← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 150

Sashe 33

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kallonsa Hajja Nana tayi kana ta jinjina kai tace.
“Haka kake gani kk? Hmm ta yaro kyau take bata ƙarko, kai yanzu Alh Bashir tunda kuke kasan asalin yaron ne?”.
Ahankali Abba ya sunkuyar da kansa ƙasa batare da yace Uffan ba.
Ƙwaffa tayi kana tace.
“Hmm ka buɗe baki kai tsaye kace baka sani ba shine magana”.
Kallonta ta mayar kan Malam Arɗo tace.
“Malam kai da suke aiki a ƙarƙashin ka kasan Asalinsa?, kasan waye Ubansa? Kasan inane Ƙasar da suka fito kasan inane Jaharsu? kasan menene tushensa? Waye ubansa waye Uwarsa?”.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe kana ya kalleta Anutse yace.
“Ai a al'amarin Aure wannan duka ba magana bane”.
Kai ta girgiza cikin tsira masa ido tace.
“Yanzu ina magana da Malam Liman zai miƙe yace min Allah yace Annabi yace amma ai Aure abin bincike ne ko”.
Cikin sanyin murya Lamiɗo yace.
“Dan Allah Addah Nana kiyi haƙuri wannan tone-tonen basu da Amfani”.
Baki ta taɓe tare da Kallonsa kana tace.
“Eh basu da amfani Ni tunda dai aka samu antsira ba ɗan Mayun bane zata aura, aishikenan sai inzira mata ido ni naɗan ji sauƙi ma akan abin”.
Kallon ƙannenta tayi kana tace.
“Yo ai gaskiya ne na fada da kuka wani tsareni da ido, kuma dole idan gaskiya ta taso a faɗeta da ace ta auri ɗan mayu jikan Mayu ai gwara ɗan shegen tunda taji ta gani tana so ta bone dai tayiwa ƴaƴanta da ahalinta”.

Kai Baffa Liman ya girgiza tare da sunkuyar da kansa ƙasa cike da takaici Hajja Nana ta cigaba da cewa.
“Tunda ta yiwa kanta tabo ita tasani amma Ni dai babu ba kina babu hannu na babu ƙafana na suje can su ƙarata sanda ƴaƴanta zasu ce ina dangin Ubansu ta nemi abin faɗa musu”.
Ahankali Mommy da Lamiɗo suka sunkuyar da kansu ƙasa Khausar kuwa hannunta riƙe da kofin madaran da bata shaba bata ajiye ba ɗumin na ratsa tafin hannunta ta tsirawa waje ɗaya ido ba ƙeftawa.

Ajiyar zuciya Malam Liman ya sauƙe tare da girgiza kai kana cike da ladabi da nutsuwa yace.
“Dan Allah Addah Nana ya za'ayi ana kitse gaba kina warware baya dan Allah wasu furucin ki riƙa sanin abinda zaki riƙa faɗa saboda Manzon Allah (SAW)
_Falyaƙun Khairan Auliyastumu”_.

Baki ta taɓe kana tace.
“Naji naji Liman aini zuwa yanzu ko ƙwaƙwalwar kifi ne dani yaci ace in haddace Hadisai sama da dubu tunda duk motsin da nayi sai kace min ga abinda Allah da Manzonsa suka faɗa”.
Sunkuyar da kai Malam Liman yayi cikin taɓe baki ta cigaba da cewa.
“Ni dai na faɗa ba bakina ba hannu na babu ƙafana kuje duk abinda kuka ga ya dace kuyi. Kai kuma”.
Ta nuna Baffa Jimeta da kansa ke ƙasa kana tace.
“Tunda kaine madadin Uba agareta kace kaji ka gani ko? Sannan kaima”. Ta nuna Lamiɗo daya ɗago kansa cikin haɗe girar sama da na kasa tace.
“Kai kuma kaine wakili kuma Uba data tashi agabansa kai kace kaji ka gani ai shikenan na cire bakina aciki amma dan Usmanu na baya raye bazan bari jinjinsa ya cuta ba”.

Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauke kana yace.
“Insha Allahu ma ba zata cutuba da izinin Ubangiji zai riƙe ta da Amana”.
Baki ta taɓe cike da takaici ta juya cikin ɗaki.
Takalli Khausar da har zuwa lokacin hannunta ke riƙe da kofin madaran Harara ta watsa mata kana tace.
“Ke kam kinyi asara gaki mace har Mace Bafulatana tsayayyar mace Kyakkyawa zubin zamani ƙirar masu tsada amma ace wai ke zaki buɗe baki kice kina son Namiji”.
Cikin sauri Khausar ta ɗago kai ta kalleta.
Harara Hajja Nana ta watsa mata kana tace.
“Ki ɗauke wannan tsayayyun idanun naki akaina Ke zakice kina sonsa wanda baisan dake bama sannan baice yana sonki ba bai damu dake ba wai kice kina sonsa shi zaki Aura”.
Fuska Khausar ta ɓata kana ta kawar da kanta gefe tare da murguɗa mata baki da Ido Mommy tayi mata alamar kar tayi magana.
Tsuke bakinta tayi tare da kawar da kanta gefe, jin lokacin sallar La'asar yayi yasa duk mazan suka miƙe suka tafi masallaci.

Bayan sun daeone suna isa afarfajiyar gida suka zauna Anutse Abba ya gyara zamansa tare da fuskantar su da kyau kana yace.
“Toh Alhamdulillah yanzu dai Kamar mun samawa tufkar hanci amma kuma dai Babban abu da yake tafe damu acikin al'amarin”.
Ya sauke ajiyar zuciya kana ya cigaba da cewa.
“Ayi ƙoƙari ayi abin cikin ƙanƙanin lokaci in Allah ya yarda ya lamunce mana komai abune mai sauƙi agaremu inhar kuma kun shirya”.
Jinjina kai Baffa Jimeta yayi kana yace.
“Bakomai in dai wannan ne mu ba matsala awajenmu tunda abin yazo na wasiyya kuma dama a wasiyyar sa ya roƙa ayi cikin gaggawa sannan ya faɗa ya kara cewa yaron nan yana ɓuƙatar aure”.
Jinjina kai Abba da Malam Arɗo sukayi alokaci ɗaya.
Cike da kamala Baffa Jimeta ya cigaba da cewa.
“Tunda har ya fadi haka to yakamata ayi ƙoƙari ayi abinda ya kamata ni awajena Insha Allah ba matsala tunda dama zan kwana biyu saboda zan samu inji da tsohuwar kasan fatanmu da Adduarmu Allah yasa mu rabu dasu lafiya”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana yace.
“Hakane ƙwarai fatanmu da addu'ar mu rabasu da lafiya domin shi yafi al'khairi”.
Murmushi Baffa Jimeta yayi kana yace.
“Toh shine nake so in Zauna da ita Ni nan awajena duk abinda ake buƙata wanda uba zaiyiwa ɗiyarsa Insha Allah bazai gagara ba komai Ashirye muke Insha Allah”.

Cikin sauri Lamiɗo ya Girgiza kai kana yace.
“A'a Alh Muhammadu ai wannan hurumi nane don Allah dan Annabi kada kuyi min haka Khausar ɗiyace awajena tun tana wata uku nake tare da ita bata da bambanci da ɗiyan cikina inaji tamkar Ni na haifeta”.

Kallonsa Baffa Jimeta yayi cike da kamala yace.
“Anya Lamiɗo za ayi haka kuwa abar maka ɗawainiya?”.
Kai Lamiɗo ya Girgiza cike da dattako yace.
“Haba dai wace irin ɗawainiya kuma?,Meye aciki ai babu wani ɗawainiya acikin al'amarin nan”.
Numfashi Abba ya fesar kana ya fuskance su da kyau yace.
“Ni duka wannan aikin ma na ɓangaren Khausar da Moddibo zanso abarmin domin burin Jameeluna ne ni kungama yimin komai da kuka lamince zaku wanzar da wasiyyar sa bayan rayuwarsa”.
Jinjina kai sukayi kana ya cigaba da cewa.
“kungama yimin komai babu abinda zan iya yi muku tukuici dashi sai dai kubarni inyi dukkan abinda ya dace na fannin Auren nan”.
Murmushi Malam Arɗo yayi kana yace.
“Masha Allah wannan Auren yazo da al'barka Ubangiji Allah yasanya al'khairi”.
Zama Malam Liman ya gyara tare da faɗin.
“Muma kanmu duk al'amarin Khausar hakkinmu ne mu sauƙe”.

Cikin sanyin murya Abba ya kallesu kana yace.
“Ni dai dan Allah na nemi alfarma abarmin wannan aikin nayi”.
Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauƙe kana yace.
“To ai ba laifi duk zamuyi buƙatun ƴa mace suna da yawa”.
Jinjina kai Lamiɗo yayi kana yace.
“Ni dai nafi so abarmin komai na fannin Khausar”.
Dariya Malam Arɗo yayi idanunsa akan su yace.
“Lallai dai kam wannan ai sai dai ɗakuna uku za aware mata irin wannan lissafin.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Insha Allah wannan duk bazai gagara ba da ɗakuna da kuma duk abinda za'a buƙata zanyi”.
Numfashi Baffa Jimeta ya fesar kana yace.
“Allah ya temaka nima insha Allah nan da mako ɗaya zan koma”.

Jinjina kai Abba yayi kana ya gyara zamansa cike da farin ciki yace.
“Ai shi kansa Aliyu ma yanzu haka yana can ƙasar Marocco yana kulamin da ayyukan Company na to Auren ma bazata muke son yi masa”.
Murmushi sukayi jin sigar da Abba yayi magana Cike da farin ciki Abba ya cigaba da cewa.
“Idan yaso bayan an ɗaura auren da kaina zan Kai masa matarsa da izinin Ubangiji sai dai yaga mata dan yanzu ya tafi yana rayuwa shi kaɗai wasu sabbin damuwa zai sake sawa ranshi”.
Chapter 33 · 0% Book details