Sashe 70
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai Hajja Nana ta gyaɗa cikin yanayinta na ƙasaita da zafi tace.
“Toh badole in zauna ba tunda kece kika ce kina son shi, bashi bane yace yana sonki, ai dole in zauna In jira inga wani irin tarba zai miki, inga kamun ludayinsa,dan wlh Allah kenan In naga ya Miki abinda bai min ba duk da ke kikace kinji kin gani kina so wallahi ɗaukarki zanyi mu tafi tare”.
Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tana kallonta cike da jin daɗi dan harga Allah ta fara tsoron a tafi a barta ba kowa nata tare da mutumin da in baici zalinta ba baya jin daɗi ta kuma san baya sonta.
Hajja Nana kuwa cike da izzah da ƙasaita ta cigaba da cewa.
“Na faɗawa Baffanki ma tun jiya ya fara cewa inyi haƙuri kuma Wallahi babu abinda zai tafiyar dani, zama daram anan sai naga yanayin kamun ludayinsa mutumin da an bani labarin tun a makarantar ma ba shiri kuke ba kinga ko nida tafiya sai naga abinda ya turewa buzu naɗi”.
Kai Khausar ta girgiza tare da sunkuyarwa ƙasa ita kanta ta san.
Moddibo baya ko ƙaunae ganinta kuma tafi kowa sanin tsanar daya mata baya son alaƙa da ita koda kallonta ne baya son yi”.
Hannu Hajja Nana ta sanya ta ɗago haɓarta kana ta tura mata Bowl ɗin dake ɗauke da Fruits ɗin gabanta da Mukara dake ɗauke da Juice kana tace.
“Gashi kici wannan koda baki ci Abinci ba shi zai ɗan taimaka miki, kinga gaba ɗaya ki rame”
Akuma dai-dai lokacin suka ɗaga kansu suka kalli ƙofan Falon jin Antura ƙofar an shigo...
Da sauri Khausar ta sunkuyar da kanta ƙasa ganin Moddibo Hajja Nana kuwa sallamarsa ta amsa tare da zuba masa ido.
Cikin ranta tace.
“Uhmmm ai ba banza Khausar tace taji ta gani wannan kyau haka ai masha Allah, Ɗan ko maƙiyinsa yasan shi mai kyau ne”.
Shi kuwa Modibbo a tsakiyar Falon ya tsaya kana ya kalli Hajja Nana dake cikin shiga ta alfarma duk da tsufanta bai hanata kyawunta fita ba cikin ɗan sakin fuska kaɗan yace.
“Ku kaɗai ne”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa masa tare da cewa.
“Eh”.
Cikin sauƙe numfashi yace.
“Ina Innayi?”
Tana tauna Inabi ta amsa da.
“Sun sauƙa ƙasa wajen Didi”.
Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke tare da faɗin.
“Uhmmy”.
Sai kuma ya nufi dining area ɗin.
Sassayyan numfashi Khausar ta shaƙa jin yadda ƙamshin jikinsa ya karaɗe wurin.
Shi kuwa cikin wani irin narkekken yanayi yasa hannunshi ya ɗan ja kujeran dake Facing ɗin Khausar.
A hankali ya zauna yayin da ƙamshin Kwallacar sirri da Khausar tayi amfani dashi ya cika masa hanci da ƙara sake mishi wata fitinenniyar kasala.
Kallon Hajja Nana dake shan Fruit yayi kana yace.
“Ya kike?”.
Cikin tsareshi da tace.
“Lau nake”. Da gefen idonshi ya kalleta jin yadda ta amsa kamar a faɗace, bakinshi ya ɗan taɓe tare da ɗan ƙara kwantar da kanshi jikin kujerar,
Tare da zaro wayarsa ya shiga latsawa a zahiri wayarsa yake kallon, amman a baɗinin kuwa ƙafafun Khausar dake ƙasan Table ɗin yake kallon yadda ta ɗan ɗaura ɗaya bayan ɗaya, wanda hakan ya bawa sharaɓanta dama bayyana a fili.
Khausar kuwa batare da ta ɗago ta kallesa ba ta cigaba da juya Tuffan dake hannunta batare da taci ba.
Ɗan leƙa ƙasan dining table din ya kumayi a hankali ya lunshe ido ganin tana ɗan kaɗa ƙafafunta yasashi ɗan tura nasa ƙafar dama ƙasa kusa da nata, a hankali ya zare takalminsa.
Sai kuma ya ɗan juya idonshi ya kalleta, still dai wasa take sa Apple ɗin
A hankali ya ɗago ƙafarsa, tare ɗan mannashi kan sharabart kana a hankali ya jawoshi yayi ƙasa dashi har zuwa kan rumfar sawun nata ya shafa da sassayan tafin ƙafarshi mai taushi.
Da sauri ta ɗago ta kalleshi tare da sakin ajiyan zuciya dan sanyin tafin sawunshin daya ratsa mata jiki da zuciya.
Hajja Nana kuwa, baki ta ɗan sake tana kallon yadda Modibbo ya tsare Khausar ɗin da ido, sai kuma ta juya ta kalli Khausar ɗin da ta ɗan lunshe idanunta ganin shima ɗin ita yake kallo.
Jin yadda ya wani irin murza tafin kafarshi kan natane yasa ta sake buɗe idanunta tare da kallonshi tana maijin wasu baƙin abubuwan na fitowa daga cikin idanunsa suna ratsa nata idanun,
Dan shima ɗin ita ya zuwa idanunshi tamkar zai mannesu cikin nata.
Ahankali ya motsa lips ɗin sa wanda ko Hajja Nana dake gefensu bataji, abinda ya faɗa daga shi sai ita yace.
“Baki iya gaisuwa ba ko?”.
Yayi mgnar cikin kasalalelliyar muryar data sa Khausar ƙara kallonsa domin bata taɓa saninsa da wannan kuryarba.
Ahankali ta sake yin ƙasa da kanta tana mai ɗan jin yadda yake mata wani irin abu da yatsunsa, cikin sanyi ta kawar da kanta gefe sai kuma ta motsa laɓɓanta tare da cewa.
“Ina yini”.
Yana shaƙan ƙamshin Kwallacar ta dake hargitsa mushimi kwanya yace.
“Lahfeyyahhh”.
Ƙasa tayi da kanta tana cigaba da wasa da Tuffan dake hannunta ita bata gutsira ba ita bata ajiye ba sai kuma yaji gaba ɗaya jikinta na amsa sabbin yanayi sabida sautin murya yadda ya amsa mata gaisuwar da yasata jin tsikar jikinta ya bada salon yum.
Shi kuwa Modibbo a hankali ya sake sanya babban yatsansa da mai bi masa akan sangalalina zuwa kan rumfar ƙafartan yana saƙƙo dashi a hankali tare da jujjuya kan yatsar.
Ahankali Khausar ta ɗago manya idanunta dake sheƙi ta kallesa.
Girarsa na dama ya ɗaga mata tare da jan dogon numfashi kana ya jingina bayansa da jikin Kujeran sai kuma ya marairaice idanunsa da suka fara rikiɗewa lokaci ɗaya wani irin yanayi ya fara ratsa sassan jikinsa musamman daya shaƙi ƙamshin Daddaɗan Kwallaca da kuma Humran da Momy ta siya mata wajen
_Aysha Aliyu Garkuwa_ .
Hajja Nana dake gefensu kuwa baki ta saki da ido cike da mamaki take binsu da kallo ganin wani irin shu'umi kana mayataccen kallon da sukewa juna kai kace tattabarune.
Da zaran ta kalli Khausar sai kuma ta juya ta kalli Namijin duniyan da shi yama mance da ita a wurin.
Zamansa ya gyara tare da sake tura ƙafarsa ya taɓa ƙafanta da kyau.
Ahankali ta kuma ɗaga manyan idanunta ta kallesa.
Ganin tana kallonsa yasa ya mata Signal tare da kashe mata ido ɗaya.
Ya Salam shine abinda ta iya faɗi cikin ranta.
Sabida abin yazo mata da saƙonni masu zafi, shi Modibbo ne kuwa, ya akayi haka harda signal abun yan ikkah ya iya.
Shi kuwa Modibbo cikin wani irin amintaccen yanayi ya kuma ɗaga mata girarsa ɗaya, sai kuma ya miƙe daga jinginar da yayi daga jikin Kujeran ya zauna dai-dai. Cikin yanayin gaza sarrafa tunaninsa da jikinsa ya ɗan fesar da numfashi tare da laso lips enshi kana a
hankali ya ɗago hannunsa tare da kafa guiwar hannun nasa, bisa table ɗin.
Hannunta dake kan Mug din dake gabanta ya riƙo cikin nasa hannun.
A tare suka ja nannauyan numfashi, kana a tare suka fesar da numfashin.
Ita kuwa Khausar ɗaya hannun nata da har zuwa lokacin take riƙe da Apple taci gaba da jujjuyawa tana maijin tamkar saman gajumare yake turata.
Yayinda shi kuma gwiwar hannunsa ke tokare da table ɗin.
Cikin yanayin mamaki ta buɗe Idanunta da baki tana kallonsa.
Gira ɗaya ya sake ɗaga mata yana lumshe idanunsa, a hankali ya matse hannunta acikin nasa bawai yanda zataji zafi irin dai ƴar matsarnan da tafi kama da tausaya yayiwa hannun yatsunta ya ɗan matse tare da zubawa faratunta ido .
Cikin wata irin kasala mai cike da shauƙi da dawowar yanayin da ya rayu kafin a sace J ɗinsa ya dawo mishi sabo, motsa laɓɓansa yayi a hankali tare da sanya ƙwayar idanunsa anata kana yace.
“Yahh mukayeeh dahh kehhh?”.
A kasalance ta lumshe idanunta acikin nasa kana ta buɗesu, baki ɗaya yanayin da yake mata magana ya tsumata wani irin yanayi take ji yana huda ko wani magudanan jinin jikinta yayin da sautin muryansa ke ratsa har ƙoƙon zuciyarta cikin wata shagwaɓaɓbiyar murya ta kalli idanunsa kana ahankali ta furta.
“Akan me ɗin?”.
Da sauri ya matse jikinsa, kana ya lumshe idanunsa sautin Muryanta nayi masa amsa kuwwa acikin dodon kunnensa yace.
“Ba cewa nayi ki yanke farcen nan ba?”.
Langwaɓar da kai tayi tana lumshe idanunta ta motsa laɓɓanta tare da cewa.
“Zan yanke ai”.
Numfashi ya fesar kana yace.
“Sai yaushe kenan?”.
Shiru tayi ta gaza cewa komai, sai zubawa sajensa ido da tayi sabida salonshi ya fara a yanayin da bata zataba.
Shi kuwa cikin sanyi ya ɗan ƙara matsowa tare yin mgnar can ƙasan maƙoshi yace.
“Ba tun jiya nace ki yanke ba baki yankeba, still yau ɗin tunda gari ya waye baki yanke ba har yanzu”.
Ta wani langwaɓar da kai tana mai narkar da ƙwayar idanunta cikin nasa tare da faɗin.
“To ai zan yanke”.
Baki sake Hajja Nana ke kallonsu ta kalli Khausar ta kalli Moddibo dake riƙe da hannun Khausar yana shafa saman tafin hannuntan da babbar yatsarshi ga wani irin fitinennen kalo da yake binta dashi kai kace zai cinyeta ɗanye ita kuwa Khausar duk ta saki da alamun da zata samu dama narkewa zatayi a jikinshi.
Moddibo kuwa har ga Allah har cikin ransa ya manta da cewa akwai wani mutum awajen.
Cikin lumshe idanu ya cigaba da shafa ƙafanta Khausar kuwa wani irin yanayi take ji aduk lokacin da sanyayyar yatsunsa suka sauka akan sharaɓanta.
Hajja Nana kam ta gaza ɗauke idanunta akansa kallon ikon Allah kawai take.