← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 150

Sashe 128

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Moddibo kam cike da mamaki yake kallon yanda Khausar ke cin ƙosai da Koko tsakaninta da Allah.
Hajja Nana dake kai biredi da Ƙosai baki ta kalli Moddibo daya zubawa Khausar idanu yana cew.
“Ni mamaki nake bata cin abinci fa agida”.
Murmushi Hajja Nana tayi tana kallon yanda Khausar ke shan Koko tsakaninta da Allah tace.
“Ai dama haka wani yake in dai yana da ciki baici agidansa amma da zaran yaje unguwa zai ci abinci”.
Kansa ya girgiza tare da cewa.
“To ai can ko munje gidan Lalla Khadijah bata cin abinci amma kinga tunda muka zo nan cin abinci fa takeyi”.
Momy dake fita zata kaiwa Abba da Man Liman nasu tayi Murmushi tare da faɗin.
“Sosai ma kam tunda aka zo nan abinci take ci babu kama hannun yaro taci ta ƙara ɗayan daren ma munyi hira mun gama tace min yunwa take ji sai da naje na dama mata Quaker oats tasha kafin tayi bacci”.
Cike da farin Moddibo ke sakin murmushi yana kallon Khausar dake ɗan Cunno baki gaba Momy kuwa idanunta akan Hajja Nana ta cigaba da cewa.
“Sannan da safe kafin ta kwanta plate da kuka zo kuka samu shima indomei taci tasha tea kafin ta kwanta tayi bacci anan gashi yanzu ma tana ta ɗurawa”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da faɗin.
“Toh Momy yunwa nake ji na daɗe bana cin abinci fa”.
Dariya Momy tayi kana tace.
“Keee dama haka kike da cin abinci nayi mamaki ma da akace wai ciki ya hanaki cin abinci.
Don banyi tunanin akwai abinda zai hana ki cin abinci ba, tunda ke ciwo ma baya hana ki cin abinci”.
Kanta ta sunkuyar ƙasa ta cigaba da cin ƙosanta kallonta Moddibo yayi ganin ta gama cinye duk ƙosan hannu tasa ta sake janyo kular ɗan ware idanunsa yayi tare da faɗin.
“Minha bazai Miki yawa ba?”.
Kallonsa tayi sai kuma ta girgiza kai tace.
“Um-um kaɗan zan ƙara naji cikina ya ƙoshi amma bakina bai gaji dashi ba”.
Yana rufe kulan yace.
“Toh ki bari sai anjima”.
Marairaice fuska tayi ganin haka yasa Momy cewa.
“Ki bari na rage Miki ƙullu a fridge idan kina so anjima zan sake soya miki ”.
Gyatsa tayi kana ta gyaɗa kai tare da faɗin.
“Toh shikenan”.
Ta ida maganar tana jingina bayanta da jikin kujera.
Ahankali Moddibo ya matsa kusa da kujeran da take ya ɗan jawota jikinsa tare da cewa.
“Zo, Zo zonan kada ki kwanta, ki ɗan zauna tukun mu samu abincin yabi jikinki”.
Ya faɗa yana manna kanta da kafaɗarsa yayin da hannunsa ɗaya ke kan cikinta yana shafawa shi kuma yana cigaba da cin abinci da hannunsa na dama.
Ahaka suka gama cin abinci suna taɓa hira jefi-jefi.

Suna gama cin abinci Momy ta shigo idanunta akan Khausar tace.
“Toh tashi ki tattare wurin”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh”.
Kana ta yunƙura zata miƙe.

Ahankali Moddibo ya kalli Momy kana yace.
“Momy bari na tattare”.
Ɗan ware idanu Momy tayi kana tace.
“Ta isa tana zaune ka tattare mata kwanika”.
Cikin sanyi yace.
“Momy toh ta gaji ne kuma ta cika cikinta da yawa bata son motsi”.
Kai Momy ta girgiza tare da faɗin.
“Aikuwa dole tayi motsi maza tashi ki tattare su”.
Ta ƙare maganar tana kallon Khausar.
Hajja Nana dake kallonsu ta ɗan taɓe baki tace.
“Kai dai kai dai kam wannan akwai ka da tsirfa iri-iri yo in Mai ciki bata motsa jiki ba mai za tayi!? Ko kaine zakayi mata naƙudar”.
Ɗan hararan Hajja Nana Khausar tayi sai kuma ta kalli Momy tare da cewa.
“Nima fa bance yayi ba shi yace zaiyi”.
Ta ƙarashe maganar tana kwashe kwanukan ta kai kitchen kana ta dawo ta zauna bayan ta dawo sun zauna Momy suka gaisa da Hajja Nana bayan sun gaisa suna cigaba da hira.
Asiya ta shigo cikin sassarfa kamar an jefota cikin yanayin tashin hankali tace.
“Momy dan Allah kizo kiga Ummana baki ɗaya yau tunda gari ya waye atsaye take bata zauna ba kona minti ɗaya fa gaba ɗaya yau jikinta ya tashi!”.
Da damuwa Momy ta miƙe cikin sauri tabi bayan Asiya suka nufi Side ɗin Hajiya Bunayya.
Khausar kam ahankali ta juya ta kalli Hajja Nana itama Hajja Nana kallonta tayi sai kuma ta juya ta kalli Moddibo cikin sanyi tace.
“Yah Mu'allim nace maka batun jikin Umma da Amina ayi musu addu'a sannan ka turo Dr Jameel yazo ya duba su amma Yah Mu'allim har yanzu baka ce komai akai ba”.
Ahankali Moddibo ya dafe kansa da hannunsa na hagu yace.
“Wallahi na manta, koyie haƙuri mantawa na keyi Minha”.
Kamar za tayi kuka tace.
“Yanzu fa kaji abinda Asiya tace”.

Hajja Nana da batasan meke faruwa ba ta kalli Khausar tare da cewa.
“Meke damunta?”.
Cikin rauni Khausar tayi ƙasa da kanta kana ta kwashe labarin duk yanda ta faɗawa Moddibo ta faɗawa Hajja Nana.

Ajiyar zuciya Hajja Nana ta sauƙe tare da jinjina kanta tace.
“Ai dama haka duniya take idan kace tukunyar wani bazai tafasa ba naka ko ɗumi bazai yiba arayuwa ka taka ahankali kada ka shiga hurumin da bana kaba duk lokacin daka shiga hurumin da bana kaba sai ka samu abinda zai shiga huruminka”.
Araunane Khausar ta risinar da kanta Hajja Nana kuwa cikin jimami ta cigaba da faɗin.
“Ya hanaka zaune ya hana ka tsaye yanzu wa gari ya waya ita wancan ta haukace ƴarta ta zama mai wari ita gata nan ƴarta ta zama wata halitta daban gashi ita kuma yanzu ƴarta tazo tana cewa tunda gari ya waye bata zauna ba ta isa ta zauna tsutsotsi na cinta”.
Ahankali Khausar ta rausayar da kanta hawaye na kwaranyowa daga idanunta tace.
“Hajja Nana Ni tausayi suke bani musamman Amina tana bani tausayi gaba ɗaya sai kinga yanda ta dawo ita ma Umman na ban tausayi bata isa ta zauna bafa Hajja Nana wlh ko jiya data shigo nan mu gaisa tsutsotsin har bin ƙafarta suke yi sai in taji kiga tana ta buge-bugen ƙafart kamar itama so suke su haukatata gaba ɗaya ”.
Cikin sauƙe numfashi Hajja Nana ta gyara zama tare da cewa.
“Dama haka duniya take”.
Still idanunta na zubda hawaye ta kalli Moddibo tare da faɗin.
“Ni dai ina so a samar mata magani ayi mata addu'a ane ma mata sauƙi awajen Allah”.

Acan Side ɗin Hajiya Bunayya kuwa Momy na shiga ta sameta atsaye sai bubbuga ƙafa take saboda yanda tsutsotsin ke cinta yayin da Amina ke gefenta tana zazzaro harshenta waje.
Da sauri Momy ta ƙarasa wajenta ta riƙe hannunta kana tace.
“Yaya ki zauna mana”.
Kai ta girgiza cikin tarin damuwa tace.
“Ina Momyn Khausar bazan iya zamaba idan na zauna ji nake har cikin hanjina tsutsotsin suke ci suna gigitani na rasa yanda zanyi na cutar dake arayuwa gashi nima yanzu na samu abinda yake cutar dani na rasa yanda zanyi a rayuwata”.
Cike da tarin tausayinta Momy ta girgiza kai tare da faɗin.
“Bakomai in sha Allah zaki samu lafiya”.
Kai ta girgiza tana cigaba da buga ƙafarta kana tace.
“A'a nikam nasan na nemowa kaina abinda yafi ƙarfina Momyn Khausar ki yafe min ki cewa Khausar ta yafe min”.
Cikin sauri momy ta juya tare da faɗin.
“Ki kwantar da hankalinki Yaya bari naje na kira Lamiɗo yazo ya kai ki asibiti ”.
Ta ida maganar tare da nufar Side ɗin Lamiɗo.

Cikin kiɗima tace.
“Wallahi Lamiɗo Yaya ce babu lafiya gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye ta kiɗime ta gigice ga Amina ma ita ma baki ɗaya yau jikinta nata abin ya sake motsa wa”.
Anutse Lamiɗo ya juya ya kalleta kana yace.
“Hmmm shine baki ɗaya kika gigice haka?, Mutanen dake suka cutar Sakayyah ce ta sauƙa akan su shine zaki gigice haka?”.
Kai ta girgiza kana tace.
“Nikam basu cutar dani ba kuma koda sun cutar dani na yafe musu Duniya da lahira”.
Gyaran murya Man Liman yayi tare da cewa.
“Wayene ba lafiya?”.
Zama Momy tayi muryanta ɗauke da damuwa tace.
“Uwar gidata ce babu lafiya Baffa Liman jinyan kuma ya kiɗima mu”.
Kai ya jinjina yace.
“Toh kunje asibiti ne?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Munje asibiti. Likitocin da kansu sunce bana asibitinba ne na gidane sai kaga yarinyar mijin da aka Aura mata ne bisa duk kan alamu tsafi yayi da ita ita kuma Yayan dai baza ka tantance ba”.
Zama Lamiɗo ya gyara kana yace.
“Ki daina cewa ba za'a tantance ba ki fito kice sihiri tayi Miki keda Khausar ya dawo kanta haka zaki faɗa masa ki fito fili ki faɗa masa abinda ta miki Saboda ko baki faɗa ba Allah ya sani kuma taga Sakayyar abinda ta aikata”.
Kai Momy ke girgiza masa shikam cikin tsanar Muguwar ɗabi'ar Hajiya Bunayya ya cigaba da cewa.
“Ita kuma Amina dama ai ƙulle ƙulle sukayi Ni kaina tsoron Al'amarin Naseer nake yi suka nuna dole-dole sai Naseer ya auri Amina yaje yayi tsafi da ita ya dawo da ita me zance musu su suka jawa kansu jiki magayi.
Ai dama sai dana ce duk abinda ya faru babu Ni aciki ba hannuna bare ƙafata aciki”.
Cike da nutsuwa Man Liman ya kalli lamiɗo tare da faɗin.
“A'a Lamiɗo baza ayi haka ba ai ita rayuwa rai da lafiya ita ake bibiya ake duban Lamarinsu kuma komai lalacewan Amina jinin kace tsatsonka ce kana Hajiya Bunayya komai lalacewan ta Matarka ce Uwar ƴaƴan kace”.
Da sauri ya girgiza kai yace.
“Uwar ƴaƴana ne babu yanda na iya amma Ni na saketa na saki Hajiya Bunayya tun wata ɗaya daya wuce Ni yanzu babu alaƙa tsakanina da ita na barta dai ta sauna a gida nane albarkacin Asiya da Sulaiman, taje can rayuwarta da ban rayuwata da ban”.
Mommy kam kallonsa take cike da matsanancin mamaki jin cewa ya saki Hajiya Bunayya ko kaɗan batayi farin cikin jin haka ba sai ma damuwarta ɗaya karu.
Chapter 128 · 0% Book details