← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 150

Sashe 124

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Asma'u kuwa cikin yanayin tsoro ganin abinda Amina keyi ta shiga jan hannun Khausar dake zaune tana cewa.
“Khausar mu tafi”.
Cikin dashewar murya da rauni Amina ta kalli Asma'u tare da faɗin.
“Ayyah Asma'u am ki barni in nemi yafiyarta”.
Kai Khausar ta girgiza cikin sake jin tsoron Allah da tsoron hakkin mutum tace.
“Amina wallahi na yafe miki duniya da lahira”.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya tace.
“Toh kicewa Momynki ma ta yafemana”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da cewa.
“In sha Allah Momy zata yafe muku Momy kam ma bata riƙe ku ba”.
Asma'u kam.da ƙarfi taja hannun Khausar suka fita daga bedroom

Khausar kam wani irin tsoro gami da mamakine ya mamaye mata zuciya ganin yanda rayuwa ta juye dasu suna fitowa compound ɗin gidan Samira Sani da Hajiya Lami na shigawo.

Samira na ganin Khausar ta nufeta tare da fashewa da kuka kana ta rike hannunta tare da cewa.
“Khausar! kece haka?”.
Cikin sanyin jiki Khausar ta gyaɗa mata kai tare da faɗin.
“Eh nice Samira ya gida”
Ta ida maganar tana kawar da kai gefe saboda wani irin masifeffen wari da take ji Samira kuwa cikin rauni tace.
“Khausar ki yafe mana Khausar dubi yanda Allah ya dawo dani”.
Idanunta ta mayar kan cikin Khausar daya fara tashi kasancewar rigar jikinta lafaffiya ce cikin sanyi ta cigaba da cewa.
“Ayyah Khausar dubi yanda Allah ya miki gata arayuwa sabida kin bishi, mukuma dubi yanda Allah ya mayar mana da mugayen aiyukabmu damu”.
Hajiya Lami dake gefe wacce duk yanda Samira taso gudu ta barta batare data biyo taba sai da ta manne ta biyota ta fashe da wani irin dariya mai firgitarwa kana ta tafe hannu tare da faɗin.
“Iyyeee sukam ai sunbi Allah sun samu yanda suke so mu da muka bi Bokaye baga nan sakamakon mu yanda ya dawo ba Itama Hajiya Bunayya Stuliya ta ruɓe tsutsotsi na zuba ke kuma gaki nan kinata Yoyon ruwa mai ɗoyi Ni kuma gani nan gani nan dai Ni ba mai hankali ba niba mara hankali ba”.
Cikin zubda hawaye Samira tace.
“Dan Allah Momy ki daina surutan nan”.
Ta wani zare idanu tana kallon Samira tace.
“Wani irin surutai zan daina ai gaskiya nake faɗa abinda muka aikata ne yoh tunda ma Allah ya ɓallomin waɗanan sutura akwai wanda ya isa ya hanani zubasune ai nice nan mai tona asirinmu”.
Bisa alamu dai yadda take maganganu ƙwaƙwalwarta ya fara taɓuwa ne ta dawo sha tara sha tara haka hankalin ya zama tara da indagi.
Khausar kam baki ɗaya ilahirin jikinta rawa ya fara Allah ya sani tana masifar tsoron Mahaukaciya ga kuma Hajiya Lami dake nan atsaye ƙam kaman ƙiran Samudawa ga tsawo ga jiki da uban zuguda.

Asma'u kam cikin sauri taja hannunta suka fita dai-dai lokacin Haiydar da Bashir suka zo akan mashin Bashir ya goyi Asma'u kana Haiydar ya goyi Khausar suka nufi gidan Ummi.

Suna isa Falon Ummi suka gaishe da Goggonayen Asma'u ƙannen Malam Ahmad da ƴan uwan Ummu kana suka wuce bedroom ɗin Asma'u...

Suna zama dai-dai lokacin kira ya shigo wayar Khausar ahankali ta ɗaga ganin sunan Moddibo yasa tayi picking.
Daga ɗaya ɓangaren ta tsinkayo sanyayyar muryansa na cewa.
“Minha”.
Cikin sanyi ta gyara zamanta murya cike da rauni tace.
“Na'am Yah Mu'allim”.
Cike da kulawa yace.
“Lafiya kuwa ya naji kinyi sanyi”.
Kai ta girgiza tare da cewa.
“Bakomai Yah Mu'allim?”
Da damuwa yace.
“Ina kike yanzu?”.
Ahankali ta ɗan lumshe Idanunta tare da cewa.
“Ina gidan Ummi ”.
Ɗan tsuke fuska yayi kana yace.
“Minha meyesa kike son yawo ne?.
Toma tukun meyasa da zakije baki kirani kin faɗa min ba”.
Still asanyaye tace.
“Yah Mu'allim kayi haƙuri nida Asma'u muka taho kuma Haiydar ne ya kawo mu”.
Da sauri ya zare idanunsa yace.
“Ya za'a yi Haiydar ya kawo? ki akan me ya kawo ki?”.
Numfashi ta fesar tare da faɗin.
“Akan Mashin ya kawo ni”.
Cikin bada umarni yace.
“Bana so kada ki sake hawa Mashin banaso”.
Kai ta gyaɗa tace.
“Yah Mu'allim kayi haƙuri bazan sake ba”.
Ahankali ya sassauta muryansa tare da gyara zamansa acikin mota yana kallon Dr Jameel da Zakariyya yace.
“Tukunna ma yanzu menene matsalar ki naji duk kinyi sanyi”.
Muryanta na rawa irin na wanda ke gan da zubda hawaye tace.
“Yah Mu'allim Amina da Umma ce basu da lafiya sai kaga yanda suka dawo”.
Cikin rashin fahimta ya shafa sajensa tare da faɗin.
“Wacece Amina?”.
Cikin sauri tace.
“Yah Mu'allim ya za'a yi kace min wacece Amina ka manta Amina?”.
Ɗan shiru yayi sai kuma yace.
“Gaskiya na manta ta”.
Tana jinginar da kanta jikin gadon Asma'u tace.
“Wannan wacce muke zuwa makaranta tare Yah Mu'allim ya za'a yi kace baka santa ba”.
Numfashi ya fesar tare da cewa.
“Ok na tuna ta”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Wallahi bata da lafiya”.
Ba yabo ba fallasa yace.
“Ayyah Allah yaye musu”.
“Ameen”
Ta amsa sai kuma tace.
“Ayyah Yah Mu'allim kayi ta musu addu'a Allah ya basu lafiya”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Toh Allah Ubangiji ya yaye musu ya basu lafiya”.
Ahankali ta gyara zamanta kana tace.
“Kuma inso samu ne dan Allah kasa Dr Jameel yazo ya duba su da jiki”.
Yana lumshe Idanunsa yace.
“Yanzu dai tukunna muyi Abin dake gabanmu Ni naji gaba ɗaya kinyi sanyi shine matsalata”.
Cikin tabbatarwa tace.
“Wallahi lafiya ta lau kawai dai jikin sune”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Ok toh Allah ya basu lafiya in Sha Allahu za'a yi musu addu'a kuma Dr Jameel zai zo ya duba su hankalinki ya kwanta”.
Kamar yana gabanta ta gyaɗa masa kai.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Toh yanzu bari muna zuwa dan Dr Jameel ma yana son ganin Asma'u”.
Kai ta gyaɗa kana sukayi sallama.
Ba daɗewa suka isa a waya Moddibo ya kirata tare tare da sanar mata sunzo yana dakin Bashir kana Asma'u kuma ta samu Dr Jameel a mota.
Chapter 124 · 0% Book details