Sashe 46
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin fesar da numfashi ya riƙa juya idanunsa lungu da saƙo na cikin falon, kafin ahankali idanunsa suka sauƙa akan wasu jerin hotuna masu yawa.
Ware idanunsa yayi ganin wani kyakykyawan Matashi mai masifar kama da shi tamkar an tsaga kara babu abinda ya raba sa dashi yana cikin shiga ta al'farmar dake nuni da rainon masarautar ce.
A hankali kuma ya dire idanunsa bisa hoton dake gefen.
Wannan mutumin daya gani a fada ne amatsayin Sarki sai kuma wata kyakykyawa mata mai matsakaicin shekaru.
Zazzafan Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da maida idanunsa dake lumshe kan wasu kyawawan mata su uku biyu daga ciki zasu girmeshi ɗaya daga cikin kuma da alamun itace ƴar auta sai kuma hoton wani Kekkyawan jariri da aka ɗaura saitin cinyar Sarki, sai dai bisa alamu haɗa hoton akayi.
Suna zagaye da iyayen nasu, sai kuma ya maida idanunsa kan hoton dake gaba...
Cikin sauri ya miƙe tsaye murya ɗauke da tsananin mamaki da kaɗuwa gami da al'ajabi ya motsa Pinch lips ɗinsa tare da faɗin.
“Innayi”.
Ganin hoton Innayinsa ɓaro-ɓaro tare dana wannan ahalin duk da kuwa cewa alokacin tana da ƙarancin shekaru bai hanashi ganeta ba, ko dan yasan hoton a wurinta ne, dan tabbas tana da hoton wanda kuma hannunta ke riƙe da jariri fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi wanda kuma ta sha faɗi mishi shine a hannunta a ranar da anka haifeshi akayi musu hoton.
Yatsunsa biyu na yasa ya murza idanunsa ganin ko mafarki yake.
Cikin bugawar zuciya yace.
“Wannan fa innayi ce ba gizo idanuna kemin ba”.
Cikin tsananin al'ajabi ya furta.
“Ya salam Abun Al'ajabi”.
Kafin ahankali ya ɗaga ƙafafunsa da yaji sunyi masa mugun nauyi ya nufi jikin hoton, yayin da ƙwaƙwalwarsa ke tariyo masa cewa tabbas Innayi nada wannan hoton awajenta.
Da sauri ya dafe kansa tuno kalmarta agaresa da take cewa Kaje sai nazo.
Hannunsa duka biyu ya Sanya tare da dafe kansa lokaci ɗaya abubuwa da yawa suka shiga dawo masa ƙwaƙwalwarsa kama daga abubuwan da yake yawan mafarkinsu, atsawon rayuwarsa wanda tunda ya shigo masarautar nan yake ganinsu ra'anul ayn.
da kuma irin kalaman da Innayi ke masa wasu lokuta kana da tsananin kamanninsa da yaron dake jikin hoton da kuma Sarki wanda Babu bancin dake tsakaninsu wanda zai iya nuna cewa ba mutum ba ɗaya bane, sai dai shekarun da Sarkin yake dashi wanda shi kuma nashi basu kai haka ba kana hatta ƴan matan dake zagaye da hoton suna tsakanin kama dashi.
Zazzafan Ajiyar zuciya ya sauƙe akaro na barkatai kana ya tsirawa farcen hannun mutanen dake jikin hoton idanu wanda baiyi fari tasss ba yayi kalan ruwan ƙasa-ƙasa wanda haka shima nashi yake.
Kansa ne ya shiga juyawa cikin tsananin tarin mmki a zuciya yashiga jada baya yana tafiya da baya da baya har ya isa jikin kujeran da aka ajiyesa da farko kana ya runtse idanunsa kansa ya dafe da hannunsa na dama ya fara tunani.
“Shin me yake faruwa dani? Me hakan yake nufi? Ina ne nan? Toh menene haɗina dasu? Meyesa suka kawoni nan suka rufe ni? Meye nufinsu? Shin ko dai mafarkaina gsky ne?.”
Tambayoyin da yake yiwa kansa kenan.
Cikin sauri ya janye hannunsa dake kansa ya shiga laluma aljihunsa da niyyar ciro wayarsa dan ya kira Innayi. sai yaji wayam iska ya furzar mai zafi tuno cewa ya barsu acikin amota...
Acan cikin gida kuwa wani hamshaƙin falone me masifar kyau da tsari wanda yaji komai na more rayuwa daga can tsakiyar falon kuwa wata kyakykyawar Matace wacce take cikin hoton da Moddibo ya gani Hakimce akan wata kujera ta alfarma.
Yayinda ƴaƴanta ke zagaye da ita a hoton, sunlma suna gefenta sai dai Ba Ibrahim kana babu Rahma, bisa alamu hira suke cike da shaƙuwa.
Cikin nutsuwa Dr Jameel suka kutsa kai cikin falon da sauri yaron da Dr Jameel ke riƙe da hannunsa ya janye kana ya nufi gaban matar tare da riƙo hannunta da cewa.
“Didi kin san wani abu kuwa".
Cikin kula da so irin na kakannin a kan jikokinsu ta girgiza mishi kai tare da cewa.
“Toh Sarkin fada, me ka gano kuma, dan na lura in kunzo dai kana son zaman fada”.
Da sauri ya zauna gefenta tare da cewa.
“Didi wlh yanzu na ga wani mai kama da Uncle Ibrahim sai kingani kamarsa ɗaya da Uncle Ibrahim.
Sai dai shi yafi Uncle Ibrahim tsawo da kyau amma Didi babu abinda ya raba su da ace Uncle Ibrahim zai ɓata toh wlh wannan za'a ɗauka ya maye gurbinsa”.
Cikin sauri da bugawar zuciya. Didi ta kalli Dr Jameel kana tace.
“Jameel waye shi?Akan wayake Hakim ke magana?”.
Ajiyar zuciya Dr Jameel ya sauƙe tare da zama akan Lallausan Darduman dake malale ƙasan tiles ɗin kana yace.
“Kai Didi gsky nima abin nan yaban mamaki.
Didi yau tsawon kwana huɗu kenan yake bibiyata bansan shiba amma tun ranan farko dana fara ganinsa yana min kama da wani sai dai na rasa da waye yake min kama ina ta tunani na rasa ganowa sabida gaba ɗaya lamarin shi ɗauremin kai yadda yake ta nuna ya sanni”.
Sai kuma ya ɗan fesar da numfashi tare da gyara zamansa kana ya cigaba da cewa.
“Na rasa dawa yake min kama baki ɗaya abin ya kwanta min akaina, sai yau da muka zo nan naga na kalli Fuskar Abualeey, sai na ga suna tsananin kama, sai kuma na tuni Ibraahim ashe dasu yake min kama kai kamanninsu da Ibraahim ya ƙazanta Didi shin wanene shi”.
Cikin wani irin yanayi na tsananin al'ajabi da tsuman zuciya. Didi ke sauraransa yayin da ƴaƴanta Lalla Khadijah, da kuma Lalla Hafsat mahaifiyar Hakim wacce take aure a Mexico wanda zuwan kakansu Sheiyk Jabeer Nuruddeen Gwadabe Joɗa, ne yasa su zuwa dan ganawa da kakansu.
Ido suka tsira Dr Jameel cikin son fahimtar wani abu.
kana hadiman Didi kuwa dake can gefe sunkuyar da kansu sukayi
Dr Jameel kuwa ahankali ya cigaba da faɗin.
“Sannan kuma ashe ban sani ba yana bibiyata, har muka shigo gidan nan”.
Nan ya kwashe komai tun daga haɗuwarsa da Moddibo har zuwa yau ya sanar mata...
Kana ya ɗaura da cewa.
“Sannan kuma Didi ɗazun da Abualeey ya kirani kan inzo in duba jikin Rahma ciwon cikinta ya tashi. Ashe ban sani ba yana biye dani sannan kuma shigowar da zamuyi *Rinƙas* ya ƙwace ya shigo cikin Masarauta Didi.
zakisha mamaki idan kika ga yanda yake sarrafa Dokin nan”.
Lokaci ɗaya Lalla Khadijah da Kalla Hafsat suka kalli juna, kana suka juyo cike da mmki suka kalli Didi.
Da bugun zuciyar ta ya sake nunkuwa fiye da kaso tamanin cikin ɗari.
Cikin fesar da numfashi ya cigaba da cewa.
“Kuma kinfi kowa sanin mutum biyu ne ke kaɗai ke iya, sarrafa Rinƙas, ko Ibraahim baya iya zuwa ko kusa dashi.
Amman shifa kai tsaye ya fuskanci dokin. Didi wlh al'amarin mutumin yayi masifar ɗaure min kai fiye da yanda kike zato”.
Didi kuwa tun daga lokacin da Hakim ya faɗa mata yaga mai kama da Ibraahim zuciyarta ke bugawa har zuwa yanzu da Dr Jameel ya dasa ayar mgnar, cikin sauri ta juya ta kalli Lalla Khadija da Hafsat, sai kuma Rahma data fito yanzu ta kwanta gefenta Lalla Hafsat tana damƙe cikinta.
cikin sauri Hafsat da idanunta ke waje ta kalle Didi kana tace.
“Didi”.
Murya cike da sanyi da bugawar zuciya Didi tace.
“Na'am”.
Sai kuma suka shiga kallon juna alamar maganar ta ratsasu.
Dr Jameel kuwa batare daya lura da yanayin da suke ciki ba ya cigaba da cewa.
“Allah Didi kamannin nasu har ya ƙazanta kamanninsa da Ibraahim is too hight har Abualeey da kansa abin ya jijjigasa kin kuwa ga Fada? yana shiga fa sai da kowa ya tashi tsaye”.
Didi kam kallonsa kawai take bako ƙyaftawa shi kuwa Dr Jameel cigaba da cewa.
“Kinga Jabeer bin Jabeer shima sosai yayi mamaki saboda naji yana cewa wai sun haɗu dashi ajirgi, dan sai cewa Abeey yake, Abeey ka ganshi ko babu abinda ya raba shi da Ibraahim kamannin yayi yawa, nacema zan faɗawa Didi kace kar in faɗa mata hankalinta zai tashi, gashi yanzu yazo har inda take Abeey wlh jininmu ne. Haka yake ta faɗa yana can yana ruɗe”.
Cikin sauri da yanayin zabura Didi ta miƙe tare da kallon Jakadiyarta da kanta ke ƙasa kana tace.
“Jakadiya maza je ki duba idan Mai Martaba na nan. Kice Ina son ganinsa cikin gaggawa. In kuwa yanada uzuri a fada, ina fatan ayi min iso”.
Cike da girmamawa Jakadiya ta gyaɗa mata kai kana ta furta.
“Toh”.
Sai kuma ta juya cikin sauri ta juya ta fita Ahankali ta riƙa ratsa tamfatsa-tamfatsan falon har ta isa bakin ƙofar fadan wayam ba kowa alamar duk an watse.
Cikin Sassarfa ta juya ta koma falon domin sanar mata...