Sashe 84
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri Didi ta ɗago kanta tare da zuba mishi ido.
Shi kuwa Modibbo cikin wani irin sanyin jiki gami da rauni da raɗaɗin ciwon mutuwar J ɗinsa, da kuma raunin ɗa idan ya kasance gaban mahaifiyarsa, ya isa gareta, tare da direwa bisa guiwowinsa cikin yanayin da bazai iya jumrewa ba, ya kife kanshi bisa cinyoyinta tare da saki wani irin maraitaccen kukunda yasa.
Zuciyar Didi wani irin gigitaccen bugawa, yayinda Lalla Khadijah kuwa da sauri ta dawo gareshi.
Tana mai zama gefenshi.
Cikin yanayin tsoro Didi ta buɗe baki a hankali tacewa Dr Jameel.
“Jameel meya sameshi?”.
Da sauri Dr Jameel ya zauna gefen Didi ganin alamu ta shiga ɗimuwa yace.
“A'a fa Didi babu abinda ya sameshi, maganar wasiyar da Amininshi Jameel mai kama da ni, ya bar mishine ya sashi cikin wannan yanayin".
Wani nannauyan ajiyan zuciya Didi ta sauƙe sai kuma ta daura hannunta bisa kanshi tana ɗan shafawa tare da sa ɗaya hannun kuma tana ɗan bubbuga bayanshi, cike da tsananin tausayinshi da kuma raunin da yasa itama ta fara zubda hawaye.
Lalla Khadijah kuwa a hankali ta sauƙe numfashi kana ta koma gefe ta zauna.
Lalla Hafsat da Khausar da yanzu suka fito ne, cikin sauri Lalla Hafsat ta matso kusa dashi cikin sanyi tace.
“Kayi haƙuri Aliy... Sai kuma tayi shiru ganin Didi ta ɗaga mata hannun kana tayi mata alamun da ta barshi yayi kuka, domin yin kukan zaisa yaji sanyi.
Ita kuwa Khausar cikin wani irin yanayi mai cike da rauni ta zauna tare da rumtse idanunta.
Rahman dake zaune gefen Khausar dake kusa da Lalla Hafsat kuwa sai yanzu ta dire numfashin dake bayyana tsoron data shiga.
Ita kuwa Khausar a hankali ta buɗe idanunta, wani irin kallo take bin Modibbo dashi wanda yake tafe da tsananin tausayi rauni jinƙai domin itace kaɗai tasan irin aminci da shaƙuwar dake tsakanin Yah Jameel din da kuma Modibbo.
Ganin yadda yake wani irin kukanda ke gab da ficewa da numfashin sane yasata jin wasu irin tagwayen hawaye masu masifar zafina kwaranyo mata tamkar an ɓalle bakin pampo.
Da sauri Lalla Khadijah ta dawo kusa ita tare da sa hannun ta fara sharce mata hawayen da ta sharcesu wasu zasu meye gurminsu.
Didi kuwa kallon Khausar ɗin take cike da so da ƙauna sai kuma ta lumshe idanunta tare, da jingina kanta jikin kujerar.
Zuwa yanzu Khausar kam itama kukan ya subce mata, sosai ya taho mata da Shesh-sheƙan mai danne numfashin, wanda hakane yasa Didi yin guntun murmushi tare da yiwa Lalla Hafsat alamun ta ɗauki Khausar su shiga ɗakinta.
Haka yasa Lalla Hafsat tallabe Khausar tare da janta suka, shiga ɗakin Didi mai cike da ƙawa na al'farmar, bakin gado ta ajiyeta, tare da buɗe fridge ta dauko goran ruwa mai sanyi ta ɓalle marfin kana tasa matashi a baki wanda dole yasa tasha.
Shan ruwan ne yasa ƙarfin kukan nata raguwa sai dai Shesh-sheƙan dake fitowa daga ƙahon zuciyarta, cikin sanyin jiki Lalla Hafsat ta jawota ta jinginata da jikinta kana a hankali ta fara mgna.
“Kiyi hakuri Khausar ki daure ki koyawa zuciyarki dauriya, tunda kinga mijinki mutum ne da wasu mahimman abubuwan ke sashi kasancewa mai rauni, to dole ke ki kasance jaruwa ki iya kwantar mishi da hankali da tausarsa, a duk sanda kika ga ya kasance cikin irin wannan yanayi, ba kuka zakiyiba, lallai ne da wuya mu mata buga mazanmu cikin damuwa mu iya hana kanmu kuka, toh amman tunda kinga a duk sanda akayi mgnar Jameel ko tunanin Jameel ya dawo zuciyar mijinki yana ɗimaucewa da raunata, Please na roƙeki ki daure kike hana kanki kuka, nasan ciwon da kikeji a zuciyarki domin babu abinda ke raunata mace kamar kukan mutum hudu miji, uba, ɗan uwa yaya ko Kani da kuma ɗanka, musamman in sun girma domin muddin kaga namiji na kuka tofa abin babbane, amman duk da haka ki koyi kontar mishi da hankali, dan na lura in ba haka ya samuba zai iya kamuwa da cutar damuwa”.
Ta ƙare mgnar da cikekken yaƙinin ganin tsananin tausayin mai jagorantar so da Khausar keyiwa ɗan uwan nata.
Ita kuwa Khausar cikin raunatacciyar murya tace.
“Aunty Hafsat tausayinshi nakeji, komaifa na rayuwar Duniya da Yah Jameel yakeyi, ko abinci baya iya ci sai da Yah Jameel, tunda nake tare dasu a rayuwata sau biyu na taba ganinsu ba a tareba, ranar da nayi rabuwa ta karshe da Yah Jameel, da kuma wata rana da naje wurin Ummi shi ya maidani nan ma yaje neman Yah Jameel din ne.
Aunty Hafsat shifa baida wani aboki a duniya sama da Yah Jameel komai tare sukeyi”.
Sai kuma ta fashe da kuka.
Hakane yasa Lalla Hafsat ƙara ruggumeta.
A can falon kuwa kusan tsawon 21 minutes Modibbo yayi yana kuka mai ciwo a rai.
Kana a hankali ya ɗago kansa ya kalli Didi dake zubda hawaye, cikin rauni yace.
“Didi J ya tafi ya barni a lokutan da zanfi buƙatarsa, Didi J fa, shine mutumin da duk abinda yasan inaso in dai yana da damar mallaka minshi koda rasa abin zai iya zame mishi ajali yakan sadaukar min dashi.
Didi J fa shine yayi min zaɓin matar aure, ya kuma tabbar da yayi dukkan abinda zai ta yadda gashi har bayan ransa saida abin ya tabbata, Didi J fa shine mutum ɗaya a duniya yake gane dukkan gaskiyar dake zuciyata da motsin jiki a koda na ɓoye abin, Didi J shike riganin sanin abinda nakeso ni kaina.
Didi akan zaɓin da J yayi minfa iyayenta ke bani Amana, Didi ta yaya zan iya cin zarafi da gaza ankilta zaɓin J na? Didi zato suke inada muguwar zuciyar da zan iya wofintar da zaɓin J ne. Didi ki gaya musu me sukeso inyi a duniya da zai nuna musu halaccin da zanyiwa zaɓin da J na yayi min Didi J fa ya gane wacece ita a ƙasan zuciyata duk da kafiya da nacin da nayi wurin ɓoyewa saida ya gane shi yasa ya zaɓa min ita”.
Zuwa yanzu kusan duk hawaye suke zubdawa.
Didi kuwa a hankali tace.
“Ba kai kadaiba Aliyu dani da ahlinka duk zamu tayaka ankiltawa da kyautawa zaɓin J dinka kuma zamu kasance masuyi mishi Addu'o'i a cikin dukkan sallolinmu."
Sai kuma tasa hannunta duka biyu ta tallabe habarshi da yayi zafi jau.
tare da share mishi hawayen da wasu ke korar wasu kana taci gaba da cewa.
“Kayi haƙuri Babana amanarsu bazata gareka riƙewaba tunda sirrin zuciyar kace da J ɗinka ya gane”.
Kanshi ya kuma jifewa yana mai ci gaba da kukan.
Jin an kira sallan azabtar ne yasa tai ta kara bashi karfin guiwar tare dasa Dr Jameel ya kama hannunshi suka tafi.
Kana su kuma duk sukayi al'wala.
Zakariyya ma dake tare da Asiya a falon ƙasa jin kiran sallame yasa ya ɗan kalleta cikin salon so yace.
“Baby bari muje muyi salla, kafin mu dawo kun gama shiri sai mu fita ko”.
Cikin kunya da kuma so haɗin da jin daɗi Asiya ta kali santalelen Balarabe da Allah yayi mata zaɓi dashi duk da hantarar data sha na rashi miji a wurin uwarta taki yarda aje wurin boka gashi Allah ya mata zaɓi, cikin nitsuwa tace.
“Toh ayi mana addu'a”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Me kikeso in roƙa mana?”.
Murmushi tayi tare dasa tafin hannuntan ta rufe fuskarta kana tace.
“Twince muke so”.
Wani irin murmushi mai cike da jin daɗi Zakariyya yayi domin wannan kalmar kaɗai ta isheshi gamsuwa Asiya ta yarda dashi, sai kuma ya bita da ido ganin ta juya ta tafi da sassarfa.
Ibraahim ya kira kana suka tafi masallaci.
A can side ɗin Didi kuwa cikin sanyi Khausar ta juyo ta kalli Lalla Hafsat dake gefenta bayan sun isar da sallan murya a tausashe tace.
“Aunty Hafsat kijifa a cikin sallama kuka yakeyi har aka idar da sallan baibar kukaba”.
Cikin sanyi Aunty Hafsat tace.
“Wlh naji Khausar ni kaina bansan sanda naita zubdawaye ba”.
Ita kuwa Khausar kife kanta tayi a gefen kujerar da take zauna a gabanta tana mai sassayan kuka.
Ita kuwa Hafsat ɗakin da Didi ta shiga ta nufa.
Bayan an isar da sallan kuwa Modibbo gyara zamanshi yayi cikin masallacin tare da fara karatun qura'an.
Ganin hakane yasa su Dr Jameel da Zakariyya kuwa fitowa suka nufi cikin gida.
Bayan daworsu ba ɗaɗe su Ummi suka fito.
Ummi da Hajia Bunayyah na bayan motar Dr Jameel, Asmau kuwa a gaba ta zauna gefenshi.
Hajja Umma da Aunty Rukayya kuma a motar Ibrahim, sai kuma Aunty Hajara dake gaba gefenshi.
Dan Hajja Nana da innayi sunce su bazasu jeba.
Asiya kuwa motar Zakariyya ta shiga, gaba kusa dashi sai kuma Haiydar da Hakim dake baya.
Sai su Abban kuwa da Abualeey yasa amintattun hadimansa suka fita dasu cikin motoci na al'farmar.
Su maza wuraren tarihin kasar aka kakkaisu da abinda ya shafi masarautar.
Su Dr Jameel kuwa kai tsaye The exotic bouknadel garden Rabat suka wuce.
Abujan Nigeria
Tun bayan da Unclee Naseer ɗin ya sake fita, Amina ta komai cikin bedroom bata sake fitowa falonba, sai bayan sallam azahar wanda ita ba sallan tayiba.
A hankali ta fito saɗab-saɗab tana ɗan lelleƙawa tare da jujjuya ido.
Shiru ba komai falon, wanda hakanne yasa ta kunna TV tashar MBC Max kana ta zauna bisa kujera tare da maida hankalinta kan Film ɗin da akeyi.
Dai-dai lokacin kuma Unclee Naseer ke zaune cikin tsakiyar taron abokansa ƴan mafiya, da suka zagayeshi da jan ƙyalle suna surutai haɗin da surkulei suna watsa mishi wani irin ruwa, bisa alamun dai gashi nan zaune a tsakiyarsu amman ruhinsa bai wurinsu.
Babban cikinsune wanda ya fisu mummunar shiga yake mgna kamar cikin raɗa da bada izini yake faɗin.
“Kayi maza ka juya, ka bayyana gareta, kana sane yau kwananku takwas da aure wanda tun daren forkonku akeso ka fara zuƙo mana jininta amman ka tsaya nawa, yanzu dai kwana biyu ya rage maka ka fara kawo mana jininta in kuwa ka bari ka cika kwana goma baka kawoba toh aikinka ya ɓaci”. Sai kuma duk suka fara surutai da watsa mishi ruwan