← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 150

Sashe 114

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Nigeria
Ana kiran sallan Magrib Hajiya Bunayya dake kwance tayi zumbur ta miƙe tsaye tare da sakin ƙara ta rugawa a guje ta nufi bathroom sabida wannan azabebben ƙaiƙayin da ta kwana dashi daran jiya da tayi ya dawo.
Ai kuwa susa takeyi harda hawaye data fito bazata wuce 15 minute ba ƙaiƙayin zai dawo sai kuma ta koma ciki.
Kafin zuwa lokacin sallan Isha har jini ke zuba sabida masifar
Kaikayawa datake.
Ganin Jini na zuba yasa ta mike azabure,
ruwan dumi ta hada a Baho kana tasa gishiri ta shiga ahankali tafara Jin masifar kaikayin na raguwa zaman minti goma tayi kana ta fito falon kan 2sitter ta zauna tana Maida numfashi wayarta ta janyo tayi dealing number Hajiya lami ringing biyu ana uku ta dauka tare da sallama cikin matsanamcin tashin hankali gami da tsoro Hajiya Bunayya tace.
“Hajiya Lami nifa nashiga cikin Masifa ƙaiƙayine yake addabata na faɗa Miki jiya kwana nayi banyi bacci ba da asuban farine na samu sauƙi yanzu gashi Maghiba nayi ƙaiƙayi ya dawo”.
Zazzafan Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauƙe tana gyara zama ta girgiza Kai tare da cewa.
“Ke dai bari Hajiya Bunayya nima Ina cikin tashin hankali tunda muka dawo yarinyar Nan ta fara Shan magani wannan abu guda² suka fara fitowa kamar masu Rai”.
Aruɗe Hajiya Bunayya ta dafe ƙirjinta da hannunta na hagu sai Kuma ta ɗago ta yarfe tare da faɗin.
“Yau mun shiga Uku wannan wace irin masiface ta tun kuramo?”.
Zazzafan Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauƙe kana tace.
“Hmmmm ni nama rasa kalar tunanin da zanyi Baki ɗaya hankali na atashe yake”.
Haka dai suka cigaba da tattaunawa.

Morocco Acan ɓangaren Khausar kuwa bayan an idar da sallar Isha'i Moddino ne da Dr Jameel cikin sauƙe numfashi Dr Jameel yace.
“Ruwanta ya ƙare yanzu zan sallameku ku koma gida sannan zan haɗa maka magungunanta”.
Numfashi Moddibo ya fesar tare da cewa.
“Toh shikenan Babu laifi”.
Sai Kuma ya juya Inda su Didi ke zaune Ganin Basu nan yasa ya Maida kallonsa Kan Dr Jameel yace.
“Ina su Didi?”.
Ɗan gyara tsayuwa Dr Jameel yace.
“Ni nace su tafi tunda zan sallameku”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Ok”.
Ya Ida maganar tare da tura ƙofan ɗakin da take kwance yana shiga Idanunsa suka sauƙa akanta tana zaune kan sallaya bisa alamu ta idar da Sallah Dr Ishaa na gefenta sai Kuma Rahama yayin da Dr Ishaa ke riƙe da Plate ɗin Indomie Wanda yaji yajii Dr Ishaa na miƙa mata kanta ta kawar gefe alamar bata so.
Kallonsa Rahama tayi kana tace.
“Yah Aleey kaga yanzu abinci kusan kala huɗu muka kawo mata Kuma duka taƙi taci”.
Ta ƙare maganar suna miƙewa ita da Dr Isha ɗin suka nufi ƙofar fita.
Shi kuwa Modibbo
Zama yayi gefenta tare da rungumeta aƙirjinsa sai Kuma ya manna Kansa a wuyanta yana shaƙan ƙamshin wajen yayin da ya Sanya hannunsa na dama yana shafa cikinta cikin wata sanyayyar murya Mai cike da aminci, tausayi jin ƙai gami da shaƙuwa yace.
“Minhaa cikin nan yana wahalar min dake sosai, nayi alƙawarin duk randa yazo duniya saina sumbacesa kana na Sanya mishi Albarka sannan nayi mishi adduar shiriya saboda wahalar min dake da yake yi”.
Jin haka ne yasa Dr Ishaa da Rahama saurin fita.
Bayan sun fita ta ɗaga kanta ta kallesa cikin wata kasalalliyar murya Mai sanyi tace.
“Waye ɗin Kuma?”.
Amintaccen murmushi ya sakar mata Wanda ya fito daga ainhin ƙoƙon zuciyarsa still Kuma hannunsa na cikinta yana shafawa yace.
“Minhaa kina da ciki fa”
Fuskanta ɗauke da mamaki ta kallesa sai Kuma ta lumshe Idanunta cikin kasalar daya game jikinta tace.
“Ciki Kuma?,Dama Ina da ciki ai”.
Ɗan shafa cikin yayi sai Kuma ya sassauta murya cike da matsanancin farin yace.
“Ba irin wannan cikin ba,Ciki na Haihufa”.
Cikin mamaki ta buɗe Idanunta dake lumshe ta kallesa giransa ɗaya ya ɗaga mata da faɗin.
“Wallahi dagaske”.
Cikin wani irin yanayi ta faɗa jikinsa hannunsa duka biyu yasa ya rungumeta itama hannunta tasa ta rungumesa tana Jin wani irin yanayi na tsananin farin ciki sai Kuma ta ɗaura hannunta asaman cikinta tana shafa muryanta ɗauke da farin ciki tace.
“Yah Mu'allim da gaske?”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Eh Wallahi da gaske”.
Ahankali ta Kuma ɗago Kai ta kallesa cikin sanyi tace.
“Allah yasa mu samu Mai kama da Ramadan idan ya girma sai mu bawa Momyna shi ya maye mata gurbin Ramadan”.
Sake rungumeta yayi ajikinsa tare da faɗin.
“Allah ya sauƙeki lafiya Allah ya ingantashi ya masa Albarka Amma Khausar bazan iya bada gudan jininmu ba kiyi haƙuri ba zan iya ba.
Ya karashe maganar cikin tabbatarwa da Kuma gaskiya da gaskiya ahankali tace.
“Baza ka iya ba?”.
Kai ya gyaɗa yana shafa cikinta ya fesar da numfashi tare da faɗin.
“Bazan iya ba,bazan iya ba kiyi haƙuri ban Miki alƙwariba kada ma in Miki ƙarya”.
Ɗan ware Idanunta dake lumshe kamar na Mai jin bacci tayi sai Kuma tace.
“Ido da ido?”.
Ɗan murmushi yayi Jin yanda tayi maganar cikin shaƙan ƙamshin ta yace.
“Um kada in Miki ƙarya ne”.
Tana sake shiga jikinsa ta ɗan cunno Baki tare da cewa.
“Ni Kuma Ina so idan na samu Mai kama da Ramadan in bawa Momy ya maye mata gurbinshi shiyasa naji daɗi”.
Cikin fahimtar har yanzu rashin Ramadan na ranta yasa yace.
“Toh shikenan in kin dage kin Haifa mana Dozen Mai yuwa in bawa Momy ɗaya”.
Zare Idanunta tayi tare da faɗin.
“Har Dozen?”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Eh mana”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Wannan ɗayan ma ga yanda nake ji”.
Cikin Jin taisayinta ya tallafe fuskarta kana ya motsa laɓɓansa tare da faɗin.
“In Sha Allahu zanyi Miki addu'a Kuma Ubangiji zai kawo Miki da sauƙi ”.
Sai Kuma ya tallafo ta tare da miƙar da ita yace.
“Tashi mu tafi sai mu biya restaurant idan akwai abinda kike so in siya miki”.
Kai ta girgiza cikin sanyi da game mata jiki tace.
“Nikam ma banajin yunwa cikina aƙoshe yake”.
Dai-dai lokacin Dr Jameel ya shigo Idanunsa akan Moddibo yace.
“Eh ko bata ci abinci ba bazata damu ba saboda ƙarin ruwan da aka mata zai taimaka.
Kuma in Sha Allahu duk bayan makonni zanke ɗan ƙara mata ruwa tunda dai bata samun cin abinci”.
Ya Ida maganar tare da miƙa masa ledan Magungunan kana ya ɗaura da cewa.
“Rahama tana jiraku amota”.
Ahankali Moddibo ya tsugunna ya tallafo ta kamar Baby muryanta cike da sanyi tace.
“Yah Mu'allim kabarni zan iya tafiya naji ɗan sauƙi fa”.
Kai ya girgiza tare da cewa.
“Um-um fa bana so”.
Ya faɗa yana gyara mata zama ajikinsa.

Baki sake Dr Jameel ke kallonsa tare da faɗin.
“Ikon Allah”.
Harara Moddibo ya watsa masa kana yace
“Ɗan sa ido”.
Murmushi Dr Jameel yayi tare da bin bayan sa suna Isa jikin Motar Dr Jameel ya buɗe masa gidan baya yasata kana Shima ya shiga Rahama na ɗaya gefen ya zama sun sata tsakiya kana Driver yaja.
Chapter 114 · 0% Book details