← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 150

Sashe 79

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sun fito daga cikin masallancin bisa umarni da jagorancin Abualeey da Ibraahim da Sarkin fada da su Galadima Waziri, Wambai, Ɗan Maliki Dan Muram, da dai sauran, aka rinka yagayawa dashi ana nuna mishi lungu da saƙi na masarautar kofa-kofa Part-part haka aka rinƙa kaishi ana nuna mishi ƴan uwa da abokan arziƙu.
Daga ƙarshe suka shiga part ɗin da yafi kusa da na Didi wanda nan ne Part ɗin ƙanin Abualeey wanda baida lafiya tsawon shekaru anyi neman mgnin duniya an gaji an zubawa sarautar Allah ido.
Daga bisani suka shiga part ɗin Niyna anan suka yada zango suka sha tea ƙarfe tara da kwata dai-dai suka fito, daga nan kuma part ɗin Didi suka shiga.
Shi da Abualeey da Ibraahim, yayinda duk sauran kowa ya nufi gidansa.

Suna shiga suka samu sau Lalla Khadijah a falo.
Kusan a tare suka haɗa baki wurin gaida mahaifin nasu, zama shi ya gyara bisa kujerara kana ya kalli taron ƴaƴan nashi.
Murmushi yayi jin Lalla Khadijah na cewa Modibbo.
“Ango mai jiran gadaje biyu na sarautar Mouley dana amarya.
Kanshi ya ɗan kauda gefe ba tare da yace komai ba sai ɗan gudun murmushin gefen baki da yayi, sai kuma ya kama hannun Hakim tare da cewa.
“Meya hanaka zuwa masallaci”.
Ibraahim ne ya ɗan mari ƙeyar Hakim ɗin tare da cewa.
“Baccin banza mana, in ya samu Game sai ya kai karfe biyun dare yana abu ɗaya”.
Cikin tsuke fuska yace.
“Daga yau kada in sake zuwa Masallaci ban gankaba”.
Cikin jin daɗi duk suke kallonsa,
Shi kuwa Hakim cikin jin shakka da ganin kwarjin Modibbo yace.
“In sha Allah bazan ƙaraba Unclee Aleyyh, kuma dama in a gidane wlh kullum da Abbana muke zuwa Masallaci ka tambayi Mom kaji”.
Da sauri Lalla Khadijah tace.
“A'a ba ruwana ni bazanyi shaidar zurba”.
Shi kuwa Modibbo a hankali ya kalli Rahama da Didi da suka fito yanzu Hannu Didi ta miƙa mishi alamun suyi muhabaha, murmushi yayi cike da jin kaunar ta a ranshi ya miƙa mata hannun.
Cikin so ƙauna kulawa ta kalleshi, sai kuma ta kalli gefen hagu da damanshi, cikin yanayin zazzafan shaƙuwa dake shiga tsakaninsu yayi mata kallun alamun.
“Me kike nema".
Ɗan matse hannunsa tayi tare da cewa.
“Naga banga ƴata ɗaya bane a nan ɗin. Ina ka baro min ita?”. Ciki ware manyan idanunsa yace.
“Didi bansanta ba”.
Kusan a tare duk sukace.
“Matar takace baka saniba”.
Sai kuma ya kalli Abualeey da yace.
“Ayi mishi uzuri yau dai kam, dan daga Masallaci muka wuce zagaya fada, wata ƙil shiyasa bai taho da itaba”.
Cikin ɗan tsare fuska Didi tace.
“Toh maza tashi kaje ka taho min da ɗiyata, yanzu-yanzu”.
Cikin karya wuya yace.
“Didi Rahman t..."
Da sauri ya katseta da cewa.
“Tashi maza kuje, Ibraahim nuna mishi hanyar tsakiyan nan”.
Toh Ibraahim yace kana ya miƙe yayi gaba.

Daga nan cikin falon Didi suka bi cikin wani dogon corridor mai faɗi.
Tafiya mai ɗan tsawo sukayi, yaga sun ɓullo, ta kan steps nan da zai sadasu da saman kuma basubi, cikin babban falon nan ba.
Cikin sanyi Ibraahim yace.
“Ga hanyar dake tsakanin ka da Didi, ni inda ka zauna ɗinnan nanne Side ɗina, sai kuma ta gefen nan akwai hanyar da zaku fita ba sai kabi cikin falon nanba, tana ƙofar part ɗinka yake, ko da mota zaka fita ranan gate ɗin ka yake”.
Cikin gamsuwa Modibbo ya gyaɗa mishi kai.
Shi kuwa Ibraahim fara sauƙa yayi ta hanyar da zata sauƙa dashi ta cikin falon yana mai cewa Modibbo.
“Nima bari inje in ɗanyi wanka kafin ku fito”.
Kai kawai Modibbo ya gyaɗa mishi kana ya wuce cikin corridor insu kana ya maida ƙofar ya rufe.

Khausar kuwa tunda tayi sallan asuba ta kwanta a nan a falon tai baccinta, sai ƙarfe tara dai-dai ta farka tana tashi kuwa ta shiga wonka.

Dai dai lokacin yake haurowan kuma khausar ɗin ke tsaye gaban dressin mirror cikin wata chiga ta al'farmar da alamun yanzu ta fito wanka ta kuma fesa kolliya.
Ɗinkin doguwar rigar Getzener ce maroon color mai masifar maiƙo da sheƙi, an yiwa rigar aiki da zaren Golden color mai ɗan karen sheƙi, sai rashin fari, da kuma yellow da blue kaɗan-kaɗan wanda daga ƙasa zuwa tsakiya ne aka watsa tsaren da salon jelar ɗawisu, daga sama kuwa wasu irin duwatsun karaine masu masifar ɗaukan ido aka watsa a jiki wanda suka kuma an jerasu kamar tsarin gashin ƙirjin ɗawisu.
Cib-cib da jikinta rigar tayi wacce har ta ɗan matseta daga saman ƙirjinta da ƙasan mazaunanta da suka fito hani'an.
murza ɗaurin ɗan kwalin turban tayi ya zauna ras yayinda daga tsakiyar ɗan kwalin ta baya ta fito da jelam gashinta, wanda bata kitseshi ba.
Ƴan kunnen da sarƙa na gold masu ƙaramin nauyi tasa, sai kuma zobe.
Fuskar ta ta kalla a madubin, sai kuma ta tura baki, ganin har yanzu idanunta na ɗan kumbure kaɗan, yayinda ƙasansu dai-dai inda akesa kolli yayi ja, kamar dai kollin jambaki, hannunta tasa ta ɗauki ɗaya daga cikin hodar da aka jera mata a gaba dressin mirror, sai kuma ta maida ta ajiye tare da tura baki kana tace.
“Ba kollinyan da zanyi ma, harshenta, ta ɗan sa ta lashi pich lips inta, sai kuma dai ta ɗauki man bakin ta ɗan goga a yatsarta ma nuniya kana ta ɗan murza yatsar kan lips inta, wani irin sheƙi suka fara kamar ta samusu jambaki.
Turare kawai ta fara fesawa.

Shi kuwa Modibbo a hankali yake takawa har ya iso, dai-dai bakin ƙofar falonta, ƙofar na buɗe amman kuma ba kowa, sai tv data kunna ana karatun qura'an.
Wucewa yayi ya shiga falonsa, kai tsaye Bathroom ɗinsa ya shiga, ya shiga wanka.

A Side dinsu Ummi Innayi kuwa Ummin Jameel ce ke waya da Mommyn Khausar cikin ɗan yin ƙasa da murya tace.
“Wallahi nima tun ɗazu nake kiran wayarta yana shiga amman bata ɗagawa, na rasa ma ta ina zan fara na kirata yafi sau shida”.
Wani irin numfashi tausayi Mommy taja kana cikin sanyi tace.
“Ni nayi mata kira yafi goma, yanzuma saida na kira bata ɗayaba, Ummin Jameel kiyi ƙoƙarin zuwa inda take”.
Da sauri tace.
“Ok ba matsala in Sha Allah yanzu zanyuwa innayi mgnar”.
Daga nan suka katse kiran kana ta juyo ta kalli Innayi tare da cewa.
“Innayi ko zamuje wurin Khausar? Tun ɗazu muje kiranta bata ɗagawa”.
Murmushi Innayi tare da cewa.
“Ai in da buƙatar zuwanmu sashinta Jakadiya zata sanar mana.
Yanzu babu mai zuwa inda take, kuma itama ƙofar Didi kawai zataje, shima dan wannan zuwan shine madubin da za'a gane cewa, ya ta kasance tare da mijinta, kuma in akwaida abinda ya faru za'a nemu. Kiranta kuwa bari zuwa anjima ku sake gwadawa”.
Innayin ta kare mgnar a dungule, wacca kuma tuni Ummi da Aunty Rukayya sun gane ma take nufi.
Haka yasa Ummi sauƙe numfashi kana ta kira Mommy ta ɗan kwantar mata da hankali toh kawai Mommy tace amman taci gaba da kiran.

Nigeria
Abuja, cikin Maitama. Amina da Unclee Naseer tsaye a bakin falonsu, bisa alamu fita zaiyi, cikin salo na musamman, ya ɗan jawota jikinshi tare da ruggume ta cike da yaudara yace.
“My Dear Kada ki damu bazan daɗeba zan dawo, bazan wuce awa biyu ba”.
Cikin yauƙi tace.
“Ni da mu tafi tare”.
Kai jujjuya tare da ɗan janye jikinshi kana yace.
“Baby mitin fa zamuyi, kuma duk mu ya mune maza. Ki dai yi haƙuri kinji, bari in tafi kada in makara”.
Cikin kwarkwasa tace.
“Toh sai ka dawo”.
Ɗan shafa fuskarta yayi kana ya fice.
Ita kuwa ƙofar ta maida ta rufe.
Tare da komawa cikin falon, bisa 2 str ta kwanta tare da ci gaba da chating.

A hankali ta ɗan juya kanta, jin kamar alamun an buɗe ƙofar ɗakin nan da bata taɓa shigaba, kai ta maida ta jingina taci gaba da latsa wayar, sabida ganin ƙofar nan a rufe.
Sai kuma ta ɗan dakata da latsa wayar sabida jin kamar hucub numfashin mutun, haka nan kuma wani irin kasala da tsoro ya diro nata, a hankali ta juya idonta zuwa kan A.C wanda a zatonsa hushin fesar da sanyinsa ne.
Da sauri ta tashi zaune jin hucin ya karuwa da kuma ƙara matsota. Wani irin gigitaccen kara da tsalle ta haɗa tayi a tare, sabida ganin wani irin zabgegen maciji baƙƙirin da yake mirgina a tsakiyar falon yana mai baza wani irin fitinennen huci da zaro harshe, abinka da babu alla a cikin rai, gaba ɗaya ta mance da addu'a sai karkarwar da ihun da takeyi, tare da dira ta bayan kujerar cikin kiɗima, ta fara lalubar wayarta, tana ɗaukan wayar ta dannawa, Unclee Naseer ɗin kira, amman bai dagaba, da gudu ta nufi bedroom ɗinta, tana shiga taci gaba da danna mishi kira babu ƙaƙƙautawa amman ko sau ɗaya bai ɗagaba.
Sai kuma ta fara kiran number Hajia Bunayyah itama waya mata ringgin amman ba'a ɗagawa.

Wani irin gigitaccen ihu ta fara kurmawa lokacin da taji hucin na ƙara matsowa bedroom ɗin nata, ga gida ita kaɗai babu ko mai gadi.
Chapter 79 · 0% Book details