← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 150

Sashe 23

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abba ya cigaba da cewa.
“To Kuma Manager company shima ba shida lafiya toh sun nemi da Inje kuma nima bana jin daɗin jikina bazan iya zuwa ba”.
Ahankali Ummi ta ɗago kanta tare da kallon sa gani tayi baki ɗaya ya rame ya zama wani so silent dashi.
Cikin sanyin murya da tausayawa tace.
“Toh Abban Jameel Idan bamu sa haƙuri aranmu ba ya zamuyi ka kwantar da hankalin ka Ubangiji Allah yajiƙan Jameelu shine kawai fatan mu da addu'ar mu”.
Kai ya gyara tare da sauƙe numfashi yace.
“Insha Allah zan kiyaye.
Yanzu mshawan jinin ne baki ɗaya yasani agaba duk kan magungunan da nake sha sai yazama kamar basa min aiki”.
Jinjina kai tayi cikin sanyin murya tace.
“Allah ya sawwaƙa amma ka rage tunani koda kana shan magani idan baka rage tunani ba ba zaiyi aiki ba”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana yace.
“Toh Fatima ya zanyi idan banyi tunani ba!?”.

Ahankali ta sunkuyar da kanta hawaye na zuba daga idanunta.
Gyara zama Abba yayi cikin sanyin murya yace.
“Toh dama shine nake so Moddibo ya wakilceni yaje shine yake cemin bawai zuwan bane baya so amma baya so yayi nesa da Umminsa”.
Ahankali ta ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kalli Moddibo murmushi tayi kana tace.
“Ba komai Babana kaje wannan ma ai abin farin ciki da al'fahari ne zaka cika burin da Jameeluna yake son cikawa. Ubangiji Allah yakai ka lafiya ya dawo da kai lafiya Allah ya maka albarka”.
Cikin sanyin murya da tausayawa Moddibo ya amsa da Ameen asaman laɓɓansa.
Ahankali Ummi ta cigaba da cewa.
“Insha Allah zanyi ta binka da addu'a ba komai Babana ai muna tare ina nan ina Marocco amma idan ya gama zai dawo ko?”.
Ta ƙarasa maganar ta sigar tambaya tana kallon Abba.

Kai Abba ya gyaɗa mata kana yace.
“Eh zai dawo Insha Allah bazai wuce sati biyu”.
Jinjina kai tayi tare da kallon Moddibo kana tace.
“Badamuwa Babana ai zamu nayin waya”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Shikenan Ummi ba matsala tunda kin amince.
Murmushi tayi still Idanunta cike da ruwan hawaye tace.
“Na amince Babana Allah Ubangiji ya kaika lafiya Allah ya dawo da kai lafiya Allah yasanya alkhairi da albarka acikin tafiyar.
Ahankali yace.
“Ameen Ummi”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauke tare da kallonta kana yace.
“Yanzu kuma sai batun kuɗin ku da aka har haɗa”.
Sunkuyar da kai Ummi tayi Atake hawaye suka cigaba da zubowa daga Idanunta cikin raunin murya tace.
“Toni me zanyi da kuɗin nan ne Abban Jameel?”.
Kai Abba ya Girgiza cikin rawan murya da rauni yace.
“Toh nima ɗin idan kun barsu awajena me zanyi dasu ga kuɗin Aliyu ga naki kowa ya karɓi kuɗin sa kowa yana da bukatarsa motar ki da Sarƙoƙinki kika siyar ki sayi wata mota amfani dashi”.
Kallonsa ya mayar kan Moddibo kana yace.
“Kaima Moddibo ka karɓi kuɗin ka ka sayi mota sannan sauran kuɗin kayi abinda ya dace dasu”.
Kai Moddibo ya girdiza ciki rauni yace.
“Abba me zanyi da kuɗin?.
Ai kuɗi na gama abinda ya dace inyi dasu Babu abinda zanyi dasu tun da har basu tseratar min da J ɗina ba wani amfani zasu yimin?”.
Cikin rauni Abba yace.
“Bakomai Moddibo ka karɓi kuɗin nan idan ka barsu awajena kun barmin tashin hankali da damuwa”.
Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da faɗin.
“Kuyi hakuri duk kan tsanani yana tare da sauƙi addu'a kaɗai zamuyi wa Jameelu amma kamar yanda yace ne Moddibo ka karɓi kuɗin nan sannan kema Fatima ki karɓi kuɗin na shine abu mafi a'ala”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.
“Yawwa shine dai ki bani account number inyi Miki transfer”.
Kai Ummi ta shiga Girgizawa hawaye na kwaranya daga Idanunta.
Ganin haka yasa Malam Ahmad ya karbi wayarta tare da fito da account number ya faɗawa Abba Atake Abba ya mata transfer kuɗinta Naira million goma da dubu ɗari takwas kasancewar yana da account number Moddibo Shima Atake ya Masa transfer kuɗinsa.
Anutse ya gyara zamansa tare da Kallonsu cikin sanyin murya yace.
“Nagode da halarcinku agareni musamman ma kai Moddibo Allah Ubangijin ya biya da mafificin alkhairi”.
Atake Moddibo yaji wani irin rauni ya mamaye sa kallon Abba yayi muryarsa na rawa yace.
“Abba akan J ne kake min godiya?”.
Numfashi Abba ya fesar tare da sauƙe ajiyar zuciya yace.
“Toh Aliyu ya zanyi kayi min halarci duk kan inda Aboki na gari ya cika ka cika Ubangiji Allah yasaka da alkhairi Nagode da halarcin ka”.
Cikin raunin murya Moddibo yace.
“Ameen Abba”.
Kallon Ummi Abba yayi kana yace.
“Toh insha Allah sammako zaiyi ya tafi kinsan akwai tazara tsakaninmu da Adamawa kuma can zai shiga jirgin zuwa Abuja”.

“Toh Allah ya kaimu Allah yakai ka lafiya Babana Allah ya kareka”.

Cikin sanyin murya yace.
“Ameen Ummi”.
Miƙewa Abba yayi tare da cewa.
“Toh bari mu tafi”.
Godiya suka masa har sun fita Ummi ta miƙe tare da bin bayansu abakin barandar ta tsaya tare da cewa.
“Babana amma ai zaka dawo daddare muyi sallama ko?”.
Jinjina kai yayi kana yace.
“Insha Allah Ummi zan zo”.
Bayan sun fita kai tsaye gidan Malam Arɗo Abba ya ajiye Moddibo zaiyi masa sallama kana Abba ya wuce gida.

Cikin sanyin jiki Khausar ta isa Bedroom din Mommy, a hankali ta zauna agabanta cikin Muryan kuka tace.
“Mommy kiyi haƙuri kada kiyi fushi dani”.
Tsira mata Ido Mommy tayi ba tare da tace Uffan ba.
Cikin raunin murya Khausar ta haɗa hannunta waje ɗaya kana ta fashe da matsanancin kuka da sheshsheƙan tace.
“Mommy dan girman Allah kiyi haƙuri ki daina fushi dani”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da fesar da nunfashi kana tace.
“Khausar to ni me zan ce miki?.
Bani da abinda zan ce miki tunda ai hukunci ne kin riga da kin gama yanke shi baki nemi shawarata ko izinina ba”.
Girgiza kai Khausar tayi hawaye na cigaba da kwaranya daga Idanunta.
Ita kuwa Mommy kauda kayi tayi gefe kaba ta cigaba da cewa.
“Kawai kin fadi maganarki gaba gaɗi, sannan koda akeɓance baki taɓa faɗa min tsakanina ni dake ba, sai da kika zaɓi cikin mutane sannan kika faɗa saboda ki kunya tani kin bani mamaki ban taɓa zaton haka daga gareki ba”.

Khausar kuwa kai take Girgiza cikin muryan kuka mai gunji kana Muryanta na rawa tace.
“Mommy nima ina tsoron Modibbo bafa, dan nasan baya sona”.
Kallonta Mommy tayi cikin da mmki ta tsareta da ido tare da cewa.
“Toh kina tsoron Auren Moddibo kuma, akan wani dalili zaki ce zaki Aureshi? Kuma bayan kina sane baya sonki”.
Sunkuyar da kai ƙasa tayi cikin gunjin kuka ta lumshe Idanunta tare da taune Lip ɗinta cikin raunin murya tace.
“Mommy wasiyyar Yah Jameel ne Yah Jameel ne ya roƙi al'farma awajena sannan tun lokacin daya faɗa min yace min wasiyya ya barmin yace koda ya mutu kada in manta ya nemi wannan al'farma awajena”.
Sai kuma ta kasa ci gaba da mgnar sakamakon kuka da yaci ƙarfinta hannu ta sanya ta goge hawayen fuskarta wani na sake zubowa Muryanta na rawa ta cigaba da cewa.
“Aranan da za'a ɗauke Yah Jameel bayan mun taho amota yace min yana neman alfarma awajena in na ɗauka Alfarman da yake nema awajena tamkar wasiyya ce".
Sai kuma ta kife kanta kan cinyar Mommy tana mai sakin wani irin raunataccen kuka murya na karkarwa taci gaba da cewa.
“Mommy a ranar a gabana Yah Jameel yayi ta kuka kamar yaro ƙaramin ya rinƙa haɗani da Allah da Manzonsa cikin sanyin murya da neman alfarma yace dan Allah kada ince bazan yi masa ba yana so koda bayan Ransa in Auri Moddibo”.
Kallon ta kawai Mommy keyi bako ƙyaftawa yayinda itama hawaye ke zubo mata.

Cikin sheshsheƙan Kuka Khausar ta lumshe Idanunta tana tuna lokacin da suka kasance da M Jameel amota yana faɗa mata magana da sauri ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta kana muryanta na rawa tace.
“Mommy alokacin Cike da damuwa na kalli Yah Jameel nace ya Jameel Meyesa kake Fadar haka Meyesa kake magana me karyar da zuciya dan Allah kada kace wasiyya nidai ka faɗi ko wace irin alfarma kake so zanyi maka domin kafi ƙarfin alfarma awajena”.
Taja hanci tare da kallon Mommy da yanayin ta ya sauya Muryanta na rawa kana numfashinta na fusga tace.
“Sai yace min Khausar koda ace kin riski labarin mutuwa ta ki tuna da Alfarman da kuma Wasiyyar da na bar miki ki Auri Moddibo idan kuma Allah yasa ina raye zanfi kowa farin cikin ganin An ɗaura Aurenki da Moddibo”.
Chapter 23 · 0% Book details