← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 150

Sashe 100

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin jin kewarsu tace.
“Toh Babana yan zu dai ga amanar ƴata na bar maka amanar Khausi”.
Shiru yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa haka nan yake ji amanar tayi masa nauyi.
Sai kuma ya ɗago kansa ya kalli Hajja Nana da duk tayi sanyi tana matsar ƙwalla tace.
“To ga dai yarinya Khausar nan mun kawo maka amanar kuma bata da kowa anan sai kai sai kuma Iyayenka wanda su na gamsu da Mutuntakansu, Kararsu, da kuma dattakon su”.
Sai kuma ta share hawayen daya zubo mata ta cigaba da faɗin.
“Nasan su zasu riƙe min Khausar babu haufi kaine dai ban sani ba kana nan kullum fuska babu murmushi bare fara'a gakanan ga ka nanne ne dai, dan haka ni dai ajihar min da jikata, banda cin zali”.
Kallon ta yayi sai kuma ya sake sunkuyar da kansa bai san wacce kalma zai fada musu ba saboda girman abinda yake ji acikin zuciyarsa ya kuma lura wannan tsohuwar ya rigimace.

Dr Jameel kuwa kallon Didi yayi cikin yanayinsa na raha yace.
“Didi dan Allah ki ciwa Khausar ta daina kuka gashi tana samin Matata kuka bana so mu rabu tana kuka, gwara ita tana tare da mijinta Ni kuma zata sa matata ta tafi tana kuka Wazai rarrasa min ita?”.
Baki sake Hajja Nana ke kallonsa kafin ta hararesa da faɗin.
“Oooh Allah Ubangiji ya shirye ku kai kuma wa zai rarrasheta kake tuhuma?Gata da Uwarta kace Wazai rarrasheta?”.
Murmushi yayi tare da langwaɓar da kai yace.
“Wallahi Hajja Nana ko Ummi bazata rarrasa min Asma'u kamar yanda nake so in rarrasheta ba”.

Dai-dai lokacin Jakadiya tashigo tare da kallon su Ummi kana tace.
“Toh Bismillah ku fito Mazan baki ɗaya sun fito Sarki yace afaɗa muku ku fito jirginku ya kusa tashi”.
Ummi ce ta fara miƙewa kafin Hajja Nana ta miƙe.
Asanyaye Innayi ta miƙe ta rungume Hajja Nana tare da cewa.
“Allah sarki Ƙawata zanyi kewarki”.
Cikin sanyi Hajja Nana tace.
“Ayyah nima zanyi kewan ki ko yaushe zamu sake haɗuwa”.
Innayi na ɗan raba jikinsu tace.
“In sha Allah bazan daɗe ba zamu zo Auren Asma'u zanzo”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da cewa.
“Allah ya kaimu lokacin ya kawo ki lafiya”.
Sai kuma ta kamo hannun Khausar ta sanya cikin na Innayi tare da cewa.
“Toh ni dai ke nafi saninki akan kowa acikin Masarautar nan, dan haka ga amanar Khausar”.
Kai Innayi ta jinjina tare da faɗin.
“In sha Allah zaku same mu masu riƙe amana da kawaici da kara”.
Da sauri Khausar ta janya hannunta acikin na Innayi ganin Ummi ta nufi ƙofan fita yasa ta faɗa jikinta ta fashe da matsanancin kuka kukan daya sa jikin kowa yayi sanyi cikin rauni take cewa.
“Ummi Ni na fasa mu tafi tare bazan zauna ba, bani da kowa anan fa Ummi, nikam zan koma wajen Momy na kaifafa Haiydar mafa tafiya zaiyi”.
Cikin shesh-sheƙan ta cigaba da cewa.
“Ba Momy ba Haiydar ba Raudhat sannan ba Asma'u Ummi abarni ni kaɗai ni na fasa”.
Ummi kuwa cikin ƙoƙarin hana kanta kuka da take ji da sauri ta kauda kai dan raunin Khausar yayi yawa a hankali tace. “Khausar alƙawarin da kika yiwa Yayanki Jameel kenan? Kin fasa cika masa alkawarin kenan?”.
Cikin matsanancin kuka ta gyaɗa mata kai tare da cewa.
“Na fasa Ni na fasa bazan iya ba, Zanyi tayi mishi addu'a kuma Allah ya bashi haƙuri ni bazan zauna da Yah Moddibo ba zaita ta cin zalina”.
Ahankali Rahama ta matsa kusa da ita tare da faɗin.
“Ayyah Addah Khausar ki zauna mana muma muna sonki muna son zama kusa dake kuma zan zame miki madadin Asma'u Didi Madadin Mommy Yah Ibrahim Madadin Haiydar Innayi Madadin Hajja Nana”.
Cikin sauri ta juya ta rungume Haiydar tare da fashewa da matsanancin kuka Haiydar kuwa kasancewar sa Namiji yasa yashiga share mata hawayen ta yana cewa.
“Kiyi shiru Adda Khausy in Sha Allah muna tare dake duk inda kike”.
Ya faɗa hawaye na zubo masa.

Ajiyar zuciya Ibraahim ya sauƙe tare da riƙe hannun Haiydar yace.
“Haba Haiydar ya haka?.
Kana Namiji kana Kuka ita kuma ya zatayi?Mu tafi”.
Juyawa Haiydar yayi tare da nufar kofar cikin sauri Khausar ta yunƙura da niyyar bin bayansa tana cewa.
“Ni wallahi na fasa zan koma bazan zauna ba Yah Jameel yayi haƙuri bazan iya cika alkawarin saba ni ban san nan za'a kawoni ba shi yasa”.
Moddibo kuwa wani irin suya da ƙunci yake ji acikin zuciyarsa Kukane da yake saka masa ƙunci azuciyarsa babu wani abu da yaji baya sonji kamar kukanta.
Didi kanta jikinta yayi sanyi saboda yanda Khausar ke kuka.

A ɗan raunane Aunty Hajara ta kalleta kana tace.
“Khausar ya za'a yi kiyi haka tun safe kike ta kuka sannan har yanzu ba zaki bari ba zaki sawa kanki zazzaɓi muma haka kike so mu tafi kenan muna kuka?”.
Cikin rauni ta ƙarasa Maganar hawaye na cika mata Ido.
Faɗawa Jikinta Khausar tayi tare da faɗin.
“Yanzu Aunty Hajara sai ku tafi ku barni anan?”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“To ai ko wacce mace haka ta saba ,Aɗauketa daga inda ta sani daga wuraren data sani cikin Mutanen ta Yayunta, Ƙannenta Iyayenta”.
Kai Khausar ke girgiza wa tana cigaba da riskar kuka.
Aunty Hajara kuwa cikin sanyi da zubda hawaye ta cigaba da cewa.
“Sannan akaita cikin ƴan Uwan mijinta, Iyeyensa, Yayunsa, Ƙannensa su zauna lafiya da ita su zame mata dangi dan haka kema ki zauna lafiya dasu”.
Sabon kuka ta fashe dashi sai kuma ta kalli Hajja Nana Muryanta na rawa ta kifa kanta kan kafaɗar Hajja Nana tace.
“Yanzu Hajja Nana kema kin yarda zaku tafi ku barni”.
Hawaye na zuba a idonta tace.
“Toh ya zanyi Khausar ke kika ce kina son Moddibo fa ke kikace kina sonshi sannan yanzu an Aura miki shi an kawo ki ki riƙa kuka nima ki sani kuka ba gaki ga masoyinki ba”.
Ta ƙarashe maganar tana share hawaye tare da nufar hanya tana cewa.
“Allah ya ƙaddara saduwarmu Khausar”.
Da gudu Khausar ta zabura zata bita ganin haka yasa Moddibo saurin miƙewa wanda shi kansa baisan lokacin daya miƙe ba.
Hannunta ya kama ya riƙe tare da haɗe tafukan hannunsu wuri ɗaya.
juyawa tayi ta kallesa da fuskanta tayi jazir ga idanunta sun kumbura murya na rawa tace.
“Ka sake ni zan bisu bazan zauna ba”.
Wani irin rawa lips ɗin sa keyi so yake yayi magana amma ya kasa wani irin ƙuna zuciyarsa keyi kukanta na tayar mishi da hankali.
Hajja Nana na fita Ummi tayi saurin bin bayanta ta fita Asma'u ma cikin rauni ta miƙe ta fita haka Dija, Asiya, Aunty Ruƙayya, Hajiya Bunayya suka miƙe cikin tashin hankali ta fashe da sabon kuka idanunta akan hannunta daya riƙe tace.
“Nikam ka sake ni zan bisu”.
Sai kuma ta maida kallon kan Hajiya Bunayya dake ƙoƙarin fita tace.
“Addah Asiya, Dija duk tafiya zakuyi ku barni ba wanda za'a barni ni dashi sai ni kaɗai”.
Jin haka yasa duk sukayi saurin ficewa Didi ma miƙewa tayi tabi bayansu haka Dr Jameel da Rahama duk suka fice domin yi musu Rakiya.
Ganin duk sun fita yasa ya janyo hannunta suka bi ta cikin Corridor da zai sadasu da Side ɗin sa.

Tana mai ci gaba da kukan suka haura, suna haurawa kai tsaye Falon shi ya nufa da ita suna shiga ya maida ƙofar ya rufe Falon...
Ahankali ya ajiyeta bisa kujera, ita kuwa Khausar kuka ta kuma fashewa dashi, kukane wanda kasan daga ƙasan zuciyarta yake fitowa.
Cikin sanyi ya janyota jikinsa ya rungumeta hannunsa na dama ya buɗe ya haɗa da nata tare da tsarkake yatsun su, kana ya runtse hannu ya ɗago hannun nata ya manna kan sajensa yana shafawa.
Haka nan yake jin wani ciwom kukan ta yayin da hannunsa daya ke shafa bayanta alamun tayi shiru amma ina kukan ta sai ƙaruwa yake aƙalla sun ɗauki minti biyar ahaka amma Still kukanta ƙaruwa yake bai tsaya ba...

Adai dai lokacin kuma tawagar motocin su Hajja Nana ya fita daga cikin Masarautar ya nufi Saleh Ramat International Airport wanda zai kaisu Adamawa kasancewar Private Jet ne yasa suna tashi daga Morocco kai tsaye Adamawa zasu sauka.
ƙarfe goma dai-dai Jirginsu ya ɗaga daga Rabat Morocco zuwa Adamawa Nigeria...

Acan Side ɗin su Moddibo kuwa cikin sanyi yace.
“Kiyi haƙuri ki daina kukan nan”.
Cikin matsanancin kuka take janye hannunta daga cikin nasa tana mutsu-mutsu da jikinta alamun so take ta kwace kanta murya a disashe tace.
“Ni zan tafi”.
Ganin haka ne yasa ya kuma ajiyeta akan kujeran kana ya durƙusa gwiwoyinsa agabanta sai kuma ya riƙe hannayenta tare da buɗa tafin hannunta duka biyu ya daura akan sajensa wanda yake da yaƙinin tana so, idanunsa ya ɗago ya kalleta cikin wata raunatacciyar murya mai cike da rauni da tausasawa yace.
“Kiyi haƙuri kukan yana samun ciwo da ƙuci azuciyata kiyi haƙuri kibar Kukan”.
Ina kukanta ta cigaba dayi tana cewa.
“Ni zan koma bazan zauna anan ba garin da bansan kowa ba!”.
Lumshe idanunsa yayi kana ya buɗesu akanta yace.
“Ba gani ba ai kin sanni Yah Mu'allim ɗinki nefa, ko dai yanzu kin daina son nawa ne”.
Cikin zubda hawaye tace.
“Ni ba mai sona a nan”.
Tafin hannunshi yasa yana sharce mata hawayen tare da cewa.
“Kiyi haƙuri bana so inajin kukan yana tada min hankali yana samin ciwo azuciyata kiyi haƙuri ki daina Kuka *Minha Vidaa* bana son ki daina”.
Sai kuma ya taune lip ɗin sa na ƙasa tare da faɗin.
“Idan har ina jin tsoron da takaicin kukan wani ɗan Adam to Kukan kine Yana min suya da ƙuna azuciyata dan Allah ki daina zubda hawaye ki ki kalleni nine fa Yah Modibbo ɗinki da kikacewa su Lamido shi kikeso, ko dai kin daina Sona ne *Minha Vidaa?*
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Ni dai zan koma gida aikaima ba sona kake ba In banda cin zalina babu abinda kake min tunda muke atsawon rayuwata zalina kake ci, kasa adakeni ka sani kaɗe ɗankwali ka zalunceni kuma yanzu ma in na zauna mugunta zakai tamin”.
Chapter 100 · 0% Book details