Sashe 96
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ita kuwa Ummi a hankali tacewa Khausar.
“Tashi kici abincin to”.
Cikin rawan jiki ta tashi zaune da taimakon Aunty Rukayya dake jera mata sannu.
A hankali suka kalli gefen da Hajia Bunayyah take sabida jin wani dogon tsakin da taja tare da juyawa ta bar falon.
Cikin zubda hawaye Khausar ta kalli Asma'u dake ta sakin murmushin tare da sune kanta.
Sai kuma ta kalli Dija ta kuna kalli Aseeya.
Cikin muryar kukan tace.
“Ummi ki ganifa dariya su Asma'u kemin”.
Da sauri Asma'u da Dija suka nufi cikin ɗaki sabida daƙuwar da Ummi tayi musu, Asiya ma bayansu tabi.
Hajja Nana kuwa cikin dariyar mugunta a fili tace.
“Yar nema ba cewa kikayi Ni Modibbo nake so”.
Cikin Shesh-sheƙan kuka murya na rawa tace.
“Wallahi na fasa, ni dai Wlh ku maidani wurin Mommy na ta kare mgnar da iyakar gskyar zuciyarta”.
Dariya ce ta kubcewa Aunty Hajara da Rukayya Hajja Nana da Innayi kuwa tafa hannu sukayi.
Ummi kuwa da sauri ta jawota jikinta.
Didi kuwa tea mai zafi ta fara haɗa mata.
A can ƙasa kuwa kwance kan 3sitter Lalla Hafsat ta samu Moddibo jikinsa cike da zazzafan kasala gaba ɗaya yayi so weak baki ɗaya bashi da kuzari saboda yayi abinda bai taɓa yi ba a tsawon rayuwarsa duk jikinsa amace yake ga wani fitinennen zazzaɓi da yakeji yana ratsa ƙasusuwan jikinsa, yayinda cinyoyinsa kuwa gaba ɗaya jinsu yake kamar ba nasaba, a hankali ya kishingiɗa da jikin Kujera yayin da ya manna kansa da jikin Kujeran yasa hannunsa duka biyu ya riƙe sabida zazzafan zazzaɓi yake ji wanda yasa har jikinsa ke rawa ga kuma ciwon kai wanda alamun kukanda yayi tayine da rashin bacci suka haifar masa da ciwon kan.
Cikin kula ta isa wajen tare da ɗaura hannunta na dama kan goshinsa jin hannunta agoshinsa ne yasa ya buɗe Idanunsa dake lumshe ya kalleta.
Cike da kulawa tace.
“Jikin ka zafi,Zazzaɓi kake jine?”.
Kai ya gyaɗa tare da maida idanunsa ya lumshe.
Cikin kulawa ta kalli fuskarsa tare da cewa.
“Subhanallah Sannu”.
Sai kuma ta juya ta kalli Ibraahim da yanzu yake shigowa tare da cewa.
“Yawwa Ibraahim dama yanzu Didi tace in faɗa maka kaje ka kira Dr Jameel yazo ya duba Khausar bata jin daɗi.
Shima Aleeyu gashi yanzu naji duk jikinsa da zafi ga yanda ya zama wani so week haka nan!”.
Jin abinda ta faɗa yasa Moddibo buɗe Idanunsa ahankali tare da faɗin.
“Dr Jameel kuma?.”
Kai ta gyaɗa mishi alamun eh.
Cikin ɗan rawan sanyin zazzaɓin yace.
“Ba Dr macene? Bana so Dr Jameel ya dubata, a nemi mace”.
Kai Ibraahim ya gyaɗa kana yace.
“Toh Shikenan bari naje na taho da Dr Jameel,Da Dr Isha in yaso Dr Jameel sai ya duba ka ita kuma sai mace ta duba ta”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana Ibraahim ya juya ya tafi...
Acan ɓangaren su Didi kuwa sauri Didi ta Sanya hannunta ta karɓi plate ɗin da Khausar ta ke miƙawa Hajja Nana mata alamar ta ƙoshi ita kuwa Hajja Nana harara ta watsa Khausar tare da cewa, nicema zan karɓi ragowar yunwarki ai shi daya jinyataki sai shi zaiyi jinyarki, Ni ko sannuma zaki samu a wuri nane,.
Murmushi Ummi da Didi sukayi, cikin kulawa Didi tace.
“Ki hutama Hajia ni zanyi jinyar ɗiyata”.
Murmushi suka kumayi baki ɗaya.
Ita kuwa Khausar a hankali ta koma baya tare da jingina kanta da jikin Kujeran ta lumshe manyan idanunta da suke ɗan kumbure kana sunyi ja saboda yawan kuka da rashin bacci.
Sai kuma ta fesar da sassayan numfashi sabida cikinta yayi mata tib saboda yanda abincin ya mata daɗi taci sosai musamman ma naman ya dahu yayi lugun gashi yayi yaji yadda take so.
Anutse Didi ta sake miƙa mata kofin tea mai kauri tare da cewa.
“Karɓi ki shanye”.
Sunkuyar da kanta tayi kana tace.
“Cikina ya cika”.
Ummi dake gefenta tace.
“Karɓi ki shanye ki kafa kai kawai ki shanye”.
Cikin lumshe idanu ta karɓa tare da kafa bakinta ta shanye tass.
A take zufa ya shiga tsats-tsafo mata tako ina.
Cike da kulawa Ummu ta kalleta tare da faɗin.
“Sannu”.
Kai ta gyaɗa tare da lumshesu so take ta gyara zamanta amman tsoron yadda zata motsa take, sabida har yanzu tanaji zogi.
Gajiya da zaman ne yasa ta ɗan kishingiɗa.
Ummi na gyara zamanta tace.
“Kwanciya kike sonyi?”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi kamar za tayi kuka ta gyaɗa mata kai tare da faɗin.
“Eh jikina ba ƙarfi,Ummi baki daya jikina amace”.
Numfashi Ummi ta fesar ganin yanda take ciccije baki alamar tana jin ciwo ajikinta tace.
“Toh ki kwanta”.
Kai ta gyaɗa tare da kwanciya.
Zama Didi ta gyara tare da kallon Hajja Nana dake cewa Innayi.
“Dan Allah nikam Innare yau dai kam ki faɗa mana meye ne sirrin Al'amarin tafiyar ku gari ya garire kuka je kuka zauna har wancan ƙasar”.
Kallon Didi Innayi tayi alamar kin amince in basu labari.
Kai Didi ta Jinjina tare da faɗin.
“Ki faɗa musu”.
Zama Innayi ta gyara tare da juyawa ta fuskancesu baki ɗaya kana ta fara basu labari kamar haka...
Masarautar Mouley ta kasance Masarautace mai girma da ƙarfin iko kana da matsayi a yankin Africa baki ɗaya, sannan su su Abualeey sarki Youseep kenan su goma ne acikin Mahaifin su suna da ƴan Uba su kuma su huɗu ne kaɗai acikin Mahaifiyarsu maza biyu mata biyu Sarki Youseep Muhammad Mouleey sai Haroon Muhammad Mouley, sai Salma Mouley da kuma yar autarsu mahaifiyar Dr Jameel.
Sannan Mahaifiyarsu ta kasance itace Uwar gida mahaifinsu tun yana da rai yayii Murabus aka ɗauki mulki aka bawa Sarki Youseef kasancewar shine babba sai suka fara fuskantar ƙalubale ƴan Uba sukayi ca akansu bayan yayi Aure dai duk abin bai bayyana sosai ba, saida suka fara haihuwa, aihuwarsu ta forko aka samu, Lalla Khadijah lafiya lau aka raineta har aka yayeta. Kana aka haifi Lalla Hafsat lafiya lau itama aka yayeta, amma tunda aka fara haifan ƴaƴa maza sai ya zama duk Namijin da aka haifa baya wuce kwana arba'in a duniya tun yana kwana talatin zuwa arba'in ɗin ake sace yaro, baya wuce kwana uku sai a tsinci gawar yaro a tsakiyar fada, an kashe shi.
Masarautar Mouley gaba ɗaya ta shiga ruɗanin wannan al'amari, sai da Gimbiya Didi ta haifi ƴaƴa maza uku duk ana kashe su kafin ta haifi Moddibo da aka haifi Moddibo kuma dai-dai lokacin Mahaifin Moddibo ya kamu da ciwo ya zama kamar irin Kiɗimamme haka ya rasa gane Ainihin abinda ke damunsa har aka ɗauki Sarauta aka maida ita hannun Ƙaninsa.
Ƙanin shine ayanzu yake kwance kusan shekaru ashirin da biyar bashi da lafiya.
Sanin danayi ana haifar yara basa wuce kwana arba'in ake ɗauke su yasa nayi niyya taimakon uwar ɗakina da uban ɗakina da kowa yasan yanayin jikinsa akwai alamun sa hannun magauta.
Kasan cewa nice Jakadiyar Didi yawan zama da ita da yaranta da take musu fulatanci yasa na iya yaren sosai tunda alokacin ma munyi kusan shekaru goma sha uku tare, dan a lokacin shekarun Lalla Khadijah 12 cib Hasfat 10. Haka yasa nayi niyyar ɗaukesa naje wani waje nayi rayuwa dashi ya zama zakaran gwajin dafi kafin na dawo dashi shiyasa na rubuta wasiƙa sannan na ɗauki sandarsa wanda tsarin Masarautarne duk Amaryar da aka aura ranar da akayi First night ɗin ta idan aka sameta cikakkiyar budurwa za'a bata wannan sandar Amma sandar za'a ajiyeta aɗakin Tarihi na Masarautar inda ake ajiye ƙyallayen budurcin matan masarautar da sarautar ke hannunsu, sai randa ta haifi ɗa Namiji ya kai shekara ɗaya aduniya za'a ɗauko shi akawo mata shi matsayin sandan godon sarautar, dan haka ne na ɗauki sandar sannan na shiga ainihin ma adanar masarautasu kasancewata amintacciyar Jakadiya yasa nasan duk shiga da fitan Masarautar shiyasa na shiga na ɗibi Silalllan Gwal ɗinna kafin na rubuta wasiƙa da yi musu cikekken bayanin ba sace ɗansu akayiba ni na ɗauleshi na tafi dashi kuma in dai yana raye ina raye wata rana zan dawo dashi.
Na basu cikekken tabbacin Cewa zan dawo musu da ɗansu in Sha Allah su kwantar da hankalin su nayi musu alkawarin zan kula dashi sannan zan bashi tarbiyya za kuma yi mishi duk abinda uwa da uwa zasuyiwa ɗan su bazaiyi kukan rashinsu a kusaba susa aransu zan dawo musu da ɗan su lokacin da yafi ƙarfin magautan su a kuma lokacin da sukafi buƙatar sa kusa dasu...