← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 150

Sashe 94

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Masu son Maganin infection da maganin mata, ku marmatso wannan account no in ne naku ta ciki zaku turo kuɗin ku 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, Sai ki turo shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 08069423567. akwai sabbin kaya masu zafi suna nan bisa hanya, ki turo kuɗinki a saki cikin lissafi. Kayanen mata masu zafi sadidan daga Chadi akwaisu Garukan daka, gumbunan, Tsumummuka, cida Ciccibi Abodi cida kaza ci da jan nama kwanon ƙasaitacciyar mace biyar sirri, furar mata, gumbar madara Gumbar kolli mai ƙyallin al'khairi gumbar uku al'khairi, gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, gumbar riɗi, garin maɗi garin melɗamhi garin ilanwaddihi garin mallaka, tsumin riɗi tsumin tsirtai tsumin kinfi budurwa, tsumin riɗi, tsumin ta baje Sabaya, matsin maliƙi mai masifar matse mace matsin daɗi har maɗiga, mai ɗan kare kyau. Kullacar sirri al'ajabu shu'umar Humra, da duk sauran kan ƙamshi. Haɗin amarya budurwa ko bazawara haɗin mai jego ko uwar gida, akwaisu Available set ɗinmu hawa hawane akwai manya akwai ƙananan, ƙanan daga 40k ne 35k 30k 25k 20k 15k 10k shine ƙarami haɗina na karshe sai kuma haɗin kwanon ƙasaitacciyar shi 7k ne shine ƙarshen haɗina kenan... Manyan set ɗin kuma daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k ke zaki faɗi haɗin nawa kikeso anyi miki kana kimin bayanin yadda kikeso da matsalarki ni kuwa nasan abinda zan haɗa miki, ina araha kam amman ina hana bashi*

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 27*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Ido suka zuba kan gadon dake hargitse ga jini dake kai sai rigar baccin Khausar da suka gani gefen pillow.
Sai kuma suka kalli juna da mamaki gami da tausayin,
Ummi kama tuni hawaye ya cika mata ido a hankali tace.
“Toh ina take?.”
Da sauri Aunty Hajara ta rumtse idanunta ganin yadda beshid ɗin ya ɓaci da jini, musamman wannan farin ƙyalle mai heart dake tsakiyar gadon.

Da sauri ta jujjuya kanta sai kuma ta ta kalli ƙofar Bathroom ɗin sabida jiyo mgn can ƙasa-ƙasa da sauri tace.
“A'a Ummin Jameel kinji fa kamar mgn a cikin Bathroom dinsu”.
Sai kuma duk sukayi kasake alamun kasa kunne cikin mmki Ummin ta sauƙe numfashi tare da cewa.
“Ai kamar ma muryar Babane a ciki".

Shi kuwa Modibbo da duk saurin Didi ya rigasu, iso kuma da suka zo basu shiga cikiba iyakar Jakadiya ma falo, shiyasa basu san ya dawo ba, a zatonsu yana Masallaci kamar yadda haka al'adarsu take kafin ango ya dawo salla biyu daga cikin ƴan uwanta da dole al'adar masarautarsunce in an kawo amarya ma sai an bar mata biyu, masu maidawa iyayen yarinya tukuici in ta kawo budurcinta da kuma kai hatimin mulki da za'a mallakawa mata shaidar kasantuwarta Gimbiya kenan.

Toh koda ya dawo kawai ciɗak ya ɗagata ya nufi Bathroom da ita, yana shiga ya direta cikin ruwan ɗumin daya haɗa mata, tun kafin ya tafi.

Jin yadda zafin ruwan ke ratsata ne yasa take yayyarfa hannunta tare da sakin raunataccen kuka murya adisashe.
A hankali ya ɗan tallaɓe kanta tare da mannawa da ƙirjinsa cikin sanyi mai cike da bayyanar asalin matsayinta dake cikin zuciyarsa yace.
“Sannu kiyi haƙuri ki zauna zakiji sauƙin ciwon sosai”.
Ya ƙare mgnar da dan ƙara zaunar da ita cikin ruwan ɗumin,
wani raunataccen ƙara ta kuma saki wanda yasa har Jakadiya da Didi dake falo suka jiyota, cikin sauri Jakadiya ta kalli Didi tare da cewa.
“Inaga sun ɗagata bari mu ɗauko ƙyallen tarihinmu da zanin gadonmu”.
Kai kawai Didi ta gyaɗa mata.
Allah yasani ji take kamar ta shiga to amman ba dama tunda Ita dai surkuwa ce.

A can cikin ɗakin kuwa Ummi da Aunty Hajara kam bushewa sukayi a tsaye kamar wasu sakarkaru, suke kallon ƙofar Bathroom ɗin fuskoki cike da mamaki.

Da sauri suka juyo suka kalli ƙofar jin a buɗe Jakadiya da yanzu ta shigo, kwaryan dake hannunta ta miƙa Ummi tare da cewa.
“Gashi ta zauna ciki ammafa kada ta wuce 2 minute”.
Toh Ummi tace tare da amsa kana ta ajiye ƙwarya, sai kuma ta kalli Aunty Hajara dake ruggume da hannun.
“Inaji mafa kamar tana tare da mijinta ne a Bathroom ɗin."
Aunty Hajara ta faɗa.
Murmushi Jakadiya tayi tare da cewa.
“Ato shike nan ai ni bari in na ɗe..."
Sai kuma suka kalli ƙofar Bathroom jin kamar an buɗe, shi kuwa Modibbo jin alamun surutaine yasa ya ɗan miƙe tsaye kana ya buɗe ƙofar dan yaji surune da gaske akeyi a ɗakin.
Da sauri yayi ƙasa da kanshi ganin Ummi.
Ita kuwa Ummi cike da kunya ta miƙa mishi kwaryar nan da Jakadiya ta bata tana mai kauda kai tace.
“Gashi ta zauna ciki, Amman kada ta wuce daƙiƙu biyu”.
Cikin tsaanin kunya yayi ƙasa da kanshi tare da amsar kwaryar, ya juya cikin Bathroom ɗin da sauri ya maida ƙofar ya rufe ba tare da yace komai ba kana bai bari sun haɗa idoba.
Itama Ummi cikin kunya ta kama hannun Aunty Hajara suka fita.
Jakadiya kuwa murmushi mai cike da jin daɗi tayi, tare da shimfiɗa wani farin leda mai taushi a gefen gadon zai kuma ta ɗan jawo wannan farin ƙyalle mai zanen heart ta sanyashi cikkn ledan kana ta maida shi ta liƙe ya zama kana iya ganin duk jinin dake jikin ƙyallen sai kuma ta sa hannun ta ɗauko wani ɗan bugeggen katako mai zagaye da gold a jiki, kana an yishi da marfin glass daga saman an Rubuta MRS Aleeyu Mouleey, da manyan baƙin larabci.
Sai a ƙasan kuma aka rubuta. Lalla Khausar.
Cikin ta shimfiɗa ƙyallen tare da maida marfin glass ɗin ta rufe, sai ya zama tamkar abun aje hoto, sai kuma daga ge da gefensa da ke ɗauke da tambarin masarautar Mouley ɗin.
Cikin sauri-sauri ta naɗa beshit ɗin kana ta zaro wani fari mai ɗauke da alamun zanen masarautarsun ta shimfiɗa tare da sa rigunan pillow da blanket.
Sai kuma ta ɗaukesu tare da fitowa falo da sauri.

Tana fita Lalla Khadijah na isowa da kaskon turaren wuta,
Da sauri ta miƙa wa Didi wannan furem ɗin ƙyallen da kuma sanin gadon, cike da jin dadi Didinta amsa ita kuwa Jakadiya, amsa kaskon turaren wuta tayi ta koma ɗakin ta ajiye.
Gefen gado kana ta jawo ledan nan, ta fito da wata dandatstsiyar Alƙyabbata irin ta matan masarautar Mouley ɗin, sai kuma wata tattausar riga mai gajeren hannun, dukansu kolon tutar masarautar sune sai fararen ondis.
Turarukan data kawo tajera gefen kayan.
Sai kuma ta juya ta koma falo bayan ta ƙarasa kimtsa ɗakin.

A nan cikin Bathroom kuwa, cikin wani irin fitinennen kallo Modibbo ke kallon Khausar da ta tura lip inta na kasa tare da kwaɓe fuska, har lau hawaye na tsiyaya, cikin sanyi ya ɗan tallabo kanta da hannunsa duka biyu, manyan yatsunshi yasa tare da fara goge mata hawayen, murya cike da taushi, tausayi, gamin da jinƙai yace.
“Kiyi haƙuri ko, kin yafewa Yah Mu'allim dinki ko?”. Cikin Shesh-sheƙan sabida jin yadda zafin ruwan ke ratsa mata jiki, ga wani irin fitinennen zazzaɓi da ciwon kai da sukayi mata taron dangi, murya a disashe tace.
“Allah zai saka min”. Da sauri ya kauda kanshi gefe jin murmushi na gaba da subce mishi, ita kuwa kuka ta ɗan saki tare da cewa.
“Ai dama na gayawa Ummi haka zakayi ta cin zalina amman suka ki yarda, Allah zai saka min”.
Cikin sanyi ya ɗan tsuke fuska kana yace.
“Zo nan, zo ki shiga cikin wannan inji Ummi”.
Da sauri ta rumtse idanunta jin ya tallabota ya ɗagota, sai kuma yayi saurin ruggume ta, jin yadda ta saki wata ƙara mai cike da alamun galabaita.
A hankali ya zaunar da ita cikin kwaryar.
Da ƙarfi ta saki ƙara tare da cakumo wuyanshi ta matseshi gam a jikinta da yake rawa kar-kar sabida zafi gami da raɗaɗin da jininta ya ɗauka.

Rumtse idanunsa yayi da ƙarfi dan ba ƙaramar shaƙa tayi mishi ba, sai kuma ya fara sauƙe ajiyan zuciya jin ta fara sassauta cacumar da tayi mishi, ido ya zuba mata jin yadda take ta sauƙe ajiyan zuciya a jere a jere, sai kuma wani irin fitinennen zufa daya keto mata tako ina a jikinta.
Chapter 94 · 0% Book details