← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 150

Sashe 80

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Can kuma sai taji hucin ya bari, ajiyan zuciya ta fara sauƙe tare da yarfe zufar dake ɗiga mata tako ina, dai-dai lokacin kuma taji Unclee Naseer na kiranta tare da bubbuga mata kofar.
Cikin rawan jiki tazo ta buɗe ƙofar ganinshi yasa ta faɗa jikinshi tare da sakin kuka.
“Ah Baby lfy kuwa meya faru?”.
Cikin tsoro tace.
“Uncle Naseer ƙaton maciji fa na gani, a tsakiyar falonmu, inata kiranka baka ɗauka”.
Wani irin makirin murmushi Naseer yayi tare da cewa.
“Oh my god Baby dama dan wannan macijin ne kika rufe, kilata ihun nan, ihunki nefa ya dawo dani dan dana sauƙa ƙasan na tsaya ina ɗan waya da Kesi shiyasa ban fita da wuriba”.
Cikin tarin mmki tace.
“Dama kasan da macijin ne a cikin gidan?”.
Hannunta ya kawo suka fito falon, bisa kujera suka zauna yace.
“Na san dashi mana, ai shiyasa nace karki shiga ɗakinnan dan a ciki yake, kuma babu abinda zai miki kawai dai nasan, idan kika ganshi zaki firgitane, shiyasa nace kada ki shiga, amman babu abinda zai miki shi gadin gidan yakeyi, babu wani abin cutarwar da zai shigo muddin yananan, dan haka ki kwantar da hankali ki”.
Cikin ɗan sauran taradadi tace.
“Da gaske ba abinda zaimin?”.
Cike da yaudara yace.
“Shin bakiga bamu da mai gadi a gidanba?”.
Da sauri ta gyaɗa mishi kai.
“Toh ai dan nasan ibada wannan macijinne shiyasa ban wani nemi wani mai gadiba.
Kada kiji tsoro gaba ko ya fito, kada ki gudu babu abinda zai miki ko kan cinyarki ya hau, in Kinga ya fito dai yunwa ne yakeji, ni har gado ɗaya muna kwana dashi”. Cikin bashi dukkan yarda tace.
“Da gaske ba abinda zai min?”.
Cikin son samata yarda yace.
“Wallahi ba abinda zai miki ke dai ko jikinki yace zai hau ki barshi kada ki gudu”.
Daga nan yaci gaba da rubta tunaninta saida yaga ta ɗan nitsu kana ya sake fita.

Taraba Gembulan.
Hajia Lami ce zaune bakin gadon da Samira take kwance cikin toshe hanci tace.
“Ki tashi ki shirya muje asibiti, dan wannan wari ya fara yawa, ni kaina tsoron matsowa kusa dake nake”.
Cikin zubda hawayeba Samira tace.
“Uhmmm Momy kenan, amman kuma lokacin da nake cewa bazanje boka yayi lalata da nuba, kece kikayi ta ingizani kina turani harda nuna zakiyi fushi dani in banjeba, sai gashi yanzu kuma harda ke a cikin masu guduna sabida warin da nakeyi"...

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 23*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 08069423567 ko kuma ta wannan 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._

🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida.

Sai kuma ta fashe da kula mai cike da rauni, murya na rawa tace.
“Momy da kin kasancemun uwa ta gari da haka bai faru da niba, mun sake Allah mun kama boka baga masifar da ta biyo bayan kauce gaskiyaba, gashi yanzu munaji muna gani Modibbo ya auri Khausar, a lokacin da ahlinsa suka bayyana da irin matsayin da ko wacce mace zasayi fatan samu, duk da ni dai Allah ya sani ba kuɗi babu ba, naso Modibbo ne har raina sabida iliminshi da kyanshi”.
Cikin zuƙar warin da Samiran keyi Hajia Lami tace.
“Yanzu dai zaki tashi mu tafi asibitin ko sai kin gama zagina”.
Cikin sharce hawaye tace.
“Kiyi haƙuri Momy bazan zagekiba, wannan zunubin dana aikata ma ya isheni ba sai na ƙara wani ba na zagin mahaifiya, ki yafe min mutafi”.
Ta ƙare mgnar da miƙewa suka fita.

Marocco
A hankali ya fito daga falon nashi yana mai zuba wani irin fitinennen ƙamshi, tare da sheƙi da ƙellin fuska.
Ware manyan idanunsa yayi lokacin da yaji ƙaran wayar Khausar da ya ajiye bisa, dinnin table a hankali ya nufi kan Dinning area ɗin.

Ido ya zubawa fuskar wayar ganin.
*My happiness* a fuskar wayar ya sashi rumtse idanunsa da ƙarfi sabida jin.
Wani irin abu mai masifar ɗaci da maƙaƙi ya tokari maƙoshinsa.
Rumtse idanunsa ya kumayi kana ya buɗesu da sauri, hakanne da kuma ganin a saman lips inshi yace.
“My happiness”.
Waye?”.
Sai kuma ya sa hannunsa ya ɗauki wayar tare da juyawa da sauri ya nufi falonta.

Can ya hangota a bakin ƙofar corridor ɗin tanata kiciniyar buɗewa amman ta gaza gane ta yaya ne ake buɗe ƙofar.
Da sauri ta juyo jin alamun takun mutun, cikin sauri tayi kasa da kanta ganin wani irin kallon da yake liƙamata shi kuwa kanta ya nufa gadan-gadan ganin hakane yasa ta fara ja da baya da baya jin ta jingina da ƙofarne yasa ta buɗe idanunta.
Da sauri ta kuma rumtse idanunta ganin yadda ya matsota gab da gab, cikin wata irin muryar da shi kansa bai tantace ta meneba yace.
“Wayeshi”. Ya ƙare mgnar tare da nuna mata fuskar wayar,
sassayan numfashi ta fesar tare da miƙa hannunta alamun zata amshi wayar, cikin tsawa yace.
“Ce miki nayi ubanwaye ne shi, baki bani amsaba kike miƙo hannu zaki amsa”.
Cikin tura baki da sauƙe numfashi tace.
“Toh ni ka bani wayata mana, me ruwanka da masu kirana”.
Wani irin gigitaccen abune yaji ya soƙi ƙahon zuciyarsa, cikin juyewar yanayi ya danna mata wani irin gigitaccen tsawa tare da ceea.
“Wane ɗan iskanne shi da zai kira m...”
sai kuma yayi shiru ganin wani kiran ya kuma shigowa.
Ita kuwa Khausar wani irin numfashi tsoro taja tare da takure jikinta wuri ɗaya sabida ganin kamar marinta zaiyi.
Amsa kiran yayi tare da liƙa wayar a kunnensa ba tare da yace komai ba.

Wani irin ɓoyeyen ajiyan zuciya mai nauyi ya fesar jin murya Mommy Khausar ce, cikin nitsuwa kamala kawaici hadi da girmamawa yace.
“Wa alaikassalam”.
Cikin sanyi Mommyn ta fesar da numfashi dan ta gane muryarshi.
“Mommy ina kwana?”. Ya kuma cewa jin tayi shiru.
Ita kuwa Mommy cikin girmama kai tace.
“Lfy lau Moddibo ya gida”.
Wani irin amintaccen numfashi ya kuma fesarwa tare da sa hannunshi ya kamo hannun Khausar ɗin kan ya juya da ita suka nufi falonta yana mai cewa.
“Alhamdullah Mommy yasu Raudat”.
Chapter 80 · 0% Book details