← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 150

Sashe 49

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sarki Youseef Mouleey kuwa cikin sauri ya buɗe wa Moddibo hannunsa kana cikin raunin murya da tsantsar bege yake faɗin.
“Zo ɗana”.
Moddibo kuwa tsintar kansa yayi da gaza yi musu gardama, kana zuciyarsa ta gamsu da kalaman da suke faɗa.
Yayin da yake jin su ɗin wani sashe ne na jikinsa.
Da wani irin bege da shauƙi ya faɗa jikin Sarki Youseep Mouleey ya rungumesa yayin da shima sarki Youseep Mouleey ya ƙanƙamesa ji yake kamar idan ya sake sa tamkar zai sake nesa dashi ne ciki rauni yake faɗin.
“Shakka babu wannan Aliyu nane”.
Kallonsa ya mayar kan Sheikh Jabeer kana yace.
“Abeey wallahi wannan ɗana ne.
Allah sarki rayuwa. Allah ya ɗauki ran Mahaifina yau da yaga jikinsa da zarrar da bai taɓa tunani da zato ba”.
Baki ɗaya kallonsu mutanen falon keyi cike da tarin tausayinsu.
Sarki Youseep Mouleey kuwa cikin rauni da farin ciki ya sake rungume Moddibo tare da kallon mahaifiyarsa Niyna yana faɗin.
“Niyna yau da Abbana na raye da yaga Jikinsa da Zarrar da zata girgiza Maƙiya, Da yaga jikinsa da zarrar da zata sa zuciyoyin maƙiya cikin tashin hankali da firgita tabbas Aliyu ɗana ne Niyna kalleshi fa”.
Kai Niyna take jinjinawa cike da gamsuwa tana mai shafa kan Modibbo.

Moddibo kuwa mamaki da al'ajabi ne ya cika masa zuciya ahankali ya janye jikinsa daga na Mahaifin nasa kana ya koma ya zauna yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

Ahankali ya maida idanunsa kan hoton Innayi kana ya dawo da kallonsa garesu cikin nutsuwa ya furta.
“Wacece wannan awajen ku? Kakata ce wacce da ita nake rayuwa, Kuma ita kaɗai nake da ita a duniyata”.
Cikin sauri Didi ta girgiza masa kai tare da faɗin.
“Kana da kowa aduniya. Kana da ƙanne, kana da Yayu, Kana da Mahaifi, Kana da Kakanni kakan ka ɗaya ne ya rasu Mahaifin Babanka, Kana da zuri'a zuri'arka mai tarin yawa gaba ɗaya wannan masarautar family'nka ne.
Aleey a ina kuke rayuwa?”.
Tun da ta fara magana ya tsira mata idanu yana sauraren ta har sai da tadasa aya kafin yace.
“A Nigeria muke rayuwa acikin Jahar Taraba Gembila” .
Da mamaki ta kallesa tare da faɗin.
“Allah sarki Innayi tana raye?”.
Da sauri ya kalleta jin Sunan Innayin sa abakinta sai kuma ya jinjina kai kana yace.
“Eh Innayi tana raye”.
Still idanunta na zubda hawaye ta furta.
“Allah sarki Innayi tayi min halarci mai yawa ashe wasiƙar data ajiye min da gaske ne ta kular min da ɗana kula mafi kyawu da inganci”.
Zazzafan Ajiyar zuciya ya sauke kana yace.
“Kin santa ne?”.
Kai ta jinjina masa tare da cewa.
“Na santa Hadima tace da aka haɗani da ita.
Jakadiyata da aka haɗani da ita tun daga lokacin da aka kawo ni ƙasar Marocco, ashe data tashi ƙasata ta koma da ɗana kusa da Jahata dan ta kular min da ɗana”.
Sai kuma ta lumshe idanunta akan Moddibo kana ta cigaba da faɗin.
“Sannan sai da tayi sanadin yanda ɗana zai kasance mutumi na gari har Alkur'ani mai girma ka rubuta ka kaiwa Mahaifina ya duba maka”.
Sai kuma ta mai da kallonta kan Sheikh Jabeer kana tace.
“Abeey Ya akayi baka taɓa kallonsa ba?”.
Sanyayyar numfashi Sheik Jabeer ya fesar cike da kamala yace.
“Fatima wannan abubuwane da tattaunawarsu sai ahankali kiyi haƙuri yanzu dai mu fara godewa Allah”.
Kai ta jinjina tana mai yin tasbihi azuciyarta...

Jakadiya kuwa cike da tsantsar farin ciki tace.
“Ai wannan ma babu bukatar wani bin cike ko wani abu tsatso ne na gidan nan, jinine na gidan nan, haihuwa ne na gidan nan,Tarbiyya ce ta gidan nan,Masha Allah”.
Ta sauƙe Ajiyar zuciya tare da cigaba da cewa. _“Fatabarakallahu Akhsanul Khaliƙin_, Halittace ta gidan nan daga gani ma babu tambaya tsatsone namu, ina Ibraahim yazo yaga ɗan uwansa da yake cewa yana haɗuwa dashi acikin mafarkai”.
Haka nan suka ci-gaba da tattaunawa cike da al'ajabi da mamaki wanda mgna ce ta gsky da gsky wacce gskyarce tayi aikin da dole Modibbo yaji zuciyarsa ta gamsu da kalamansu koda suka fara yi mishi tambaya kan yadda ya sarrafa Rinƙas ya shaida musu yasan Rinƙas a mafarkine ga mamkinsu dukkan wasu al'adu ko wani abu na sittin masarautar duk ya sani.

Cike da kulawa Sheikh Jabeer ya kalli Moddibo kana yace.
“Moddibo ka shiga ka kwanta in Allah ya kaimu da safe zamu ƙarasa magana”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Wayoyina suna cikin mota ina so akawo min su ina buƙatar mgn da innayi inada tarin tambayoyin da nakeso inyi mata”.
Kallonsa Sarki Youseep Mouleey kana ya girgiza masa kai tare da faɗin.
“Kada ka damu duk abinda kake buƙata ga hadimanka za'a yi maka sannan duk tambayoyinka ka tarasu lokacin amsasu nan tafe”.
Kai ya gyaɗa yana mai cigaba da jin nutsuwa su kuwa sallama suka masa kana suka fice.

Nigeria Gembulan
Dai-dai lokacin kuma Naseer ne, zaune tsakiya falonshi wasu hawaye masu zafin gaskene wani ke korar wani, tunda yaje gidan Lamiɗo, hira wurin Amina da Lamiɗo da kanshi ya sanar masa an daura auren Khausar da Modibbo ya kasa ƙara sawa cikin gidanma ya juyo ya dawo, kuka yayi tayi tamkar mace har yanzu ɗaya gaza bari kife kansa yayi bisa guiwowinsa a fili yake faɗin.
“Khausar ya za'ayi jinin haka, duk wani burina da sha'awata a kanki ne, na soki tun baki san kanki ba, rana tsaka ba zato ba tsammani inji wai an aura miki Modibbo, shike nan na rasaki kenan, domin na sani yafi ƙarfin iyawata, bani da abinda zan iyayi a kanshi, yayi min zarrar rayuwa ya kwace min ke”.
Sai kuma ya ɗan tsagaita kukan tare da kallon wayarsa da kiran Amina ya shigo, cikin tarin takaici ya kashe wayar a fili yace.
“Khausar ne kaɗai a raina Amina zan dai aureki ne dan biyan buƙatar rayuwata, da kuma rage jarabar rashin malakar Khausar ne”.
Haka yaci gaba da surutai kamar zautacce, Allah ya sani baiyi zaton hakaba.

Rabat Marocco
Washe gari tun shida da rabi na safe ƴan uwanshi mata suka shigo a jere, Lalla Hafsat ce riƙe da wani tray mai ɗauke da wasu ƴan ƙaran kwanuka masu kayan gani, Ragama kuwa wayace makale a kafaɗarta. inda yake suka nufa, jawo stoll Hafsat tayi tare da ajiye trayn kana ta fara haɗa mishi tea.
Lalla Khadijah kuwa hannun ta miƙe mishintare da yimishi sallama alamun musabaha takeso suyi.
a hankali ya ɗago hannunsa na dama ya miƙa ta, dai-dai lokacin kuma Rahama ta manna mishi wayar dake hannunta a kunne, tare da cewa.
“Yah Aleey ga Yah Ibraahim daga jiya zuwa yau ya kirani yafi sau goma, wai in ban haɗuka ba yaji muryarka in ya dawo bazai min mgn ba”.
Ɗan murmushin gefen baki yayi tare da sa hannushi na hagu ya amshi wayar.
It kuwa Rahama cikin jin dadi ta kalli askin kan Modibbo tare da cewa.
“Lah Yah Aleey ko askinkafa irin na ahlin masarautar Mouley ne”. sai kuma ta ƙara sunkuyowa kanshi tare da cewa.
“Lah Adda Khadi zoki gani, wlh shima yanada naɗeɗɗen gashin irin na Abualeey”.
Numfashi me ɗan tsawo ya fesar ganin Hafsat na miƙa mishi cup ɗin tea da kuma turo masa stoll din gabanshi tare da cewa.
“Bisimillah Didi tace ka ɗan taɓa wannan kafin ta ƙarasamaka breakfast inka”.
Longwaɓar da kai yayi tare da ɗan yamutsa fuska kana a hankali yace.
“Toh me ɗaya zanyi mgn a waya ko cin abinci ko gaisuwar ku, ko kuma kallon kaina zan bari Rahama tayi tayi”.
Ya ƙare mgnar da amsa sallamar da yaji anyi mishi da muryar da ta kasance irin tasa sak.
Sai kuma ya ɗanyi murmushi jin Ibraahim na cewa.
“Yah Aleey ka koresu in ba hakaba bazasu Barka ka huta ba fa more especially Rahama Bata da aiki sai suru”.
Cikin sanyi yace.
“Kana ina yanzu Ibraahim kai ban gankaba”.
Cikin jin daɗi Ibraahim yace.
“Ina Istanbul, nima jiya na tafi da safe kai kuma ka isa da yamma”.
Kai ya gyaɗa tare da kallon Hafsat dake miƙa mishi tea ɗin amsa yayi da hannunsa na dama. Ya lura kusan halinta iri ɗaya ne da nashi bata da yawan surutu da fara'a sosai sai dai kuma tana da kula.
Lalla Khadijah kuwa miƙewa tayi tare da cewa.
“Bari inje in taya Didi aiki”.
Kai ya gyaɗa mata kana ta fita.
Daga nan yaci gaba da mgn da Ibraahim, tare da kallon Hafsat dake ƙara mishi siymil wani abinci su ne na larabawan can da fulawa akeyishin sai dai ya wadatu da nama.

Cup din ya miƙawa Rahama tare da kallon Hafsat kana yace.
“Alhamdullah na ƙoshi, kai ta jinjina kana ta tattara wurin tare da cewa.
“Toh kaje ka ɗan kwanta ka huta, ke kuma Rahana zomi tafi".
Kai jinjina mata, daga nan suka fita suka tafi.
Chapter 49 · 0% Book details