← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 150

Sashe 82

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta sauƙe numfashi tare da sa hannunta ta dauki goran ruwan dake gefenta wanda yake zuba nason sanyi, a cup ta zuba mishi ruwan tare da miƙa mishi.
Da sauri ya zura mata idanunshi dake cike tab da hawaye, ba musu yasa hannunshi ya amshi cup din tare da kaiwa baki, lokaci ɗaya ya zuƙe ruwan tare da ajiye cup din.
Didi kuwa da Abualeey duk ido suka zuba mishi Ashshe kuwa da sauri tace.
“A'a Aleey ko dai kaima irin su Hafsat ne da yaji ke gigitaku”.
Juyowa yayi ta kalleta da idanunsa da tamkar hawayen zasu zubo, sai shafa ƙeyarsa zuwa sajensa yake tamkar ba gobe.
Juyowa sukayi baki ɗayansu suna kallon Khausar data ƙara mishi ruwan sanyi tare da cewa.
“Issah”. Sai kuma tajanye plate ɗin daga gabanshi tare da turawa Ibraahim da har ya cinye nasa cikin ɗan sanyi tace.
“Yayanka kam in yaci wannan zai iya sume mana a nan”.
Cikin dariya Ibrahim yace.
“Kai haba dai”.
Lalla Khadijah cewa tayi.
“Yah Salam Aliyeeh ashe baka cin yaji kuma bazama faɗa minba”.
Ina bazai iya mgn ba yanzu sai sauƙe numfashi yake da shan yaji a hankali tare da bin Khausar da kallo mai cike da mamaki ya sani duk duniya J ɗinshi ne kaɗai yake iya gane dukkan motsinshi koda ko baiyi mgn ba, toh ya akayi ta gane duk halin da yake ciki”.
Didi kuwa cikin murmushi da tsareshi da ido ta zuba mishi abincin da akeyi dan Abualeey ta miƙa mishi tare da cewa.
“Sak komai nashi na Abbanku ne, wato har yadda idanunsa sukayi haka nan idanun Abbanku keyi matuƙar dai yanacin yaji, kuma wai bazasu faɗaba, yanzu in badon Allah ya baka mace Mai lura da kulaba ya zakayi kenan”.
Shi dai sai shafa saje yake dan har yanzu baya jin zai iya mgn.
Abualeey kuwa cikin kulawa yace.
“Daga yau kada ku sake bashi abincin da Rahama ta dafa, dan na lura ita harshenta ya mutu baya jin yaji ita da Ibrahim da Khadijah”.
Dr Jameel kuwa dariya yai tare da cewa.
Ai ni ko gigin bacci nake bazanci abincin da Ibrahim yaci ba yaro kamar maye”.
Sai kuma duk suka juyo kan Modibbo jin Khausar na ce Mushin.
“Isah yar diyam fahin". Kai ya ɗan jujjuya mata zuwa yanzu duk hawayen sun ɓace sai dai zirin idonshi da yayi ja.
Sannu suka rinƙa jera mishi Rahama kuwa kamar zatayi kuka tace.
“Allah ko Abualeey ban san baya cin yajiba ni yamin irin Yah Ibraahim ne shima, kuma in Sha Allah daga yau cikin abincinka zai rinka ci".
Sai yanzu ya ɗan fesar da numfashin kana yayi ɗan murmushi gefen baki tare da cewa.
“Kada ki damu Rahama abincinka yayi”. Cikin murmushi jin daɗin ya yaba mata ta kuma ce mishi sannu.
Zakariyya ne yace.
“Ni dai banji wani yajinba”.

“Yoh dama kai zakaji ne tunda kaima irin Ibrahim ne”.
Cewar Kalla Hafsat.

Daga nan suka ci gaba da cin Abinci shi kuwa a hankali yake cin abinci yana kallon Khausar ta ƙasan ido da mamkin lamarinta.

Bayan sun gama cin abincin ne duk suka dawo tsakiyar falon da sauri Dr Jameel yabi bayan Abualeey dake shirin fita.
“Cikin girmama yace Abualeey, ka kirani”.
Cikin kulawa da son Dr Jameel daya kasance ɗane ga marigayi Aminin Abualeey wanda bashi da kamarsa a duniya a hankali yace.
“Eh dama cemaka zanyi kuɗauki bakin nan ku fita dasu da kai da Ibrahim da Zakariyya ku kaisu su ɗan ga gari, dan yau saura kwana biyu zasu koma Ibrahim da Haroon zasu fita da mazan kai kuma sa Zakariyya ku fita da matan”.
Cikin girmama yace.
“Toh”. Sai kuma yaci gaba da binshi ganin hakane yasa Abualeey juyowa ya ɗan kalleshi tare da cewa.
“Da mgn ne”.
Cikin yin ƙasa da kai yace.
“Eh Abualeey”. Daga nan kuma ya kwashe labarin Asma'u ya bashi ya ɗauka da cewa.
“Wlh kuma Abualeey ina sonta har raina”.
Cikin tsanananin jin dadi Abualeey yace.
“In sha Allah kuwa ka sameta, kada ka damu kaje abunka sanyi mgn da manyansu”.
Daga nan ya juya ya koma ciki.

Shi kuwa Abualeey daga nan kai tsaye wurinsu Abban Jameel ya nufa, bayan yayi musu dukkan bayanin sosai abin yayi musu daɗi domin dama tun jiya Zakariyya kam yayi mishi mgnar Aseeya a cewarsa ya lura Modibbo ɗan tsarine.

Lamiɗo kam daga wurin ma yace in dai Aseeya ta yarda ya bawa Zakariyya ita.
Domin ranshi ya cika da farin ciki ya kuma gamsu da kamalarsu yasan ko ba komai Allah yayiwa Asiya zaɓin mafi Al'khairi a gareta.

A can falon kuwa cikin jin daɗi Dr Jameel ya faɗawa Zakariyya da Ibraahim yadda sukayi da Abba.

Shi kuwa Modibbo a hankali ya kalli Didi tare da cewa bari inje wurin Abban Jameel.

“Ka gaidashi”.
Tace mishi tana mai miƙawa Khausar hannu alamun tazo.
Shi kuwa Modibbo hannunshi ya miƙawa Dr Jameel tare da cewa.
“Zo muje wurin Abba yaga mai kama da Jamilunshi”.
Dr Jameel na miƙewa yace.
“Ai Innayi ta kaini wurinsu jiya, yayi ta kuka saida nima ya sani kuka”.
Ya ƙare mgnar yana bin bayan Modibbo.
Yayinda Zakariyya kuma ya kamo hannun Ibrahim tare da ce mishi.
“Zo ka rakani wurinsu Innayi”.
Toh yace kana ya miƙe suka tafi can.

Shi kuwa Modibbo bisa jagaroncin Dr Jameel , sukaje Side dinsu Abba.

A falo suka samu Lamiɗo da kuma Bappa Jimeta da Malam Arɗo.
Sai Haiydar dake can kan danning table.
Ganin Modibbo da Dr Jameel ne yasa ya sauko da sauri tare da isowa tsakiyar falon.
Shi kuwa Modibbo cikin nitsuwa suka gaisa dasu Lamiɗo.
Bayan ya gaidasu ne kuma ya ɗan kalli Malam Arɗo dake cewa.
“Yanxu dai ya tabbata kun guji makaranta kenan?”.
Yayi mgnar yana kallon Dr Jameel da tamkar M Jameel ne ke zaune gabansa,
Murmushi Dr Jameel yakeyi tare da binsu da ido ganin yadda suke kallonsa cike da rauni.
Shi kuwa Modibbo
Kai ya ɗan juya tare da miƙawa Haiydar hannun, sai kuma ya juyo kan Malam Arɗo tare da cewa.
“In sha Allah nan kusa ai zamu dawo”.
Murmushi Abba Jameel dake fitowa daga cikin ɗaki yayi tare da cewa.
“Uhmmm Aliyu kace dai za kuje, amman ai komawa kam banga alamaba”.
Ya ƙare mgnar da zama kusa dasu tare da shafa kan Dr Jameel dake cewa Abban.
“Barka da safiya Abba na”.
Cikin zuba mishi ido da ta'ajjudin kamannin daya zarta zaton mai zato yace.
“Barka dai Jamilu na”.
Sai kuma ya ɗanyi shiru tare da sunkuyar da kai dan muryarshi data fara rawa.

Moddibo kuwa a hankali ya ɗan taune lips inshi ta gefen tare da gyara zamanshi ganin Abban Jameel ɗin ma ya zauna tare da cewa.
“Yanzu Mai martaba da Waziri da Galadima suka fita nan”.
Cikin sanyi Modibbo ya gyaɗa mishi kai.

“Sunzo mun tattauna kan lamarin Jameel da Asmau da kuma Asiya da Zakariyya Alhamdulillah kuma mun tsaida matsaya.”
Cikin sanyi Modibbo ke jinjina mishi kai
Sai kuma ya kalli Haiydar dake cewa.
“Yah Modibbo ina Adda Khausy”.
A hankali yace.
“Tana wurin Didi”.

“Tun ɗazu nake ta kiranta bata ɗaukaba, Mommy ma tace min tai ta kiranta bata ɗauka ba”.
Cikin kauda kai yace.
“Eh wayar ce tana hannuna”.

Kai Haiydar ya jinjina tare da cewa.
“Ina son zuwa wurinta”.

“Toh sai na tashi tafiya”. Ya Bashi amsa.
Daga nan kuma Haiydar ɗin ya nufi wata ƙofa yana cewa.
“Bari inje in canza kaya dan ance zamu fita”.
Da ido kawai suka rakashi.

“A wanne hotel ne ka sauka da kazo”. Abban Jameel ya jefawa Modibbo tambayar.
Cikin girmama yace.
“Sofiyel Mouley Youseep hotel na sauka”.
Cikin sauri Dr Jameel yace.
“Hotel ɗin Abualeey ne ai”.
Kai Abba ya jinjina tare da cewa.
“Batun kayanka da kuma takardun aikinmu na Companyn'ne dama yasa nake son muje mu ɗaukosu”.
Cikin sauri Dr Jameel yace.
“Room no ɗin kawai zai gaya mana Abba, idan mun fita zamuje mu ɗauko, komai barema da Ibrahim zamu fita da wanda komai na Hotel ɗin a hannunsa yake”.
Cikin jin daɗin abin yazo da sauƙin Abba yace.
“Toh Alhamdulillah”. Sai kuma ya ɗan gyara zamanshi tare da fuskantarsu da kyau a
hankali yayi gyaran murya tare da yiwa Dr Jameel wani irin kallo mai cike da sonshi, ganin ko zamanshi yadda Jamilunsa ke zama a gabanshi haka ya zauna.
Cikin danne raunin sa ya kira Modibbo.

Shi kuwa Modibbo cikin nitsuwa ya amsa tare da takwashe sawunshi yayi ƙasa da kai.
Abba kuwa cike da sanyi ya fara bashi labarin wasiyar J ɗinsa, da kuma yadda sukayi ta fafutukar samun auren ya kasance daga forkon har ƙarshe sai dai abinda ke gefen Khausar da bai saniba.
Gaba ɗaya jikin Modibbo tsuma yakeyi duk da kafiyarsa na son hana kukanshi subcewa ya gaza.
Gaba ɗaya mutuwar J ɗinsa ta dawo mishi sabuwa dal, ashe J ɗinsa ne ya haɗa aurensa da Khausar kenan da gaskene lokacin da yake cewa yayi mishi zaɓin matar aure, ashe Khausar ya zaɓa mishi.
Wani irin maraitaccen kuka ne ya subce mishi sabida tunowa da wasu abubuwa masu tarin yawa wanda yake da yakinin gsky ne a zuciyar J ɗinsa kenan Sadaukarwa ce J ɗinsa yayi masa, Sadaukarwar da yayi ta ƙoƙarin yiwa J ɗinsa tsawon shekaru na nuna baison abinda yakeso a nashi ran sabida fahimtar J ɗinsa naso yasa yayi ta cusawa ransa nesanta da muradinsa da J ɗinsa ya mallaka.

Malam Arɗo ne ya ɗanyi gyaran Muryar tare da cewa.
“Kayi haƙuri Modibbo tun jiya muke son yi maka bayani amman tunowa cewa zamu fama maka ciwon rashin Jameel ne yasa muka gaza hakan".
Sai kuma ya ɗan yi shiru ganin yadda Modibbo ke wani irin Shesh-sheƙan mai fitowa daga ƙasan zuciyarsa har numfashinsa na cizgewa.
Cikin sanyi lamiɗo ya dafa kafadarshu tare da cewa.
“Kayi haƙuri Modibbo addu'a zakayiwa Jameel”.
Abban Jameel kam Ina ya gaza cewa komai shima sai kukan yake.
Chapter 82 · 0% Book details