Sashe 39
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannu ya miƙawa Norse dake gefensa cikin wani salo ta ɗaura tafin hannunta akan nasa ta riƙe tana murzawa.
Ahankali ya juya ya kalleta kana cikin wani shu'umin murya yace.
“Ruwa zaki bani ba hannun ki ba”.
Yanayin da yayi magana kaɗai zai tabbatar maka da cewa shi ɗin shu'umin Namiji ne na ƙarshen zamani mai cike da shu'uman da sanin barikanci.
Kai ta gyaɗa kana ta fita kai tsaye Office ɗinsa ta nufa ta ɗauko masa goran ruwa ta dawo ta miƙa masa karɓa yayi kana yasa atafin hannunsa ya watsawa Moddibo ruwan da ƙarfi dogon numfashi Moddibo yaja kana cikin wata raunan'niyar murya yace.
“Ummi naga J ɗin mu Ummi J ɗinmu bai mutu ba Ummi ga Jameelun ki bai mutu ba”. Yayi mgnar da larabci kasancewar dashi ya sume a bakinsa.
Baki ɗaya ido Norses ɗin suka zuba masa musamman wacce Dr Jameel ya kira da Baby wani irin kallo take bin ilahirin jikinsa dashi musamman Lips ɗinsa da yake tattarewa yayi pinch dashi.
Dr Jameel kuwa ahankali ya ɗago Ido ya kalleta cikin wani narkakkiyar murya yace.
“Ya dai Baby wani irin kallo ne wannan kada fa ki cinye sa yana kwance agadon asibiti”.
Sai alokacin ta lura da kallon ƙurullan da take bin Moddibo dashi numfashi ta fesar kana ta narkar da murya tace.
“Masha Allah kaga madaran kyau babu algus ga haiba da kamala”.
Harara ya watsa mata cikin muryarsa dake ɗauke da kishi yace.
“Ya fini ne?”.
Kallonsa tayi kana ta kalli Moddibo tace.
“Hmmm in dai kyaune da ƙasaita ya fika sai dai kuma ai kaine nawa kuma jaruntarka na sani”.
Ɗaya Norse data kirasa ta watsa masa Harara kana ta taɓe baki.
Moddibo kuwa ba tare daya dawo hayyacinsa ba ya cigaba da cewa.
“Ummi ga Jameelun ki ki daina kuka Abba ga J ɗina na gane J ɗina”.
Maganar Moddibo da Dr Jameel yaji shi yasa ya janyo hankalin sa ahankali ya sunkuya da kansa daidai kunne Moddibo yace.
“Ikon Allah”.
Moddibo kuwa Jin sautin Muryan ma sak ta J ɗinsa akunnensa yasa sannu Ahankali ya fara buɗe idanunsa domin ba zai taɓa mantawa da muryarsa ba akan Dr Jameel da har zuwa lokacin ke durƙushe kansa ya buɗe idanunsa cikin wani irin sauri ya yunƙura ya zauna Atsakiyar gadon kana ya janyo Dr Jameel ya fashe da wani irin kuka yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa.
Lokaci ɗaya kuma jikin Norses dake ta faman rawan kai da zumiɗin ganin kyawunsa jikinsu yayi masifar sanyi ganin yanda Kamilin mutum kana Matashi mai jini ajiki ke kuka Dr Jameel ma Baki ɗaya jikinsa ya mutu ganin yanda mutum dake kiranshi da J ke kuka tamkar mace.
Cikin rauni da tarin damuwa kana da kuka da yaci ƙarfinsa ya cigaba da cewa.
“Alhamdulillah Allah Nagode maka Ubangiji ya cika min burina Allah na gode maka dama J kana raye?”.
Ya ida maganar tare da janye jikinsa daga na Dr Jameelu ya tallafe kuncinsa still hawaye na bin fuskarsa kana muryarsa na rawa yace.
“J”.
Cikin sauri ya sake Rungume Dr Jameel Araunane yace.
“Ummi! Ina kike? Yau ina Abbana? Ummi ina kuke ga J ɗina Ummi J ɗina bai rasu ba Ummi gawar wani aka nuna mana akace J ne Ummi J ɗina bai rasu ba Ummi”.
Dr Jameel kuwa cikin sauri da tsoro ya janye jikinsa daga na Moddibo kana ya nuna sa da yatsa muryarsa na rawa yace.
“Bawan Allah ni ban sanka ba nifa ba J ɗinka nan da kake faɗa bane”.
Miƙewa Moddibo yayi ido cikin ido ya kallesa kana yace.
“J nine kake cewa baka sani ba!?,A.J ɗin ka nefa”.
Ya ida maganar kana baki daya ilahirin jikinsa rawa yake yayinda maransa ke cigaba da damƙarsa cikin rauni ya kalli Dr Jameel daya zuba masa ido kana yace.
“A.J ɗinka nefa Amma kake cewa baka sani ba”.
Ajiyar zuciya Dr Jameel ya sauƙe tare da fesar da numfashi cikin gaskiya da gaskiya yace.
“Wallahi ban sanka bani ban taɓa ganin ka ba”.
Cikin tsanananin tashin hankali tsoro da kiɗima Moddibo yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n J kaji tsoron Allah ka daina rantsuwa nine kake cewa baka sani ba J Moddibo kane fa Jameelu Nine zaka ce baka saniba!?”.
Cikin yanayin rashin fahimta Dr Jameel ya Girgiza kansa kana yace.
“Wallahi ban sanka ba ni ban taɓa ganinka ba”.
Araunane Moddibo ya tsira masa idanu kana yace.
“Baka Sanni ba J kace baka taɓa kallona ba?”.
Ya ƙarasa maganar tare dasa hannu ya shafa jikinsa jin babu waya yasa yayi saurin kallon Dr Jameel yace.
“Ina wayata?”.
Araunane ya sake kallon yace.
“J naji baka sanni ba domin Ni Aminine daya cancanci ka wurgar ko? to amma J Ummi fa Ummi ma baka santa ba?”.
Kai Dr Jameel ya girgiza kana yace.
“Wacece Ummi kuma?”.
Zare ido Moddibo yayi Aƙiɗime yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n J Ummi mahaifiyar kace baka sani ba!?”.
Ahankali Dr Jameel ya sunkuyar da kansa ƙasa kana ya ɗago ya kalli Moddibo yace.
“Ni kuma Mahaifiyata?,Gaskiya dai inaga wannan kana da Lalurar ƙwaƙwalwa!”.
Cikin sauri Moddibo ya zauna abakin gadon ya dafe kansa da hannu bibbiyu muryarsa na rawa yace.
“J ni kake cewa ina da matsalar ƙwaƙwalwa yayi kyau J shin wani irin laifi muka yi maka aduniya da muka cancanci irin wannan hukuncin agareka me muka yi maka mai tsanani da zaka hukunta mu ta wannan hanyar”.
Kallonsa kawai Norse din keyi cike da tausayawa.
Cikin rauni ya cigaba da cewa.
“J Ni kake jifa da kalmar cewa ƙwaƙwalwa ta ba ɗaya bane, to koma ƙwaƙwalwa ta takasance tana da matsala J rashinka akusa damu ne da kalmar da aka faɗa mana cewa ka rasune ya jefamu cikin wannan halin”.
Kallon ikon Allah kawai Dr Jameel yake kana yana kallon yanda hawaye ke bin kuncin Moddibo.
Cikin sanyi da rauni Moddibo ya cigaba da cewa.
“J sannan koda na kasance mai taɓin hankali katari da gawarka da akayi da gawarka akace ka rasu shiya jawowa ƙwaƙwalwata matsala!”.
Ahankali Dr Jameel ya matsa kusa dashi Asanyaye yace.
“Bawan Allah ka nutsu ni bansan kaba ban san mekake nufi ba”.
Cikin fushi Moddibo yace.
“J ƙarya kake”.
Miƙewa Dr Jameel yayi tare da ɗage kafaɗa yace.
“Ok toh shikenan”.
Ya ƙarasa maganar tare da ficewa Norses suka mara masa baya.
Cikin sauri Moddibo ya mike ya fita kai tsaye wajen motarsa ya nufa ya ɗauki wayarsa ya dawo reception din ya kunna wayarsa dake ɗauke da hotonsa dana M Jameel ya nuna masa kana yace.
“Yanzu wannan ka mantani ai gaka gani”.
Kallon fuskar wayar Norses ɗin sukayi Wacce Dr Jameel ya Kira da Baby tayi saurin buɗe baki cike da Mamaki ta kalli Dr Jameel kana tace.
“Iyee Dr da gaske fa kaine”.
Harara ya watsa mata kana yace.
“Kuma dai baku da hankali”.
Ahankali Moddibo ya juya da fuskar wayarsa nan yaga takwas tara cikin sauri yace.
“Yah salam banyi maghariba banyi Isha'i ba”.
Sai alokacin Dr Jameel ya tuna da batun sallah kallon Moddibo yayi da duk kiɗima da ruɗu kana da gigita dake jikin mutumin amma ga mamakinsa sai ya juya ya nufi Masallacin dake cikin Hospital Kai tsaye Tap dake wajen Moddibo ya nufa ya ɗaura alwala har zai shiga Masallacin ya tsaya ya juya tare da kallon Dr Jameel da still Idanunsa ke kansa.
Kai ya jinjina muryarsa na rawa yace.
“Yayi kyau J nine kake cewa baka gane ba zan shiga Masallaci in faɗawa Ubangiji duk abinda ke damuna”.
Ya ida maganar tare da shiga Masallaci nunfashi Dr Jameel ya fesar kana shima yayi alwala ya nufi masallaci.
Yana shiga Masallaci yayi maghariba da Isha'i yana idarwa idanunsa suka sauƙa kan Moddibo daya tsira masa ido.
Cikin sanyin murya da rauni Moddibo yace.
“J Nine kake cewa baka gane ba”.
Kai Dr Jameel ya Girgiza cikin gaskiya da gaskiya yace.
“Wallahi bawan Allah Ni bansan kaba ban kuma gane kaba kadena cemin J Ni sunana Jameel”.
Cikin sauri Moddibo ya katsesa kana yace.
“Aina sani dama sunan ka Jameel ne”.
Dr Jameel kuwa jin wayarsa na ringing yasa ya Mike ya fita kai tsaye cikin Hospital ya nufa duba matar daya mata Theater Yana shiga Moddibo yabi bayansa bayan ya gama duba ta yafita ya kalli Moddibo kana yace.
“Yanzu ko inda zanyi aikin ma sai kabini har ciki?”.
Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.
“Eh dole sai na bika J”.
Cikin alamun gajiyawa Dr Jameel yace.
“Toh kabarni mana ina sarara”.
Kai Moddibo ya Girgiza cikin tsaresa da ido yace.
“Ai tsakanina da kai babu sararawa sai lokacin dana danƙa ka ahannun Ummi da Abba”.
Siririn tsaki Dr Jameel yaja kana ya juya yabar wajen kai tsaye Office ɗinsa ya nufa dai-dai lokacin Baby ta shiga.
Tana shiga ta tsaya daga bayansa bayan ya zauna akan kujera cike da salo ta sanya tafin hannunta tashafa sajensa zuwa kan Lips ɗinsa.
Cike da shu'uman ci ya lumshe Idanunsa cikin wata narkakkiyar murya mai tarwatsa lissafin mata yace.
“Ohhhh My Baby don't kill me. Cikon Office muke fa, mu tafi gida Please I need you”.
Shagwaɓe Murya tayi tare dayi masa fari da ido tace.
“But Dr Ina da Nightduty”.
Wani kallo ya bita dashi yana shinshina wuyarta kana yace.
“Toh yanzu yakike so inyi”.
Ido ta kashe masa tare da ɗage gira tace.
“Duk yanda kace haka za ayi?”.
Cike da tsanananin Mamaki Moddibo ke kallonsu Aruɗe yace.
“J wacece wannan kuma kasan abinda kake yi kuwa?”.
Cikin tsawa ya kalli Baby kana yace.
“Ke ki sake shi baki da hankali ne?”.
Juyawa Dr Jameel Yayi tare da kallon Moddibo Up anda down Cike da takaici yace.
“Ya dai bawan Allah Meyesa kake shige min rayuwa da ƙudundunai ne?,Ko kuma dan kaga bansa security sun jefa ka waje bane?Ina ruwanka da ita?”.
Araunane Moddibo ya kallesa kana yace.
“J baka da hankali ne J mekake yi haka? Shin wace rayuwa ka jefa kanka aciki J?”.
*Gembila*