← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 150

Sashe 48

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin fesar da numfashi ya koma kan step ɗin ya tsaya a Balcony yana mai cigaba da kallon tsananin kyau da tsaruwan wajen tun da yake a iya tsawon rayuwarsa bai taɓa kallon falo mai masifar girma da kyau irin wannan ba.
Ahankali ya ɗaga idanunsa sama anan ya hango ainihin tsakiyar Fadan.
Babbar Fadace mai masifar kyau da girma akwai wurare daban-daban yayin da Part-part sunfi aƙirga iya inda idanunsa ke iya hangowa Part-part ne ashimfiɗe sai kuma hadimai da yake hangowa suna zirga-zirga wanda bazai iya ƙiyasta yawansu ba, ga wani irin wuta mai haske da ƙyalli daya haske ko ina na cikin fadar tamkar rana kana ga bishiyoyin dabino da mijin gwanda wanda duk ta inda ka cilla ido suke rausayawa sai zurga-zurga Hadimai keyi.
Ahankali ya juya bayansa daga gefe nan idanunsa suka hango wani garden Mai azabebben kyau daga can bayan Garden ɗin kuwa wani Swimming pool ne dake ɗauke da ruwa Sky blue ga wasu fararen kujeru kaman resting Chair dake gewaye da wajen kana daga ƙasa su kuwa Grass Carpet ne da yayi dark blue Mai azabar kyau yayin da wasu irin tsuntsaye masu kyan gani da daɗin sautin murya ke shawagi awajen wanda da alama saboda ƙayatarwa aka ajiye su...

Ya ɗauki tsawon lokaci yana kallon wajen haka nan ya tsinci kansa da son ganin wajen domin kallon wajen yatuno masa da Gembilan sak yanayin tsarin gidansu haka wajen yake sai dai tsarin wannan ba suda yalwan Furanni haka kawai aransa yaji da ace za'a bashi dama zai ƙawata Ilahirin Fadar da Furanni saboda arayuwar duniya babu abinda ke sashi farin ciki kamar yai ta kallon Furanni har misalin 11:30 yana tsaye awajen kafin ahankali ya motsa ƙafafunsa jin sun gaji da tsayuwa kana ya gangaro ya dawo cikin ainihin falon da aka kawo sa...

Yana shiga falon ya zauna akan kujera tare da lumshe manyan idanunsa dake lumshe yana mai sakin ajiyar zuciya akai-akai.
Zaman sa babu daɗe wa kamar misalin 12:00 yaji ƙaran ƙofa an buɗe.
Jin ƙaran buɗe ƙofa yasa ya buɗe Idanunsa dake lumshe kana yabi wajen da kallo...
Da mamaki yake kallon Jabeer bin Jabeer da suka haɗu ajirgi kasancewar shine agaba.
Jabeer bin Jabeer kuwa cikin ƙaguwa ya maida idanunsa kan Didi da Lalla Khadijah da Hafsat ke gefenta, tare da cewa.
“Didi shigo kiganifa, Didi dan Allah ki ganshi da kyau fa”.
Sheikh Jabeer, Sarki Youseep Muhammad Mouleey, Waziri Galadima, Sarkin Dawakai, Jakadiya, Mahaifiyar Sarki Niyna Lalla Khadijah da Lalla Hafsat sai kuma Rahama dake can biya tana biyosu da sassarfa tare da faɗin.
“Didi ku jirani mana”.
Su kuwa cikin nutsuwa suka shiga cikin falon.
Suna shiga Moddibo ya zuba musu ido cike da mamaki yake bin Didi da Abualeey da wani irin amintaccen kallo yana mai jin wani irin yanayi na ratsa mishi zuciya a kansu haka nan ya gaza janye idanushi a kansu sai bugun da zuciyarsa keyi.
Lalla Khadijah da Hafsat kuwa ruggumeshi sukayi tare da sakin wani sassayyan kuka, wannan na gefen dama wannan na gefen hagu,
Rahama kuma na isa, sai kawai ta kifen kanta bisa guiwowinsa tare da faɗin.
“Yah Aleey laisa leeh misluka abadan, ana uhubbuki hubban azeeman”.
wani irin amintaccen nitsuwa ne yaji yana ratsashi, wanda yasa baisan lokacin da yasa tafukan hannunsa yana sharewa Lalla Khadijah da Hafsat hawayeba.
Su kuwa Khadijah da Hafsat sai kuma suka ɗan janye jikinsu tare da ruggume juna cike da tsananin farin cikin.
Ita kuwa Rahama cikin yanayin shogwaɓar ƴan auta take ɗan kuka tare da cewa.
“Yah Ibraahim ina kake kazo kaga Yah Aleey na ya fika kyau daga yauma niba ruwana da kai”.
Dan fesar da numfashi Modibbo yayi tare da sa hannushi yana ɗan shafa bayan Rahama alamun tayi shiru.

Sarki Youseep Mouleey kuwa cikin kamala ya zauna bisa kujera kana Sheikh Jabeer ma ya zauna gefensa yayin da Galadima, Waziri, Sarkin Dawakai, suka zauna a ƙasa.
Amintattun Hadiman dake biye dasu kuwa daga can baya dasu suka zauna.
Jakadiya kuwa idanunta akan Moddibo ta saki yalwataccen murmushi mai cike da zallan farin ciki kana tace.
“Masha Allah nesa ta matso kusa abin nema ya samu”.
Moddibo kuwa idanu ya zuba musu baya ko ƙyaftawa ganin Jabeer bin Jabeer ya zauna aƙasa gasu Galadima sai shima ya zamo daga kan kushin ɗin ya zauna akan Carpet tare dasa hannunsa yana sharewa rahama hawaye.
Yayin da yake kallon Sheikh Jabeer cike da mamaki kasancewar ya masa farin sani domin yasha zuwa wajensa a Adamawa sai dai baya samun haɗuwa dashi cikin tsananin mamaki ya motsa laɓɓansa tare da faɗin.
“Sheikh Jabeer”.
Sheikh Jabeer na kallonsa tare da mamakin kiran sunan sa ya furta.
“Na'am. Ka Sanni ne?”.
Ware idanu Moddibo yayi kana ya jinjina masa kai cikin sanyi Murya da yanayin nutsuwarsa yace.
“Farin sani ma kuwa shekaran Kur'anin dana rubuta na farko kusan uku awajenka wanda na rubuta daga baya kuma yayi cika shekara ɗaya awajenka amma har yanzu ban samu an dubasuba.
Batare da Sheikh Jabeer ya janye idanunsa daga kansa ba yace.
“Menene sunan ka”.
Moddibo kuwa ahankali yace.
“Sunana Moddibo daga Taraba nake tura maka wanda aminina Jameel Bashir Mai Dala yake kai maka”.
Baki ɗaya falon ya sake yin shiru baka jin muryan kowa sai na Moddibo da Sheikh Jabeer yayin da Didi da Sarki Youseep Mouleey kuwa jikinsu ke wani irin tsuma aduk lokacin da Muryan Moddibo ya ratsa kunnensu.
Kai Sheikh Jabeer ya jinjina kana yace.
“Toh menene cikekken sunanka ai Moddibo ba sunan yanka bane?”.
Lumshe idanu Moddibo yayi tare da buɗe su kana ya shafa sajensa a hankali yace.
“Sunana Aliyu Youseep Muhammad Mouleey”.
Cikin matsanancin mamaki daya sake mamaye zuciyoyinsu da tabbatar musu lallai babu haufi jininsu ne, akaro na barkatai suka juya suka shiga kallon junansu da ƙyar Sheikh Jabeer ya furta.
“Kace me sunan ka?”.
Ahankali Moddibo ya kuma motsa laɓɓansa tare da faɗin.
“Sunana Aliyu Youseep Muhammad Mouleey”.
Cike da matsanancin mamaki daya daki zuciyoyinsu suka haɗa baki wajen faɗin.
“Ikon Allah sunan ka kenan?”.
Kai ya gyaɗa yana ɗan ciza lips ɗin sa na ƙasa ya furta.
“Eh sunana kenan?”.
Ahankali Sheikh Jabeer ya furta.
“Ikon Allah toh waye mahaifinka”.
Araunane ya jingina bayansa da jikin Kujeran kana ya girgiza kai tare da lumshe idanunsa yace.
“Babana ya rasu!”.
Da sauri Lalla Khadijah tace.
“Wlh mahaifinka na raye gashi nan a gabansa kusa da kai”.

Cikin Sauri Didi ta katse Khadijah ta hanyar daga mata hannun, kana ta juyo ta kalli Modibbo zuciyarta na cigaba da bugawa da karfi tamkar zai fasa ƙirjinta ya fito ta tace.
“Toh wacece Mahaifiyarka!?”.
Idanunsa cike da rauni ya buɗe ya kalleta kana yace.
“Mahaifiyata ma ta rasu”.
Cikin sauri Rahama tace.
“Ga Didi nan a gabanka a raye waya ce maka baka da mama”.
haka nan yakejin baya son kukan Rahma har ransa, ya kuma lura ta ƙoshi da sakalci cikin sanyi yake jujjuya mata kai alamun kada tayi kuka.
Sarki Youseep Mouleey kuwa cikin sauri yayi gyaran murya tare da faɗin.
“Toh waya faɗa maka Iyayen ka sun rasu?”.
Moddibo kuwa cikin sanyi da fesar da numfashi ya kallesa kana ya gyara zamansa tare da faɗin.
“Kakata ce ta faɗa min”.
Aƙage Sarki Youseep Mouleey ya kuma cewa.
“Shin wacece kakar ta ka?”.
Ahankali ya ɗaga yatsarsa tare da nuna musu hoton dake manne jikin bango kana yace.
“Gata can Kakata na rasa ya akayi nazo na samu hotonta acikin wannan Fadar taku”.
Cikin jin dadi Jabeer bin Jabeer yace.
“Aha bana faɗa mukuba, ai wlh dama na sani wannan daga gani babu tambaya Aliyu ne”.

Da sauri Didi dake kuka ta matso kusa dashi tare rungumesa.
Shi kuwa Moddibo shiru yayi, sai idanunsa daya lumshe yayin da lokaci ɗaya wani irin yalwataccen farin ciki ya lulluɓesa alokacin data rungumesa tsintar kansa yayi da ɗaura tafukansa abayanta ya rungumeta lokaci ɗaya kuwa yaji ruwan hawaye na cika masa idanunsa wanda bai san dalilin zuwan suba kawai dai yasan yanajin wannan matar da yaranta har cikin ƙahon zuciyarsa hakanan yakeji ya aminta da ita fiye da aminci da yayiwa ko wacce uwa a duniya.
Haka zalika rungumar da tayi masa ji yayi kamar Innayi ce ta ruggumeshi amman sai yakejin aminci da son fiye yadda yake ji tare da innayi wannan ruggumar jinsa yayi ruggumace ta mahaifiyar data ɗauki cikinsa tsawon wata tara da kwana tara ce ta kuma yi naƙudarsa so a matsayin uwa zuciyarsa da jininsa suka amshi rungumesa da tayi kamar yadda jikinsa zuciyarsa suka amshi Khadijah da Hafsat da Rahman a matsayin tsotsonshi muharamansa, sabida jini baya ɓuya.
Ji yake tamkar rungumar da yake nemane tsawon shekara da shekaru ne wanda bai samu ba.

Didi kuwa kuka ta saki hadda shesh-sheƙa batare data raba jikinsu ba tace.
“Abeey wallahi wannan ɗana ne. Abba wallahi ɗana ne ku gani taya za'a yi kuce sai kunyi wani bincike? ɗana ne Aliyuna ne fa Abba ɗana ne fa”.
Kalmar da take maimaitawa kenan tana cigaba da kuka.

Da sauri Sheikh Jabeer ya riƙo hannunta kana yace.
“Fatima kada kiyi kuka na gamsu na kuma yadda ɗan kine kuma tsatsonki ne nima ina ji ajikina tabbas tsatsonki ne kuma jikana”.
Ya ida maganar yana share mata hawayen daya ƙi tsayawa a idanunta.
Chapter 48 · 0% Book details