Sashe 54
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan awa ɗaya, sun ci sun sha Hajiya Bunayya ta kalli Hajja Nana dake goge baki da Tissue tace.
“Wannan al'amari dai da ɗure kai yake”.
Cikin taɓe baki Hajja Nana tace.
“Toh Ni dai fatana dai Allah yasa basayar damu akazo yi ba ehee”.
Dariya mai sauti Innayi ta sanya ganin yanda Hajja ke magana tsakaninta da Allah cike da kamala tace.
“Babu Sai dawa sai karramawa wanda gadon mune, kuma ma in banda abinki a saidaku a nemi me, ki dai dubafa duk wata ɓukata da ɗan Adam yake dashi muna dashi a masarautarmu”.
Ummi kam murmushi kawai take, dan talura Hajja Nana da innayi har yanzu ba'a shiryaba.
Suna cikin haka sukaji sallama, tare da ganin jagorancin Hadiman Didi
Cike da zaƙuwa ta tashigo tare da Jakadiyar ta da kuma Kakar Moddibo Niyna sai kuma su Rahama bakinsu ɗauke da sallama.
Innayi na ganin Didi tayi saurin miƙewa tare da durƙusawa agabanta kana ta sunkuyar da kanta ƙasa batare da tace Uffan ba.
Didi kuwa cikin yalwataccen farin ciki ta tsugunna tare da sanya hannunta akafaɗar Innayi kana ta ɗagota ta tsayar da ita suna fuskar juna, sai kuma kawai ta ruggumeta tare da faɗin.
“Kin gama min komai Innayi kiyi min duk kan abinda ɗan Adam zai yiwa abokin zamansa na halacci, daga yau na ƴan taki kin tashi daga Baiwa kin zama ƴa ƴan tacciya kuma Uwa amintacciya kuma kamila kuma cikekkiyar jakadar sarki mai jirangado”.
Dariya mai sauti Innayi ta sanya wanda ke nuni da zallan farin ciki kana tace
“Alhamdulillah Nagode wa Allah ina tahowa zuciyata na tsinkewa ina tunanin shin ya rayuwa ta kasance shin ana raye ko kuma anbar duniya zuciyata ta cika da fargaba”.
Baki ɗaya mutanen falon kallonsu suke cike da tsantsar mamaki musamman Hajiya Bunayya da wani irin zufan hasada ke fita agoshinta.
Innayi kuwa cike da annashuwa ta cigaba da faɗin.
“Amma Alhamdulillah nayi katari da Youseef akan karagar mulki kana kema nayi katarin dake acikin shigar Gimbiyya amma banga Ubangida naba Sarki Muhammad Aliyu Mouley”.
Kai Jakadiya ta girgiza kana tace.
“Allah yayiwa Sarki Muhammad rasuwa yanzu ɗanki ne Youseef akan Mulki”.
Cikin sanyi Innayi tace.
“Allah sarki, Sarki Muhammad Mouleey. Ubangji Allah yajiƙan sa da Rahma”.
Amin suka amsa a tare,
Ita kuwa innayi juyawa tayi tare da kallonsu Hajja Nana da suka zubo musu idanu sai kuma ta maida idanunta kan Didi tace.
“Yanzu dai idan na fahimta Moddibona Aliyuna shine Yariman Masarautar nan? kuma Sarki Mai Jiran gado?”.
Yalwataccen murmushi Didi ta Saki kana tace.
“Tabbas kuwa shine ɗa Namiji babba A masarautar nan kuma ɗa Mai jiran gado Ahamdulillah kuma ya dawo alokacin da Masarauta ke jiranshi”.
Kai Jakadiya ta jinjina kana tace.
“Sosai kam”.
Didi kuwa cike da nutsuwa ta nufi kujeran dake tsakiyarsu kana ta zauna murmushi ta sakar musu da lallausan murmushi tare da faɗin.
“Jaɓɓama Moɗon”.
Ga Mamakinsu sai sukaji tayi musu magana cikin Harshen Fullanci.
Cikin yanayin mamaki Hajja Nana tace.
“Allah bauɗo be Fulfulde voli, kamar da fulatanci kike yi mgn fa ko?”.
Murmushi ta saki kana tace.
“Sosai ma kuwa Asalina Bafulatanar Adamawa ce ni ɗuyace ga Sarkin Joɗah Sheiykh Jabeer”.
Kai Hajja Nana ta jinjina kana tace.
“Ai kuwa lallai gashi Yaren da kike mana dashi ya tabbatar mana da hakan”.
Wani irin zufa mai kamar tafasasshen ruwan zafine ke tsats-tsafowa Hajiya Bunayya abaki ɗaya ilahirin jikinta acikin ranta take mgn kamar zautacciya.
“Toh shin Me hakan yake nufi, kenan haka nufin Khausar tayi katari ta tsinci dami a akala? Ko shegiyar yarinyar da wayo kamar dala, ko dai dama ita tasan Modibbo ɗan manya ne, kaji shegiyar yarinya da iya bada kafa, yoh da na sani ai wlh shi Amina zata aura.
Ashe Samira da abinda ta hanga.”
Gaba ɗaya tayi kasake ta tafi dogon tunanin.
Ƙanwar Mommy Aunty Hajara. cike da farin ciki tace.
“Khausar Lelelwal asheko da gaske Lelelwal ɗince ke”.
Murmushi Aunty Ruƙayya tayi kana tace.
“Tabbas kuwa abu yayi yadda ran masoya ke so. Dama wani hanin ga Allah Baiwa ce”.
Hira suka cigaba dayi cike da farin ciki da mutunta juna saɓanin Hajiya Bunayya dake cikin tashin hankali da ƙunan zuciya.
Acan ɓangaren su Abban Jameel kuwa Sarki Youseef Mouley da Sheik Jabeer ne suka nufi masauƙin su.
Sheikh Lamiɗo na kallon Sheikh Jabeer ya faɗaɗa murmushin fuskarsa cike da kamala yace.
“Allah nhokke sabugo Sarkin Joɗa kana shagaban ƙungiyar TABITAL POOLAKU, da mi yetti Allah da kansa ne a nan?”.
Kai Sheykh Jabeer ya jinjina kana cike da girmamawa yace.
“Ikon Allah Allah yayi mun haɗu kenan?”.
Murmushi Lamido yayi tare da zamewa gefensa dan shi kansa yasan idan ana batun sarauta toh in su Sheiykh Jabeer na kusa shi dole a ƙasa zai zauna.
Shi kuwa Sheykh Jabeer cikin kamala da kulawa yace.
“Ikon Allah sai kuma muka haɗu anan, amma yanzu dai ku huta in Allah ya kaimu gobe sai muji meke tafe daku?”.
Cikin gamsu Lamido da Abban Jameel sukace to.
Su kuwa daga nan suka fice...
Acan ɓangaren su Didi ma Sallama suka yiwa su Innayi tare da faɗin su huta gobe zasu ci gaba da tattaunawa Godiya sukayi musu kana suka fice.
Washe gari da safe misalin ƙarfe 9:00am Innayi, Hajja Nana, Jakadiya Sheikh Jabeer, Sarki Youseef Mouley, Galadima, Waziri, Didi Abban Jameel, Ummi, Baffa Jimeta Lamiɗo jakadiyarta zaune suke wuri na musamman kuma keɓantaccen palon Abualeey wato sarki Youseef Mouley kenan. yayin da baki daya idanunsu ke kan Innayi.
Innayi kuwa cikin sauƙe numfashi ta cigaba da basu labarin tun randa ta tafi da Modibbo ta wuce Nigeria dashi kana ta nufi Taraba yankin Gembulan sabida sanin yanki fulanine domin Didi na bata labarin, kuma ta iya fulatanci tun a lokacin domin Modibbo shine ɗa na shida a wurin iyayensa daga Khadijah da Hafsat sai da akayi ya'ya uku maza duk basa gama arba'in ake nemansu a rasa sai bayan kwanaki sai a tsinci gawarsu. A wannan lokacin kuma Khadijah da Hafsat sunyi girma da bazasu mance kamannin innayi ba shiyasa sunka ganeta.
Fesar da numfashi innayi tayi kana taci gaba da labarta musu, yanda ta rayu da Moddibo yanda ya taso da yanda yayi karatu, da irin ƙalubalen daya fuskanta, da amintakarsa da Jameel har zuwa mutuwar M Jameel da kuma dalilin zuwansa Morocco da kuma irin ƙalubale da baƙaƙen magana da kuma hantara da suka samu awajen mutane kana ta ɗora kuma da wasiyyar da M Jameel ya bar musu akan Modibbo, haɗin da basu labarin Khausar da dole in dai za'a bada labarin Modibbo da Jameel toh dole cikaton na uku Khausar ce.
Didi Kam lumshe idanunta tayi wani abin idan taji tayi murmushi wani ta zubda hawaye saboda tausayin halin da ɗan ta yakasance cikin na rashin aminisa da kuma rashin su a kusa dashi da ya zame masa sanadin da ake shegantashi.
Cikin sanyin murya tace.
“Allah sarki ɗana Jameel Allah baiyi zamu ganka ba bare muyi maka godiyar kekkyawar amintakarka da gudan jinin, sai dai Alhamdulillah Innayi tunda Jameel bai mutu da rashin sanin iyayen amininsa, in Sha Allah mukuwa zamu kasance mashinyi mishi addu'a a tsawon rayuwarmu. Ummin Jameel Ngd MATUƘA Abban Jameel babu abinda zance daku sai addu'a. tabbas Aliyu na kuma yaga jarrabawar rayuwa wanda nasan ya samu darussan rayuwa masu tarin yawa acikinsu Innayi na gode kinyi min halarcin da bazan taɓa mantawa ba kin tseratar da rayuwar ɗana alokacin da ake neman hallakasa kamar yadda akayi ta hallaka yan uwansa da suka gabata”.
Murmushi Innayi tayi kana tace.
“Wannan yiwa kai ne sannan babu godiya tsakanin mu domin kin cancanci fiye da haka sabida matsayin uwa kika riƙeni ba Hadimarkiba, shiyasa nima nayi miki abinda zan iya yiwa ƴaƴana na cikina”.
Kai Didi ta jinjina tare da juyowa ta kalli Ummin Jameel dake sharce hawaye cikin sanyi tace.
“Ummin Jameel kada kiyi kuka ga Aliyu na in Sha Allah ya ishemu nidake baki ɗaya”.
Cikin gamsuwa Ummu tace.
“In sha Allah kuwa”.
Innayi kuma gyara zamanta tayi tare da cewa.
“Toh Alhamdulillah bayan ta howarsa nan.
Muka gama mgnar komai akan Khausar da bai sani ba. toh Alhamdulillah dama acikin labarin dana baku na faɗa muku wasiyyar da amininsa Jameel ya bari toh Alhamdulillah a makkoni biyu da suka gabata an Aura masa Khausar”.
Cikin wani irin Didi ta kalli innayi tare da cewa.
“Aliyun akayiwa aure!”.
Da sauri innayi ta gyaɗa mata kai kana tayi ƙasa da kanta.
Sai kuma innayi tayi saurin ɗago kanta jin Didina faɗin.
“A....!
Ba editing kam