tsaye Mouley Youssef Hotel Rabat ya nufa cike da tunani iri-iri, yana isa yayi Parking kana ya fito yashiga cikin harabar Hotel ɗin ya shiga reception kai tsaye ya wuce masauƙinsa yana ya sa key ya buɗe ya shiga bakinsa ɗauke da sallama
Zama yayi akan 1sitter ya dafe kansa da hannu bibbiyu cikin sauri ya janye hannu ya ɗauki wayarsa ya kira Number Abba amma har ya katse ba adauƙa ba.
Lokacin da kiran yashiga wayar Abba tuni yayi bacci miss call uku Moddibo yayi ganin bai ɗauka ba yasa ya haƙura ya jinginar da kansa da jikin kushin yasani koda ace J zaiyi ko wani irin basaja ne aduniya ba zaiyu ace anyi masa Aure Iyayensa basu sani ba kuma ga duk kan alamu ma wancan karuwa ce domin tafi kama da karuwai wannan ne ya fara ɗarsa mishi shakku anya wannan J ɗin shi ne kuwa a fili yace.
“Ina inada tabbacin J na ba mazinaci bane, kuma bazai aikata zinaba, shin toh in ba J na bane waye wannan”.
Kanshi ya daddafe da duka hannunsa yana mai rumtse idanunsa da ƙarfi da kuma ƙarfin yace.
“No J bazai kasance haka, ina ba J ɗina bane kuma J na ko allura bai iya yiba ba abinda ma ya haɗashi da likitanci”.
Yayi mgnar da cikekkiyar yaƙini da yarda da hakan sabida yanzu ya fara samun nitsuwa, ya gamsu kawai tsananin kamannine mutumin yake dashi da Jameel ɗinsa wanda hatta sautin muryarsu iri ɗaya ne da J dinsa.
“Yah Salam. Allah mai iko to waye wannan ɗin".
Yayiwa kansa tambayar da yake masifar son sanin amsarta”.
*Gembila*
Ɓangaren Asma'u da Khausar ma haka suka raba dare wajen hira har misalin ƙarfe uku suna zaune suna hiransu ta Aminai daga baya suka koma hiran makaranta wani abin idan sun tuna suyi dariya wani suyi murmushi musamman rigimar kwausar da Modibbo, rayuwa kenan shikenan rayuwar makaranta ta wuce kamar ba ayiba cikin murmushi Khausar ta gyara zamanta tare da kallon Asma'u kana ta ɗan tsuke fuska sai kuma tayi kasa da kai cikin juya murya zuwa irin ta Modibbo tace.
“Ke uwar rawar kai”. Sai kuma taja tsaki tare da cewa.
“Ko sunanafa baya kira wai ke”
Dariya sosai Asma'u keyi tare da riƙe ciki, ita kuma Khausar baki ta ɗan taɓa kana a hankali tace.
“Da jajayen lips inshi a wurin kamar balarabe da dunduniyarsa laushi kamar ta jariyai, gashin ƙeya kamar jikin Mage.”
Cikin nunata da yatsa Asma'u tace.
“Yah Salam ashe har haka akeson Ƴaƴana ban saniba”.
Harara ta watsawa Asma'u tare da cewa.
“Kamar yaya so”.
Tafa hannu Asma'u tayi tana faɗin.
“Toh fisabilillahi in ba soba mai ya kai hankalin da idanunki kan lips inshi harda ƙeyarshi duk yawan sa hulanshi, shin tukun nama ya akayi kika san dunduniyarsa da taushi, na shiga uku ashe Allah ya tsare bawan Allah da kin fyaɗeshi”.
Cikin kauda kai dan sai yanzuma taji kunyar kalamaanta a hankali tace.
“Ba wani nan kin dai san kawai ni ina son mai kyau, haka Allah yayini”.
Ta ƙare mgnar tana lumshe idanunta, a hankali ta buɗesu ganin yadda lips enshi ke motsawa in yana mata masifa.
Haka dai sukayi ta hira mafi akasari kan Modibbo ne yanayi tana kusheshi kushen da yake naɗe da cikekken yabon halittarsa da ɗabi'unsa.
Washegari da safe Misalin shaɗaya bayan sun gama yiwa Mommy Komai suka shirya suka tafi gidan Ummi suna isa suka samu komai fes-fes ta gyara har ta gama girki.
Ummi kuwa murmushi tayi ganin su yasa tace.
“Yawwa ƴan al'barka tun ɗazu nake son zamu tafi gidan Abban Jameel nida Innayi, kuma gidan shiru Bashir ya tafi sabgogin gabansa”.
Khausar na zama tace.
“Ai haka suke Ummi haka ma Haiydar shegen yawo ne da yaran nan”.
Kai Asma'u ta jinjina tace.
“Haka suke kuma idan mutum ya fita na minti biyar su riƙa cewa shine yake yawo.
Murmushi Ummi tayi kana tace.
“Yau ɗauki wannan Asma'u ki ƙaiwa Innayi yanzu na leƙa na samu tana walaha”.
Zare ido Khausar za tayi cikin sauri tace.
“Innayin tana nanne?”.
Da sauri Asma'u tace.
“Ai tunda Yah Modibbo ya tafi Marocco ta dawo nan”.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe ta koma ta zauna tare da faɗin.
“Au”.
Ahankali Asma'u ta jawo kular dake gaban Ummi tana buɗewa tace.
“Yau kuma mai akayiwa Innayi?”.