← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 150

Sashe 4

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asma'u dake gefen Ummi zaune Idanunta cike da hawaye tana ganin Khausar ta fashe da sabon kuka kana ta miƙa mata hannu cikin sauri Khausar ta kamo hannunta tare da zama gefenta ta.
Rungume juna sukay tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Mommy da Hajiya Bunayya kuwa kusa da Ummi suka zauna.
Mommy na Kallon Ummi taji wasu sabbin hawaye sun zubo mata cike da tausayawa Mommy tace.
“Ummi Sannu”.
Sunkuyar da kai Ummi tayi cike da dauriya tace.
“Toh ya zamuyi Aysha ya zamuyi da hukuncin Ubangiji.
Jameelu ya riga mu gidan gaskiya ya tafi ya barni da gurbin da bansan ya zai cikeminba”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da cewa.
“Kiyi haƙuri Ummi”.
Kasa ƙara sawa tayi sabida kuka yaci ƙarfin ta kawai saita kife kanta gefen Ummi ta shiga rera kuka.
Ajiyar zuciyar Ummi ta sauƙe cikin sanyin murya me ɗauke da ƙuna tace.
“Kiyi haƙuri Aysha haka Ubangiji ya tsara bamu isa muja da lamarinsa ba addu'ar mu suke buƙata muyi musu addu'a Allah ya gafarta musu”.
Cikin sheshsheƙa Mommy tace.
“Ameen”.
Ahankali Mommy ta juya suka gaisa da Hajiya Turai da Hajiya Karima sannan da ƙannen Abban Jameel Hajiya Maryam da Hajiya Fa'iza suka yi musu ta'aziyya.

Khausar dake Rungume da Asma'u cikin Muryan kuka tace.
“Asma'u yanzu da gaske Yah Jameel ya rasu shikenan ya tafi ya barmu!”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.
“Da gaske Khausar Yah Jameel ya rasu shikenan gatanmu ya rasu rufin asirin mu ya tafi garkuwan mu ya barmu Inuwarmu wajen fakewar mu ya gushe, bangon da muke jingina muji daɗi ya fadi ƙasa”.
Kasa ƙara sawa tayi kawai ta fashe da kuka me tsuma zuciya.
Cikin sauri Ummi ta girgiza mata kai Araunane tace.
“Kul Asma'u!,Kada ki faɗi haka kada kiyi butulci ga Ubangiji domin shi ya bamu Jameelu kuma shi ya ɗauke mana shi kuma zai jibanci laluranmu muddin mukayi tawakkali”.
Innayi dake gefe ta matso kusa da Asma'u da Khausar ta janyosu jikinta tare da ɗaura kansu akan cinyarta cikin Muryan rarrashi tace.
“Kuyi haƙuri kuyi masa addu'a”.
Ahankali Khausar ta ɗago tare da kallon Innayi kana tace.
“Innayi yanzu shikenan Yah Jameel ya tafi ya barmu har abada baza ku sake ganinsa ba!? Bazai sakeyi mana nasihaba, bazai sake neman al'farma a wajenaba ashe Yah Jameel Wasiyya yayi ta barmin a wancar ranar”.
Shafa kanta Innayi tayi kana tace.
“Khausar kada kiyi kuka muyi masa addu'a shine abinda yake buƙata awajenmu kana mu cika masa dukkan wasiyar daya bar mana”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana ta cigaba da kuka mai ciwo har Idanunta suka kumbura.
Sai Bayan sun idar da Sallar Maghariba kafin Lamiɗo ya ɗebe su suka tafi
A wannan daren ranar baki ɗaya haka suka kwana cikin ƙunci zuciya da alhini Moddibo kuwa baya um bare Um-um ko awajen zaman makoki idan akace masa sannu baya magana saidai kallo sai ance Allah ya jikansa kafin yace.
“Ameen ya Allah Nagode”. Iya abinda yake iya faɗi kenan.

Haka rayuwa tayi musu ƙunci da ɗaci haka aka ɗauki tsawon kwanaki bakwai ana zaman makoki har awannan kwanaki kullum cikin gida da waje a cike yake da masu zuwa ta'aziyya.
Washe garin rana ta takwas da safe Moddibo na fita bai nufi ko ina ba sai gidan Ummi bakinsa ɗauke da Sallama yashiga falon zaune ya sameta hannunta riƙe da carbi ta zubawa waje ɗaya ido.
Jin Sallamar sane yasa ta ɗago kanta tare da tsira masa Ido agefenta ya zauna.
Cikin sanyi tace.
“Babana”.
Ahankali yace.
“Na'am Ummi”.
Cike da tausayawa Ummi tace.
“Babana kalli yanda ka sake dawowa fa yaushe zaka sawa ranka dangana ne? Kadafa muyi abinda Allah bayaso”.
Batare da yace Uffan ba yayi ƙasa da kansa yana jin wani irin zafi azuciyarsa.
Jin muryarsa yasa Asma'u dake Bedroom ta fito tare da zama agefensa kana ta gaishesa.

Ahankali Moddibo ya juya ya kalli Ummi kana yace.
“Ummi yanzu a Duniya babu abinda nake buri daya wuce ingano su waye suka sace J sannan suka yi masa kisan gillah ina so insani. Ummi inaso inyi bincike akai ina so inga lallai a hukunta su kwatankwacin zalinci da suka mana”.
Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe tare da cewa.
“Aikuwa Yah Moddibo Khausar tana da dan abinda ta sani.
Domin ranan da muka rabu da Yah Jameel na karshe aranan ne ya maida Khausar gida kuma tace mana.
Taga wata mota na binsu.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tace.
“Amma Babana Meye amfanin bincike bayan sun kashesa!?”.
Cikin sauri yace.
“To ai Ummi nan nema yake da amfani tunda suka kashesa dama mun biye musu ne saboda munji tsoron kada su kashesa shiyasa mukabi tsarinsu!”.
Girgiza kai Ummi tayi kana tace.
“Toh amma dai ni inaganin barin shi yafi A'ala kada kai ɗinma da ka rage mana su cutar mana da kai”.
Sam Ummi ta rigada ta saki komai na duniya shiyasa duk yadda yaso ayi mgnar a sake buɗe file din binciken taki.
Fahimtarsa bazata yardabane yasa ya nuna mata ya hakura.
Kallon Asma'u yayi tare da miƙewa kana yace.
“Asma'u zamuyi magana”.
Kai ta gyaɗa sannan ya fice.

Yau ya kama sati biyu da rasuwar Ramadan wanda yayi daidai da kwanaki sha biyu da jana'izar M Jameel.
Acan gidan Lamiɗo kuwa da misalin karfe sha biyu na rana Hajiya Ruƙayya da Mommy da kuma Khausar na zaune afalo suna hira kamar daga sama suka jiyo Sallamar Hajja Nana da faɗin.
“Assalamu Alaikum”...!

*Kada kyiwa labarin bahagon fahimta. Wasu abubuwa na cikin Labarin gaba ɗaya gaskiyane ya faru da gaske. Ina mai roƙonku da Allah kuyiwa Jameel Addu'o'i Allah ya jiƙamsa da rahama ya kuma toni asirin waɗanda sunka saceshi suka kasheshi kisa mai muni. Ku sashi a addu'o'i ku, domin Wallahi tallahi rasuwar Jameel gsky ne kuma ya faru, da gaske wanda nasan mafi akasarin mazauna Adamawa zasu san labarin rasuwar Jamilu matashi mai Kekkyawan ɗabi'un sun kashewa sun bar mahaifiyarsa da ƙunshin a zuciya, sun sa mahaifinshi a rauni mai ciwo. Yah Allah ka jiƙan Jamilu kayi masa rahama da gafara, ka tausashi zuciyar iyayensa ka ƙara zamewa mahaifiyarsa Gatan*

🤝🏻KADA KUMA KU DAMU ZAKUSHA MAMAKIN YADDA LABARIN ZAI SAKU FARINCI DA SHAUƘI ZAKUSHA MMKIN YADDA LAMARIN ZAI BADA CITTA, KU DAI KU BIYONI KUSHA LABARI, WACCE BATA BIYA TA BIYA.

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 2*

Spbnɗettett. Cikin ɗan sakin fuska Mommy ta miƙe tare da cewa.
“Wa'alaikum Salam Hajja Nana sannunku da zuwa”.
Hajja Nana na zama aɗaya daga cikin kujerun falon tace.
“Yawwa Aysha sannunki”.
Cike da farin ciki Khausar ta miƙe tare da riƙe hannun Dije kana ta jata suka zauna akan 2sitter.
Murmushi Mommy tayi tare da juyawa ta shiga kichen.
Ta kawo mu abin taɓa,
Fuska ɗauke da murmushi Khausar dake riƙe da hannun Dije ta juya tare da kallon Hajja data zuba mata Ido, cikin sanyi tace.
“Maraba Hajja Nana ya gida ya Baffa Liman, Baffa Jauro,Baffa Sadu, Baffa, Garga Yaya Sadik? Duk kowa da kowa dai”.
Harara Hajja Nana ta watsa mata kana tace.
“Sai yanzu kika ganni wacce ta dameki ai gashi tun shigowarta kika jata jiki, kuke gaisawa idan kin matsu da sanin yanda suke sai kije ki duba su da kanki”.
Uhum kawai Khausar ce tare da loggobar da kai dan har yau bata dawo dai-dai ba cikin sanyi tace.
“Kai wannan tsohuwa ke dai akwai ki da kishi, da mita ina ce dai yanzu gashi na gaishe ki amaimakon ki amsa shine sai kin cakaleni”.
Riƙe haɓa Hajja Nana tayi tare da maka mata Harara kana tace.
“Yo ki riƙe abinki mana ko wata tsiyar gaisuwar ki zai min?”.
Ta ida maganar tare da sauƙa ta ɗauki Cup ɗin tea da Mommy ta zuba mata kana ta kurɓa”.
Taɓe baki Khausar tayi tare da cewa.
“Oho dai ai ko bazai miki amfani ba kin nema bare ma amfanin zai miki”.

Mommy da fitowarta daga kichen kenan tayiwa Khausar alamar tayi shiru kana ta zauna gefen Hajja Nana cike da girmamawa ta gaisheta tare da tambayar mutane gida.

Miƙewa Khausar tayi tare da riƙe hannun Dije tace.
“Zo mushiga ciki”.
Saurin Kallonta Hajja Nana tayi tare da faɗin.
“Dawo ki zauna”.
Tsayawa tayi tare da kallon Hajja Nana still hannunta na riƙe da Dije tace.
“Toh me kuma zan miki?”.
Sassauta murya Hajja Nana tayi tare da faɗin.
“Ke kam ki dawo ki zauna mana”.

Sake hannun Dije tayi tare da tsare Hajja Nana da ido kana tace.
“To wai mai zan miki zamuje muyi hiranmu irin na ƴan Uwanta kema kuyi hiranku mana ko sai dole na zauna ne?”.
Harara Hajja Nana ta maka mata tare da cewa.
“Wato ke dai daga zuwana sai kinsa mun raba hali, ko ba a isa ace yi kiyiba sai kinyi musu?”.

Kallon Khausar Mommy tayi tare da cewa.
“Ke dai ki dawo ki zauna mana koma menene ai zaki ji”.
Kai ta gyaɗa tare da janyo hannu Dije suka zauna gefen Mommy ya zamana Khausar na fuskantar Hajja Nana.
Hajja Nana kuwa zamanta ta gyara tare da fuskantar Mommy Cike da isa, gadara, taƙama, Iko, kana da Power da take jin tana dashi akan Khausar da kuma rigima irin ta tsofaffi tace.
“Alhamdilillah mun godewa Allah daya nuna mana lokacin da Khausar ta gama karatu lafiya”.
Cikin sauri Khausar ta kalleta tare da cewa.
“An gama karatu lafiya ko kuma anfara taka matsayin karatu? Ko tsakiyar karatu ma naje ne bare akai ga maganar gamawa?”.
Wani kallo Hajja Nana ta watsa mata tare da cewa.
“Karatun ƙa'ida kam nasan angama shi tunda kinyi haddar Alkur'ani kin sauƙe sannan kinsan, Ahallari, Kinsan ishmawi, Kinsan Fiqhu, Kinsan Arbauna, Kinsan Sira da sauransu yanzu wani karatu ya rage miki”.

kallonta kawai take sai data gama jerawa kafin tace.
“Karatu kam wanda ya ragene yafi yawa aisharan fage kawai nayi acikin karatu”.
Harara Hajja Nana ta watsa mata cikin yanayin zafinta tace.
“A'a sannu Al-huda-huda sarkin karatu dole kika ce sharen fagi kikayi mana, tunda kin samu anbarki kinyi wannan ɗin”.
Sake baki Khausar tayi tare tura baki kana tace.
“Ikon Allah dana samu anbarni nayi da mekike nufi kenan, ko kuma dama kece zaki tsara min abinda zanyi?”.
Chapter 4 · 0% Book details