Sashe 65
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Acan falon da aka sauƙe su Khausar kuwa cikin gigita Asma'u ta shiga falon tare da faɗawa kan Ummi dake zaune cikin ficewar hayyaci take faɗin.
“Wallahi Ummi naga Yah Jameel”.
Da sauri Ummi ta zaro ido kana tace.
“Me kike faɗa Asma'u”.
Cikin zubda hawaye da rauni Asma'u ta gyaɗa kai tare da cewa.
“Wallahi Ummi naga Yah Jameel tare da Yah Moddibo”.
Yanayin da take magana cikin alamun kiɗima da gigita yasa Ummi saurin janyota ta riƙe ta.
Innayi ma matsowa kanta tayi kana ta riƙe hannunta tare da cewa.
“Asma'u wanda ya rasu yana dawowa ne?”.
Kallon Innayi tayi da jiƙaƙkun idanunta kana tace.
“Innayi wallahi Yah Jameelu na gani naga Yah Jameel Wallahi na ganshi”.
Cikin fesar da numfashi Ummi tace.
“Asma'u ki nutsu mana, In dai Jameelu ne da gaske ai zai iso mu”.
Ummi kam kallonta kawai take aranta tasani cewa tabbas Jameelunta ya rasu ya barta tasan cewa babu wani Jameelu sai dai in gezo yake wa Asma'u ta.
Aunty Ruƙayya dake zaune can gefe ta miƙe ta matso gefen Asma'u ta zauna tare da riƙe hannunta tace.
“Asma'u ya za'a yi wanda ya mutu ya dawo? Shi wanda ya mutu baya dawowa ai shi mutuwa ɗayace idan mutum yayi ta yayi ta har abada”.
Cikin matsanancin kuka Asma'u ke girgiza kai kana tace.
“Wallahi Allah Aunty Ruƙayya na gansa”.
Ƙiran Sallar Maghriba da akayi ne yasa Ummi kallon Asma'u cikin tsawa ta haɗe fuska kana tace.
“Maza tashi Kije kiyi a''wala kizo kiyi Sallah”.
Da sauri tace.
“Wallahi! Wallahi!! Ummi Yah Jameel na gani, ki yarda dani”.
Cikin haɗe fuska Ummi tace.
“Zakije kiyi salla ko zaki tsaya hauka”.
Jiki asanyaye ta miƙe taje tayi al'wala kana tazo ta shimfiɗa Sallah kana tayi Sallah koda suka idar da sallar Maghriba Azkhar sukayi har aka kira Isha'i kana sukayi ...
Bayan sun idar da Isha'i Asma'u ta koma gaban Ummi ta zauna cikin muryan kuka tace.
“Wallahi Ummi Yah Jameel na gani Ummi ki yarda dani ku nemi Yah Moddibo wallahi Yah Jameel na gani fa Ummi”.
Ganin yanda ta rikice yasa Ummi sauke zazzafan ajiyar zuciya tare da kallon Innayi da tazo gabansu kana tace.
“Innayi ane momin Moddibo al'amarin Asma'u yayi yawa fa, gaba ɗaya agigice take kinga Sallar nan har aka idar da Maghriba kuka take har aka zauna Azkhar still kuka take har muka jira Isha'i kuka Asma'u keyi”.
Kai Innayi ta jinjina tare da faɗin.
“Toh shikenan”.
Ta faɗa tare da miƙewa ta nufi side ɗin Didi.
Tana shiga Side ɗin Didi suka sake gaisawa kana ta yiwa Didi bayanin abinda ke faruwa.
Cikin sauƙe numfashi Didi tace.
“Tabbas ai shima kanshi Aleeyu sanadin shigowar sa Masarautar nan haɗuwar sa da Dr Jameel ne”.
Cikin yanayin mamaki Innayi ta tallafe kuncinta tare da faɗin.
“Toh waye Dr Jameel ɗin?”.
Ahankali Didi ta shiga bata Labarin da Dr Jameel ya bata.
Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe kana tace.
“Toh dan Allah ayi min iso zuwa Side ɗin dasu Moddibo suke dan bansan inda suke ba”.
Ƴar dariya Didi tayi tare da cewa.
“Ai suna kusa daku suna ƙasa, kuna sama bari nayiwa Jakadiya magana ta rakaki”.
Nan Didi ta umarci Jakadiya kana ta yiwa Innayi jagora zuwa sashen dasu Moddibo suke...
Innayi na shiga ta samu Zakariyya Dr Jameel Ibraahim suna Kan dining yayin da ta haɗu da Moddibo gab bakin ƙofa da alamun zai tafi wajensu ne, dan ya duba halin da Asma'u ta tafi.
Yana ganin Innayi sai yayi saurin komawa baya.
Innayi kuwa tana ganinsa tayi murmushi.
Shi kam hannunta ya riƙe suka ƙarasa cikin falon kana suka zauna kan kujera suna zama kan kujera yace.
“Innayi nayi kewarki”
Cikin jin daɗin ganinsa ta gyara zama tare da faɗin.
“Nima nayi kewarka, amman dama ai nasan cikin danginka za taho nasan ka dawo cikin ƴan uwanka muhallinka”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Innayi wani irin tarin abubuwa kikayi ta ɓoye min a iya tsawon rayuwata?”.
Numfashi ta fesar da cewa.
“Sai ahankali yanzu dai farko waye Asma'u ta gani ta koma tana ihu tana ce mana Jameel ne”.
Kai ya jinjina tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Gashi can Innayi juya ki kallesa baiyi miki kama da Jameel ba?”.
Da ƙarfi Innayi ta tashi kana ta buga hannunta akan ƙirjinta cikin tsananin ruɗu tace.
“Kamar yaya kama?,Aliyu kace min Jameel dai Ashe gaskiyan Asma'u Jameelu ta gani”.
Ta ida Maganar tare da juyawa ta nufi dining area cikin sassarfa.
Tana zuwa ta kamo hannun Dr Jameel tare da riƙewa tace.
“Jameelu”
Kallonta yayi tare da yin murmushi shima kansa yanda suke zuzuta tsananin kamansa da Jameelu ya fara bashi tsoro da mamaki.
Innayi kuwa batare data jira komai ba ta kama hannunsa tana ja.
Shi kuwa Dr Jameel tsintar kansa da bin bayanta yayi.
Shima Moddibo cikin sauri yabi bayansu yana cewa.
“Innayi ba Jameelu bane wallahi tsananin kama ne”.
Ina tuni Innayi ta fice batare data sauraresa ba ta fara haurawa step ɗin tana cewa.
“Ummin Jameel”.
Zakariyya da Ibraahim ma na biye dasu suna shiga Falon da Ummu ke zaune Innayi na cigaba da cewa.
“Ummin Jameel Wallahi gaskiyar Asma'u ne Jameelun kine”.
Akuma dai-dai lokacin Ummi ta juya da sauri idanunta suka sauƙa akan Fuskar dake tsananin kama da Jameelunta komai na Jameelunta a fili.
cikin wata raunatacciyar murya tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”.
Sai kuma ta koma ta faɗa kan kujera idanunta na zubda hawaye shar-shar-shar.
Itama Asma'u cikin sauri ta riƙe hannun Ummi tare da faɗin.
“Ummi ba kin gani ba na faɗa miki Yah Jameel ne”.
Sai kuma ta saki hannun Ummi ta koma ta riƙe hannun Dr Jameel na dama Innayi kuma na riƙe da hannunsa na hagu suka zo gaban Ummi suka durƙusa sai shima ya tsinci kansa da durƙusawa agabanta, haka nan yaji kima da martaban matar sun cika masa idanu.
Da sauri Moddibo ya ƙarasa shiga wa falon tare da zama gefen Ummi wacce ke kan 3sitter kana cikin raunin murya yace.
“Ummi”.
Cikin zubda hawaye ta juya ta kallesa cikin rauni ya cigaba da cewa.
“Ummi ki kalli duk komai na Jameel ne muryansa, Tafiyarsa, Gangar jikinsa, Har fa asakin da Jameel keyi shi yake yi amma wallahi Ummi ba Jameelunki bane kamannin ne yayi yawa Wallahi!³ Ummi ba Jameelunki bane”.
Juyawa Ummi tayi ta kallesa cikin jinjina masa take cigaba da gyaɗa kanta jikinta yana bata ba Jameelu bane domin jikinta ba amsheshi a matsayin Jameel ba wannan bawai ɗan ta bane agabanta amma zuciyarta taƙi yarda.
Kai ta girgiza still hawaye na bin fuskarta ta juya ta kalli Dr Jameel da yake durƙushe agabanta.
Ganin yanda take zubar da hawaye yasa shima yake zubar da hawaye.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Toh meyesa ka kuma?”.
Ahankali ya ɗago kai ya kalleta cikin tarin tausayinta da kuma rauni yace.
“Saboda kukan da naga kunayi shiyasani kuka, nasan ko waye Jameel awajenku mutum ne mai daraja, mai kima wanda shine jigo acikin rayuwarku”.
Kallonsa kawai Ummi keyi hawaye na cigaba da zuba daga idanunta sabida yadda muryasa ma sai ta Jameel ɗinta.
Shi kuwa Dr Jameel kuwa cikin rauni da zubda hawaye ya cigaba da faɗin.
“Na fahimci kuna jin ƙuna na rashinsa amma Ummi nayi miki al'ƙawari in dai kin amince kun bani dama in sha Allah zan maye muku gurbinsa”....