← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 150

Sashe 32

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anutse Mommy ta gyara zamanta tare da kallon Hajja Nana cikin sanyin murya tace.
“Dan Allah Hajja Nana kiyi haƙuri abinda ya kawo mu nazo ne in baki haƙuri naga kin tafi ranki aɓace abinda Khausar ta aikata ba laifi na bane ba kuma da yawuna bane”.
Ta ida maganar Muryanta na rawa tamkar zata fashe da kuka.
Hajja Nana kuwa jin yanda Muryan Mommy ke rawa yasa tayi saurin Kallonta har ranta take Jin Mommy domin alokacin zamansu tasan bata da matsala cike da kulawa tace.
“Kar kiyi kuka Aysha aina zauna dake nasan halinki fitsaran Khausar ba daga gareki bane kuma ba daga Allah bane halitta ce da tayiwa kanta”.
Cikin sauri Khausar ta ɗago kanta ta watsa mata Harara cikin ƙasa da murya tace.
“Inma tsiwarce ai awajenki na gada”.
Harara Mommy ta watsa mata hakan yasa ta tsuke bakinta.
Ahankali Mommy ta sauƙe Ajiyar zuciya kana ta fuskanci Hajja Nana cikin sassauta murya tace.
“Itama kanta Khausar al'amarin yazo mata adolene”.
Baki Hajja Nana ta taɓe kana tace.
“Bangane yazo mata adole ba inace soyayya take da wani can yasa ta kalli tsabar idona tace bata son ɗan Uwanta”.
Kai Mommy ta Girgiza kana ta kwashe duk yanda Khausar ta faɗa mata sunyi da M Jameel aranan da aka sace sa kana ta daura da faɗin.
“Sannan kuma yaron shine ƴan Kidnapping suka sace sa suka ɗauresa har ya rasu”.
Ahankali Khausar tayi ƙasa da kanta hawaye na taruwa akwarmin Idanunta.
Cikin sanyi Mommy ta cigaba da cewa.
“Sai maganar tasa ta zama kamar wasiyya kuma ya roƙi alfarma ya faɗawa kakar Amininsa Moddibo kana Ya faɗawa mahaifiyarsa da mahaifinsa yanzu ma haka da mahaifinsa muka zo kuma yace alfarma yake nema ko bayan ransa acika masa wannan burin nasa, jin haka yasa nima baki ɗaya jikina yayi sanyi”.
Numfashi Hajja Nana ta fesar kana tayi ƙasa da kanta cikin sanyin murya tace.
“Allah sarki shine akace ansace sa a daure sa ya rasu ko?”.
Asanyaye Mommy ta gyaɗa mata kai tare da faɗin.
“Eh shine aka sace aka ɗaure har ya rasu”.
Jinjina kai Hajja Nana tayi tare da watsawa Khausar Harara ta kalli Mommy cikin raunin murya tace.
“Ayyah Allah sarki Allah yajiƙan sa da rahma ina ma ace yana raye dashi zan bawa Khausar ya aura wallahi koda Khausar bata auri Aliyu ba bazan damu ba”.
Cikin raunin murya Mommy tace.
“Gashi kuma shi ɗin Ubangiji bai nufa za ayi dashi ba, babu gatan da zamuyi masa sai dai addu'a”.
Jinjina kai Hajja Nana tayi cikin sanyi tace.
“Sosai ma”.
Mommy kuwa sassauta murya tayi kana tayi ƙasa da kanta tace.
“Kuma inda hali mu samu mu cika masa wasiyyar daya bari”.
Gyara zama Hajja Nana tayi tare da kallon Khausar da kanta ke ƙasa kana ta kalli Mommy nunfashi ta fesar cikin sanyin murya tace.
“To aini bani da tacewa acikin wannan maganar sai abinda iyayenta suka faɗa tunda annuna min bani da iko da ita”.

Dai-dai lokacin Baffa Jimeta ya shigo Anutse ya zauna gefenta ya tanƙwashe ƙafafunsa kana ya fuskanceta da kyau yace.
“Kina da iko da ita mana muma kam mu aike kike da iko damu amma ana neman alfarma awajenki gacan Baban yaron ma awaje sai hawaye yake zubarwa yana neman alfarma acikawa dansa wasiyyar sa”.
Daga waje ta jiyo sheshsheƙan Kukan Abba cikin sauri ta miƙe ta nufi ƙofa ta fita kusa dashi ta zauna cike da tausayawa tace.
“Kuka kuma kake Alh Bashir?”.
Cikin sheshsheƙa Abba yace.
“Ya za ayi ba zanyi kuka ba burin da Jameeluna da kuma fatan da yake so yana tangarɗa koda aranan da muka rabu na ƙarshe yace min shine babban burinsa daya rage aduniya”.
Cikin zubda hawaye ya cigaba da cewa.
“Yace babban burinsa yaga Moddibo yayi Aure kafin nasa Saboda Aliyu yana buƙatar mace yana buƙatar ayi masa Aure sai dai Allah bai nufa Jameelu na zai gani ba ina tsoro saboda bani da damar da zan cika masa wasiyarsa”.
Gyara zama Hajja Nana tayi kana ta gyara ɗaurin dankwalinta ta sunkuyar da kanta ƙasa kana ahankali ta ɗago Muryanta na rawa tace.
“Na amince ina dai dan nice. To acikawa yaron nan burinsa Allah yajiƙan sa da rahama na amince Ayi aure...

Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N 09097853276.

By
*GARKUWAR FULANI**SAKAYYAH book 2... page 9*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwatanta Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.
INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.

Shiru Hajja Nana tayi kafin ahankali ta ɗago ta kallesu ɗaya bayan ɗaya tace.
“Shikenan ni babu abinda zance acikin wannan al'amari zira ido da kunne nawa duk abinda yaje ya dawo Khausar ita tajawa kanta”.
Ƙwaffa tayi kana ta cigaba da cewa.
“Tunda kuma iyayenta kuce kun amince, to ni dai babu abinda zance bare inyi baƙin jini”.
Kallon Baffa Jimeta daya sunkuyar da kai ƙasa tayi taɓe baki tayi kana tace.
“Yo ni me zai da meni tunda uban daya haifi Aliyu bai damuba yanuna ayi mata yanda take so ai shikenan, tunda bata illar tsintacciyar mage bata mage ba, ɗan da ba'asan Asalinsa ba ba'a san tushensa ba duk abinda ya faru ita tajawa kanta”.

Anutse Lamiɗo ya ɗago kansa ya kalli Hajja Nana cikin sauri yace.
“Insha Allahu ma babu abinda zai faru sai Al'khairi”.
Abba kuwa karɓan maganar yayi ta hanyar cewa.
“Insha Allah Moddibo zai riƙe ta da amana da gaskiya da Izinin Ubangiji Khausar ba zata tozarta ba yanda Khausar ta amince tayi niyyar cikawa Jameelu na wasiyyar sa”.
Ahankali Khausar dake can cikin ɗaki ta lumshe Idanunta zuciyarta na bugawa da Masifaffen ƙarfi.
Cikin sanyin murya Abba ya cigaba da cewa.
“Insha Allahu Ubangiji bazai tozarta taba Allah zai cika mata burikanta na rayuwa insha Allah zata kasance cikin kwanciyar hankali da nutsuwa”.
Chapter 32 · 0% Book details