← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 150

Sashe 131

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kanta ta langwaɓar tare da cewa.
“Ayyah Yah Mu'allim ba gardama da taurin kai bane kaga idan mun koma kafin na sake ganin Momy fa zai daɗe ”.
Yana gyara zamansa gefenta yace.
“Amma Ni bakya jin tausayina tunda muka zo fa kike bari na ina rayuwa Ni kadai kamar Maraya Babu kowa kusa dani”.
Kallonsa tayi tace.
“Yah Mu'allim aima mun kusa komawa dai kayi haƙuri kwana nawa ya rage”.
Ta ƙare maganar tana cigaba da dudduba littattafan sai kuma ta ajiyesu ta gefensa kallon yanda ta hargitsa Littattafan yayi kana yace.
“Me kike nema?”.
Tana cigaba da abinda take tace.
“Wani littafi na nake nema?”.
Da mamaki yace.
“Littafi kuma?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh”.
Kamar mai raɗa ya sake matsawa kusa da ita yace.
“Toh me zakiyi dashi?”.
Kanta na kan tulin littattafan tace.
“Wani abu ne aciki?".
Da mamaki yace.
“Wani abu ne kuma aciki?,ki bari gobe sai ki duba”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“Ina so ne in tabbatar yana nan ko baya nan saboda da nazo na samu Raudat tana wasa takarduna da jakar makarantana ta bubbuɗe min ban sani ba ko ta jefar min da littafin ”.
Cikin mamakin yanda take neman littafin yace
“Toh littafin na wani Subjects ne?”.
Tana ɗan tura baki tace.
“Um-um fa littafin bana karatu bane?”.
Yana ɗan ƙara matsota yace.
“Ikon Allah toh littafin na menene?”.
Ya ƙare maganar yana dudduba littattafan data tutturo gefensa yayin da take sake zaro na cikin jakar ganin basu cikine yasa ta jawo durowan ƙasan Weldrop ɗin tare da cewa.
”Toh ban sani ba bari in duba ko suna cikin nan ne”.
Dai-dai lokacin yaga wani note Book An rubuta *SPECIAL MAN* da manyan baƙi Aransa ya maimaita Special Man ahankali ya jawo littafin yana ɗan jujjuyawa Khausar kuwa baki ɗaya hankalin ta na cikin durowan Weldrop ɗin.
Ahankali ya buɗe shafin farko na littafin.
ga mamakinsa sai yaga Drawing ɗin hoton fuskarsa ne rauɗau ba abinda aka bari har sajensa.
Cikin tarin wani irin mamaki al,ajabi da kuma kaɗuwa ya kalli gefen shafin.
A gefen kuwa Drawing ɗin fuskarsa ne acikin aji hannunsa na kan Black board kamar yana rubutu cikin sauri ya kalli rubutun da akayi da kalo wanda akayi musu design yanda ya kasance na musamman haka sunansa ya kasance na Musamman _Aliyu Youseef Mohammed Mouley (Moddibo)_
da mamaki ya kalli inda aka rubuta sunansa anyi zanen ❤️ sai kuma ya maida idanunsa inda akayi Drawing ɗin fuskarsa yaga date and time ɗin da akayi rubutun Drawings ɗin.
Idanunsa ya jujjuya ya kalleta amma baki ɗaya hankalinta na kan tarin himilin sauran littafan.
Kallonsa ya mayar kan date ɗin idan har baiyi kuskure ba toh shekaru huɗu kenan ranan dasu Khausar suka fara zuwa SS3 cikin mamaki da wani irin yanayi ya buɗe page ɗin gaba sai yaga Drawing ɗin Fuskarsa ne amma ba'a fitar da fuskan sosai ba sai sajensa aƙasan ta rubuta.
_One's if I remember your face, my actionable will be change to cool, is your Breed brightly my heart always yo be sunshine , i really love you with deep voice. Uncle Aliyu Youssef Mouldy (Modibbo)_
Ahankali ya motsa laɓɓansa ya furta.
“Ya salam”.
Wani irin amintaccen numfashi ya fesar saboda jin kalaman suna Barka duk kan lakar jikinsa.
Fahimtar da yayi baki ɗaya littafin kamar akansa yake magana haka nan yaji wani abu yana sauƙa tun daga ƙwaƙwalwar kansa har zuwa babban yatsarsa a iya shafi biyu daya buɗe ya fuskanci gaba ɗaya Khausar ta rayune da soyayyar shi acikin zuciyarta shi kansa baisan meyesa ba ya dai tsinci kansa da naɗe takardan yasa cikin aljihunsa.
tare juyawa yayi mata wani amintaccen rugguma yana mai kallonta yace.
“Wai wani littafi kike nema ne?”
Batare data kallesa ba tace.
“Wani Littafina ne na musamman, nasan da wuya in Raudat bata ɓatar min da shiba dan haka taɓatar min da ɗan uwanshi da Nai ta rubutawa tun daga JSS one to 3”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Ko dai Diary kine?”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Kusan haka amma shi babban littafine ai yama fi Diary daraja awajena”.
Gira daya ya dage tare da faɗin.
“Toh tashi mu tafi da safe sai muzo na tayaki dubawa”.
Kai ta langwaɓar kana tace.
“Allah ina so ba mamaki yanzu Raudat ta ɓatar min dashi. In dai ta baddashi wlh sai na daketa dan yana tunamin abubuwa da yawa a rayuwata”.
Kai ya girgiza tare da faɗin.
“In sha Allah ma bai ɓata ba kada ki damu kizo mu tafi da safe za'a zo mu duba”.
Ya ƙare maganar da ƙaguwar so yake ya ga su ƙeɓe daga shi sai ita.
Kai ta girgiza tana cigaba da hautsina littattafan tace.
“Um-um.ni dai ina son gani ”.
Fuska ya tsuke tare da cewa.
“Mu tafi nace ko?”.
Ganin yanda ya tsuke fuska yasa ta gyaɗa kai tare da faɗin.
“Toh”.
Kana tattare littafan ta mayar cikin drawer.
Hannunta ya jawo ya riƙe kana ya kalli gyalen jikinta ganin babu laifi yasa yace.
“Mu tafi toh”.
Suna fita motarsu Dr Jameel na fita agidan motarsu suka shiga kana suka tafi gida.
Chapter 131 · 0% Book details