← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 150

Sashe 35

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sake baki Asma'u tayi cikin Mamaki tace.
“Tabb Ummi ai kusan Auren Dodo da mutum za ayi dan wallahi Khausar matsayin Dodo take kallon Yah Moddibo”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauke kana tace.
“Aikuwa da saninta”.
Zare ido Asma'u tayi tamkar zasu zubo tace.
“Ummi Khausar ɗin ta sani?”.
Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.
“Eh”.
Dafe ƙirji Asma'u tayi Idanunta akan Ummi tace.
“Shine kuma bata faɗa min ba iyeee Kam bala'i bari Inje in sameta”.
Ta Ida maganar tare da miƙewa.

Cikin sauri Ummi ta riko tsintsiyar hannunta tace.
“Zauna ai zuwa ta ƙarshe naji tana cewa tazo kuyi wata magana kuma ta samu kuna aiki sannan fitowar ku kenan taga Moddibo yazo kinga ai jikinta na rawa ta fita”.
Jinjina kai Asma'u tayi still Hannunta na cikin na Ummi tace.
“Eh dan na kirata awaya ma nace ta faɗa min shine tace idan inaso Inje gidansu inji labari ashe dama wannan ne maganar amma Ummi tasan maganar kuma ta yarda?”.
Cikin sanyi Ummi tace.
“Eh ta sani ta yarda kuma ta amince”.
Dafe kunci Asma'u tayi kana tace.
“To amma Ummi garin ya akayi haka?”.
Kallonta Ummi tayi tare da gyara zamanta kana ta sauƙe numfashi cikin sanyi tace.
“Wasiyyar Yayanki zata cika?”.
Cikin sauri Asma'u ta kalleta fuskarta ɗauke da mamaki tace.
“Wasiyya kuma Ummi ya bar mata?”.
Jinjina kai Ummi tayi tare da fesar da numfashi kana ta jingina bayanta da jikin kushin ɗin tace.
“Idan baki manta ba Ranan da yazo gidan nan na ƙarshe itama Khausar tazo sannan tare suka tafi”.
Cikin sauri Asma'u ta jinjina kanta kana tace.
“Ƙwarai kuwa Mommy na tuna aishine tace suna tafiya taga wata mota na binsu”.
Kai Mommy ta Jinjina kana tace.
“To awannan ranan ne ya bar mata wasiyar. Mommy ta ke sanar min yanda suka yi”.
Jinjina kai Asma'u tayi cike da tausayawa Aminiyar tasan yanda Khausar ke masifar tsoron Moddibo tabbas ta ɗauki al'ƙawari mai girma cikin sanyin murya tace.
“Allah sarki Khausar!, Allah sarki Aminiya!!, Ubangiji Allah yabar ƙauna Allah yabar ƙauna tsakaninta da Yah Moddibo”.
Sai kuma ta kalli Ummi da fuskarta ke ɗauke da murmushi tace.
“Ummi inshirya inje”.
Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.
“Kije mana Asma'u wa zai hana ki zuwa wajen Aminiyarki”.
Cikin sauri Asma'u ta miƙe tashiga Bedroom ta sanya hijabinta kana ta fito tayiwa Ummi Sallama.

Aɓangaren Hajiya Lami kuwa miƙewa tayi daga Bedroom ɗinta ta nufi ɗakin Samira zaune ta sameta Idanunta sun kaɗa sunyi jawur tamkar garwashi alamar tasha kuka sosai cikin sauri ta ƙarasa kana ta zauna gefenta cike da kulawa tace.
“Samira wai lafiya yau baki fito ba meya faru?”.
Ahankali ta ɗago kanta Idanunta da suka sauya launi ta kalleta Muryanta na rawa tace.
“Mommy ni baƙi ɗaya wari nake ji idan na tambaye ki kinajin wani sai kice min bakya ji Mommy kullum warin nan ƙaruwa yake ya zanyi da raina”.
Cike da tausayawa Hajiya Lami ta janyota jikinta cikin sanyin murya tace.
“Haba Samira ki kwantar da hankalin ki mana idan ya dawo sai mu sake komawa wajensa”.
Cikin raunin murya tace.
“Mommy wani irin in ya dawo zaku koma wajensa ni dai ina ganin mutumin nan ya lalata min rayuwa ne yanzu ayanda nake warin nan ko maigadin gidansu Modibbo ma zai yarda ya aurenki ne bare Modibbo da ɗan karen tsabta”.
Sai kuma sharce hawaye masu masifar zafi kana tace.
“Yanzu Mommy wani namiji ne zai kalleni bare yace yana sona! ga ruwa mai wari da ƙarni yana ta bina ko yaushe ina tare da ƙunzugu kamar mai jego”
Cikin sanyi Hajiya Lami tace.
“Bakomai Samira kasa ki damu Insha Allah yana dawowa zamu koma wajensa”.
Cikin muryan kuka da tashin hankali tace.
“Mommy Ni dai ina ji ajikina wannan al'amari ya zama min bala'i arayuwata na saɓi Ubangiji gashi ya kamani tun ba aje ko ina ba Wayyo Allah! Kaico na! Ni Samira”.

Asanyaye Hajiya Lami tace.
“Haba Samira kar ki karyar min da zuciyata mana Insha Allah burinki zai ciki”.
Kai ta girgiza kana tace.
“Mommy ni kam hankalina bai kwanta ba burina inga na samu lafiya wannan ruwan ya daina zuba shine kwanciyar hankalina”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da dafa shoulder ta tace.
“Kada ki damu Insha Allah Samira Zaki samu sauƙi”.
Jinjina kai tayi kana tace.
“Allah yasa Mommy Ina fatan hakan Allah na tuba Allah kayafemin Allah kaji ƙaina ka gafarta min”.

Acan ɓangaren Lamiɗo kuwa bayan ya fita ɗakin Mommy Kai tsaye sashen Gimbiya Dadu yashiga bakinsa ɗauke da sallama zaune ya ganta da ƙanwarta Hajiya Kubra.
Anutse ya ƙarasa tare da zama kana da murmushi afuskarsa yace.
“A Yafendo Kubra kin zo ne?”.
Kai ta gyaɗa tace.
“Eh Lamiɗo kana gida kenan?”.
Kai jinjina kana suka gaisa bayan sun gaisa Hajiya Kubra ta gyara zamanta tare da kallon sa tace.
“Toh yau dai kam nazo da aiken Ƙaninka duk da yace min iyayenshi maza sunzo”.
“Wanne ƙarin nawa”. Yayi tambayar a bauɗo domin babu wanda ya taɓa mishi mgnar.
Shi kanshi mahaifin Naseru cewa yayi yaji suna mgnar ne bakwai sun gaya mishi bane, to kuma shima sai abin ya kwanta mishi musamman da yasan Nasiru na biye-biyen mata shiyasa ya nemi alfarma a bashi Amina kuma ayi auren cikin gaggawa.

Murmushi tayi tare da Kallonsa tace.
“Naseeru mana”.

Kai ya jinjina kana yace.
“Ikon Allah Naseeru kuma ko ɗazun ma muna tare kuma bai faɗa min ba shine sai ya aiko ki? ai da kin kirani ma zanzo har gida in sameki”.

Kai ta girgiza kana ta kalli Gimbiya Dadu sai kuma ta kalli Lamiɗo tace.
“A'a ai aiken ne dole muzo da kan mu tunda iri muke nema”.
Jim yayi kana yace.
“Ikon Allah wani kalar iri kenan?”.
Ƴar dariya tayi ta gyara zamanta kana tace.
“Iyeee al'amarin ne ya sauya sheƙa”.

Gyara zama Gimbiya Dadu tayi kana tace.
“Eh aihakama shi yafi alkhairi Hausawa sunce naka sai naka daɗin zama sai bare gwara dai kome za ayi ace na kane” .
Ido kawai Lamiɗo ya zuba musu cikin rashin fahimta ko kaɗan bai taɓa fuskantar alaƙar dake tsakanin Amina da Naseer.
Ganin yanda yake kallon Hajiya Kubra tayi murmushi tayi kana tace.
“Akan al'amarin Naseeru ne da Amina”.
Cikin sauri ya kalleta ya girgiza kai kana yace.
“Ba dai Amina da Naseeru ba saidai Nasseru da Khausar dai ko?”.
Dariya tayi tare da gyara dankwalinta tace.
“A'a da Aminar dai”.
Ido ya zuba mata cike da son nazartansu yace.
“Da Amina dai?”.
Jinjina kai tayi ta kalli Gimbiya Dadu kana tace.
“Tabbas da Amina”.
Jingina Lamiɗo yayi da jikin kujeran kana yace.
“A'a baki fahimci maganarsa da kyau ba da Khausar ce kuma al'amarin ma dai gashi nan yanda yazo abirkice”.
Fuska Gimbiya Dadu ta ɓata kana tace.
“Babu abinda ya birkice sai dai sune ya birkice musu acan tunda Khausar ta nuna bata sonsa ai Alhamdulillah ga ƴar Uwarsa ta soshi”.
Cike da Mamaki Lamiɗo ya ɗago kansa ya kalleta yace.
“Da ita Aminar kenan?”.
Jinjina kai Hajiya Kubura tayi kana tace.
“Eh ai Amina da Nasseru sun daɗe da haɗa kansu soyayya suke sosai basu dai fito sun faɗa maka bane suna so sai angama shirya abubuwa komai ya kankama”.
Jinjina kai Lamiɗo yayi still da mamaki atare dashi yace.
“Allah mai iko shi kuma Naseeru ƴarsa zai Aura?”.
Cikin sauri Gimbiya Dadu ta katsesa da cewa.
“Ya haramta ne?”.
Murmushi yayi tare da girgiza kai yace.
“A'a a'a bai haramta ba na isa in haramta abinda Allah ya halatta ba wai ya haramta bane amma da yake tana sunan ƴarshi ce”.
Baki Gimbiya Dadu ta taɓe kana tace.
“To wannan dai ba wani abu bane aciki ka dai kayi fatan alkhairi Allah yasanya albarka acikin al'amarin”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Kuma haka abin ya zama kenan?”.
Kallonsa Gimbiya Dadu tayi kana ta kalli Hajiya Kubura dake murmushi tace.
“Sosai ma tunda naji Kakar Khausar tana cewa ba zata bawa Zuri'ar Mayu ba tana ƙananun surutai shiyasa nace ya janye da nemanta ya nemi Amina ƴar Uwarsa shiyafi mana kwanciyar hankali”.
Ahankali Lamiɗo ya sunkuyar da kansa ƙasa batare da yace Uffan ba.
Dariya Hajiya Kubrua tayi kana tace.
“Ai shiyasa nace bari nazo da kaina muyi magana”.
Anutse ya ɗago kansa ya kalleta ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Toh Yafendo Kubura ai wannan al'amarin Aure magana ce ta maza bata mata ba ai da Babban Naseeru ne zaizo muyi magana zai fiko sai insamu gamsuwa da sahalewar sa za ayi dukkan maganar?”.
Cikin sauri Gimbiya Dadu ta katsesa da cewa.
“Ai zaizo amma dai ta fara zuwane ta sanar maka saboda bakasan da Maganar ba”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Toh shikenan Ubangiji Allah ya mana zaɓin alkhairi”.
Gimbiya Dadu kuwa cikin sauri ta tari numfashi ta hanyar cewa.
“Shine ma alkhairi Nasseru ya auri ƴar uwarsa ita kuma taje can ta ƙarara ta auri duk wanda taga dama da masifaffiyar Kakarta”.
Murmushi yayi kana yace.
“To Allah ya kyauta”.
Chapter 35 · 0% Book details