Sashe 113
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Morocco*
Yau kwanan Khausar hamsin Cif da tarewarta sashen Moddibo bayan sallar Asbah Khausar ce zaune a bedroom ɗin Moddibo tun da ita idar da Sallar Asbah bata motsa ba tana kan sallayar yayinda gaba ɗaya jikinta ke a saluɓe kasalar data zame mata abokin rayuwa a jiya da yau ta tsananta mata wata ƙil hakan baya rasa nasaba da rashin cin abinci wanda ta kai kwana biyar sai ruwa tea da fruits domin abin ƙaruwa yakeyi.
Bayan Moddibo ya dawo daga Masallaci kai tsaye bedroom ɗin sa ya wuce ganinta zaune kan sallaya yasa ya nufeta tare da zama gefenta ya zuba mata ido gaba ɗaya ta rame ta ɗanyi fiyau sai wani irin fari mai kamar yellow da tayi wanda har jijiyoyin jinin jikinta suka ɗanyi kore kaɗan suka bayyana.
Ganin kamar azkar takeyi ne yasa shina ya janyo Alkur'aninsa dake kan Starm.
Cikin lumshe idanu da nutsuwa yayi A'uziyyah kana ya fara karatu cikin Suratul Ibrahim daga forko.
Yayinda ita kuma taci gaba da yin azkar ɗinta bayan ta gamane ta shafe jikinta da addu'ar kana a hankali ta ɗan yunƙuro ta matso kusa dashi a dai-dai lokacin kuma yazo aya ta (39)a hankali ya ɗan juyo ya kalleta tare dasa hannunshi ya kamo nata, cikin sanyayyar muryansa yaci gaba da karantun kamar haka.
_“Alhamdulillaziy wahabli alalkibri Isma'iyla Wa Ishaƙ,Inna rabbi lasami,Uddu',a.”_
Sai kuma ya janyota jikinshi a hankali ya rungumeta,
Ita kuwa Khausar cikin kasala ta daura kanta akan kafaɗarsa hannunta ɗaya na bisa ƙirjinsa idanunta na kan Alkur'anin tana mai jin zazzaƙan sautin muryarsa.
Shi kuwa Modibbo hannunsa na dama na kan Kur'anin na hagu kuma na rungumeta da ita yana cigaba da karatun,
A hankali ta kuma manna kanta da ƙirjinsa sai kuwa ta lumshe Idanunta jin yana karanto aya ta(40) yanda sautin karatun ke ratsa dodon kunnenta yasa itama buɗe bakinta muryarta a sanyaye a hankali ta fara binshi suna karatun a tare sai dai muryarshi ya ɗanfi nata fita a jere suke karanta harufan ayata 40.
_“Rabbij Alniy Muƙiymassalati wamin zuriyyatie.Rabbana wataƙabbwl du'aaa”_.
Cikin lumshe idanu da sauƙe numfashi ta kuna zamewa ta kwanta kan cinyarsa tana fuskantar qura'an ɗin sabida duk yadda tayi bata jin daɗin jikinta ga azabar yunwa da kasala ga alamun zazzaɓin da take ji,
Shi kuwa Modibbo still dai yana karatu ya ɗaura hannunsa aƙugunta yana shafawa yana cigaba da lumshe idanunsa yayinda ita kuwa Khausar tayi lamo a jikinsa, sai kuma ta miƙe zaune tana ɗan fuskantarsa, cikin sanyi ya ɗaura bayan tafin hannunshi bisa kuncinta na dama yana ɗan shafa har lau kuma idanunsa na kan qura'an ɗin.
Cikin narkewan jiki ta langwaɓar da kai tare da ƙara matsoshi sosai ganin haka ne, yasashi sa hannun tare da ɗan tura katakon da Qura'an yake a kai, kana ya jawo ta ya rungumeta tsam a jikinshi da hannunsa duka biyu a hankali yake ɗan shafa bayanta da hannunsa na dama da yake saman na hagun alamun yana son ta samu nitsuwane yasa yaci gaba da karatun cikin zazzaƙan muryansa ya ɗauko ayata (41) kamar haka.
_“Rabbanagfirliyy,Walilwalidiyya Walilmu'uminiyna Yauma Yaƙuumulhisab”_.
Ahankali ta ƙara rungumesa tare da ɗan ɗago kanta ta kalleshi idanu cike da alamun hawaye sai kuma ta sauƙe numfashi mai zafi, wanda yake sauka acikin kunnensa.
ba tare daya kai ƙarshen Surar ba kasancewar yazo ƙarshen Ayar ya rufe Kur'anin tare da gyara mishi zama kana ya janyota jikinsa ya rungumeta da kyau yana goga sashen sa afuskarta ya motsa laɓɓansa tare da cewa.
“Ya dai?”.
Ahankali tayi miƙa tare da lumshe idanunta wani irin kasala da yunwa takeji baki ɗaya jikinta yayi nauyi ba tada kuzari ko kaɗan zuwa yanzu ta gama fahimtar baki ɗaya yanayinta ya canza ta rasa meyesa meta cikin sanyi ta girgiza masa kai tare da cewa..
“Ban sani ba”.
Yayin da idanunta suka canza launi saboda yanayin da take ciki.
Sake jawota jikinsa yayi kanaya cusa kansa tsakanin wuyanta muryansa can ƙasa cike da kasala yace.
“Minha yau baki da lfy me yake damunki ne?”.
Kai ta girgiza tare da cewa.
“A'a nima ban sani ba fa?”.
Cikin rauni, kulawa, tausayi, gami da jinƙai da damuwar yadda yaga yauɗin gaba ɗaya ta sake yace.
“Minha Vidaa yunwa cefa take son lahanta min ke”.
Bai jira jin abinda zata ce ba ya mike tare da ɗaukarta cak a jikinsa, batayi musu ba, sabida bata da ƙarfi a hankali ta lumshe udanunta ganin side ɗin Didi ya nufa da ita.
Da sauri Didi dake tsaye a dinning area ta zuba mishi ido cike da tsoron da yasa jikinta mutuwa tace.
“Aliyu lafiya kuwa”.
Ta ƙare maganar tana nufi tsakiyar falon ganin ya kwantar da ita bisa kujera murya cike da damuwa yace.
"Didi yau kusan kwana biyar bataci abinciba yau kuma kinga duk ta sake na rasa meke damunta Didi”.
Ya ƙare maganar yana zama gefenta, ita kuwa Didi da sauri ta koma dinning ta haɗa tea mai zafi kana ta dawo,
Cup ɗin ta miƙa shi tare da cewa.
“Gashi bata”. Da sauri ya tallabota ya zaunar da ita tare da amsar cup ɗin yasa mata a baki, ba musu ta kafa kanta ta fara sha saida ta shanye a janye cup ɗin dai-dai lokacin kuma Innayi ta shigo da sauri ta ƙaraso gabanta kusan a tare suke mata sannu ganin wani irin zufa daya keyi mata.
Ita kuwa Khausar cikin wani irin gigitaccen yunƙurin amai daya taso nata, ta damƙi hannun Modibbo tare da niyar miƙewa wanda tuni ta fara kakari da sauri Didi ta maida ita zaune, shi kuma ya tallabota.
Aiko nan take ta fara zuga.....
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 32*
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
*Masu son Maganin infection da maganin mata, ku marmatso wannan account no in ne naku ta ciki zaku turo kuɗin ku 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, Sai ki turo shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 08069423567. akwai sabbin kaya masu zafi suna nan bisa hanya, ki turo kuɗinki a saki cikin lissafi. Kayanen mata masu zafi sadidan daga Chadi akwaisu Garukan daka, gumbunan, Tsumummuka, cida Ciccibi Abodi cida kaza ci da jan nama kwanon ƙasaitacciyar mace biyar sirri, furar mata, gumbar madara Gumbar kolli mai ƙyallin al'khairi gumbar uku al'khairi, gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, gumbar riɗi, garin maɗi garin melɗamhi garin ilanwaddihi garin mallaka, tsumin riɗi tsumin tsirtai tsumin kinfi budurwa, tsumin riɗi, tsumin ta baje Sabaya, matsin maliƙi mai masifar matse mace matsin daɗi har maɗiga, mai ɗan kare kyau. Kullacar sirri al'ajabu shu'umar Humra, da duk sauran kan ƙamshi. Haɗin amarya budurwa ko bazawara haɗin mai jego ko uwar gida, akwaisu Available set ɗinmu hawa hawane akwai manya akwai ƙananan, ƙanan daga 40k ne 35k 30k 25k 20k 15k 10k shine ƙarami haɗina na karshe sai kuma haɗin kwanon ƙasaitacciyar shi 7k ne shine ƙarshen haɗina kenan... Manyan set ɗin kuma daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k ke zaki faɗi haɗin nawa kikeso anyi miki kana kimin bayanin yadda kikeso da matsalarki ni kuwa nasan abinda zan haɗa miki, ina araha kam amman ina hana bashi*
Amai kamar ba gobe, wasa wasa dai amai yaƙi tsaya, ganin hakane gaba ɗaya Modibbo ya birkice kawai sai ya rungumeta a jikinshi tanata kakarin wanda ba abinda take hararwa sai miyau da ɗan ruwa kaɗan sabida ba abinda taci shiyasa gaba ɗaya ta galabaita.
Cikin sauri Didi ta shiga ɗakinta alƙyabbata ta sako kana ta dawo tare da cewa maza.
“Maza ɗauketa mu tafi asibiti”.
Cikin ruwan jiki ya ɗauketa suka fito harabar side din Didi suna fita hadimai na buɗe musu mita Didi da Innayi mota ɗaya suka shiga shi kuma mota ɗaya da Rahama da tazo shigowa ne ta gansu.
Kai tsaye Mouldy hospital suka nufa.
Wanda tuni Didi ta gayawa Abualeey da kanshi ya gayawa Dr Jameel shiyasa tun kafin su isa an shirya komai.
Suna isa aka amsheta tare da bata taimakon gaggawa wani ɗan karamin ruwa suka ɗaura mata da allurai kana suka nufi ɗakin gwaje-gwaje da ita.
Wanda duk inda sukayi Modibbo na biye dasu a baya.
Cikin iyawa da ƙorewa Dr Isha ke ɗan jujjuya na'urar dake saman cikin Khausar yayinda Dr Jameel kuwa yana ɗaya gefen yana haɗa ruwan allura.
Cikin murmushin Dr Isha ta kalli Modibbo fuska cike da jin daɗi tace.
“Alhamadullah Mrs Aliyu Youssef Mouldy nada ciki na tsawon kwanaki arba'in da biyar”.
Ya Salam shine abinda Modibbo yayi ya faɗi a fili da kuma ƙarfi sai kuma ya juya da sauri ya fuskanci alƙibla yayi sujudushukur, yana ɗagawo kuma ya dawo bakin gadon da sauri ya yasa hannunsa da nufin zai ɗagota sai kuma ya kalli Dr Jameel da ya riƙe hannunsa tare da cewa.
“Malam barta bakaga bacci tayiba”.
Kawai sai sunkuyo kanta bisa goshinta ya sakar mata amintaccen kiss sai kuma a kunatu daga nan sai haɓarta kawai sai ya rinƙa bin duk jikinta da sumbatar dake nuni da tsananin farin cikine ya gigita shi, ita kuwa Khausar bacci takeyi cike da wahala.
Ganin alamun Modibbo zai takura tane yasa Dr Isha cewa.
“Afwan a barta tai vacci”
Jin hakane yasa ya juya da sauri ya fita.
Yana fitowa ya nufi Didi itama ɗin shi ta nufa, yana isa inda take kawai sai ya rungumeta cikin tsananin farin ciki jin daɗin mara musaltuwa na yadda labarin yazo mishi a bazata yace.
“Didi Minha vidaa nada ciki Didi ciki nanefa a jikin Khausar Didi ɗa nane a jikinta fa”.
Cikin tsananin jin daɗi Didi da dama ta daɗe da fahimtar cikine da Khausar kanshi ta fara shafawa tana cewa.
“Kayi sujja ka godewa Allah”.
Da sauri yace.
“Didi nayi”.
Sai kuma ya saki Didi ya kama Innayi da yanzu ta ɗago kanta daga yin sujjadar godiya ga Allah ruggemeta yayi yana cewa.
“Innayi kinji ko?”.
Kai ta gyaɗa mishi dan da alamu yama rasa me zauce.
Sai kuma ya kamo hannun Rahama dake rawa da juyi da waya a kunneta da alamun Lalla Khadijah take gaya cikin jin daɗin yace.
“Kinji kin kusa zama Goggo ko”
Sai ta ruggumeshi.
Kan kace kobo Abualeey da Waziri Galadima da Niyna suna sunzo.
Haka dai ranar suka wuni a asibiti wanda ita kam Khausar batama san meke faruwa ba dan bacci ta wuni.