Sashe 135
Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tsaye suke a abakin gate kallon Asma'u Khausar tayi tare da cewa.
“In sha Allah daga nan zamu wuce gidan Addah Asiya”.
Cikin sanyin Asma'u tace.
“Wallahi nima ina son zuwa”.
Dr Jameel da baki ɗaya nutsuwarsa ke kanta tace.
“Ki bari idan kin sake warware wa in Sha Allahu zan kai ki”.
Langwaɓar da kai tayi tare da cewa.
“Toh ba ance kwanan nan zasu tafi ba?”
Kai Khausar ta girgiza tace.
“A'a ance dai kwanan nan zasu koma kuma naji ance anan zai gama hutunsa”.
Kai Asma'u ta gyada tare da cewa.
“Toh shikenan In sha Allahu kafin su tafi zamu sake zuwa mu wunin mata ko?”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da faɗin.
“Eh in sha Allah”.
Daga nan sukayi sallama suka fita.
Suna fita kai tsaye gidan Asiya suka nufa.
Dai-dai lokacin kuma Asiya ce da Dr Zakariyya ke zaune a falo suna hira jin ana knowking yasa Dr Zakariyya miƙewa ya buɗe.
Khausar ce agaba Asiya na ganinta ta miƙe da gudu taje ta rungumeta Moddibo kuwa cikin Murmushi yace.
“Addah Asiya abi ahankali”.
Murmushi tayi kana ta riƙe hannun Khausar tare da cewa.
“Adda Khausy tun shekaran jiya nake ta zuba ido ina so in ganki ban ganki ba”.
Cunno Baki Khausar tare da kallon Moddibo da suke magana da Dr Zakariyya tace.
“Yah Mu'allim ne ai”.
Murmushi Moddibo yayi kana ya marairaice fuska yace.
“Komai dai Ni ko wani laifi nawa ne komai ace Yah Mu'allim toh naji na ɗauki laifina”.
Cikin narke fuska tace.
“Ato ai kasan hakane”.
Murmushi yayi.
Asiya kuwa kitchen ta shiga ta kawo musu abubuwan motsa baki taɓa ka lashe.
Khausar ce dai ta ɗanci Amman shi Modibbo ko ruwa bai sheba.
Bayan sun gama hira kusan karfe goma na dare sukayi musu sallama suka tafi.
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya Khausar na samun kulawar Uwar mijinta da danginsa Innayi ma na iya bakin ƙoƙarin ta kana suna waya da Momy, Ummu, Hajja Nana, akai-akai hakama Aunty Ruƙayya da Aunty Hajara.
Bayan sati Uku Asma'u da Khausar suka je gidan Asiya suka yini mata bayan sati ɗaya da zuwa su Asiya da Dr Zakariyya suka koma Indi'a...
Washe garin ranan da suka tafi a Nigeria Amina ce zaune a falo yayin da Hajiya Bunayya ke tsaye tana bubbuga ƙafa tare dasa hannunta tana bubbuga mazaunanta jin yanda masifaffun tsutsotsin nan ke addabar rayuwarta wanda da ƙanane suke fita yanzu kuma manya ne Amina kuwa Alhamdulillah bisa ga duk kan alamu jikinta yayi sauƙi sosai kasancewar har ta fara maida ƴar ƙibanta alamun ta samu sauƙi sosai-sosai.
Ahankali ta tallafe haɓarta tana kallon Mahaifiyarta ta zuwa yanzu ta fahimci tsutsotsin nan sun haukata mata mahaifiya saboda ko yaushe ƙoƙari take ta cire zaninta ta yasar ita take ƙoƙarin hanawa kamar dai yanda yanzu ma take ƙoƙarin cirewa.
Cikin sauri Amina ta miƙe cikin rauni da zubda hawaye tace.
“Dan Allah Umma kada ki cire zanin”.
Alalace ta juya ta harareta tare da cewa.
“Kada in cire zani in zauna kenan su cinyeni ke kin san abinda nake ji kuwa? baki ga tsutsotsin nan yanda suke cina ba ko kuma dan ke kin samu lafiya bake kike shan azaba yasa zakice haka, ai dacan da kike zazzaro harshe waya ce ki daina”.
Ta ƙare maganar tana kwayewa Amina ɗuwawunta tare da cigaba da faɗin.
“Ki ga fa”.
Cikin sauri Amina ta runtse idanunta kana tace.
“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un”.
Ganin manya-manyan tsutsotsin dake cin Mahaifiyarta cikin matsanancin tashin hankali ta saki ihu dai-dai lokacin da Lamiɗo ya hau Farandar falonta saboda yanda Amina tayi ta kuka daren jiya akan cewa ya kai Hajiya Bunayya asibiti cikin sauri ya karaso Falon yayin da Momy ke biye dashi abaya ganin haka yasa Momy saurin ɗaukan zanin ta daura mata.
Ga mamakinsu sai suka ga Hajiya Bunayya ta fara buge-buge tare da ɗaga hannu zata daki Momy cikin sauri Lamiɗo ya kamo hannayenta ya riƙe.
Dariya ta fara ƙyalƙyalawa alamun hauka ta tabbata tuburan ziraran.
Kuka sosai Amina ta fashe dashi.
Dai dai lokacin Haiydar da Sulaiman suka shigo ganin haka yasa Sulaiman rungume Haiydar suka fashe da kuka cikin rauni da shesh-sheƙa Sulaiman yace.
“Haiydar kaga Ummana yanda ta koma”.
Shiru yayi ganin yanda take ƙoƙarin ƙwace hannunta Momy kuwa duk da yanda take ƙoƙarin kawo mata duka sai da ta jawo zanin ta ɗaura mata ta baya.
Wani irin abu ta fara kamar rawa kamar tsalle alamun dai hauka Muraran ziraran.
Kai Lamiɗo ya girgiza tare da juyawa ya kalli Gimbiya Dadu da tazo wacce hayaniyar dake faruwa ne yasa taxo tana shigowa taga Hajiya Bunayya keyi ta saki ƙara ta faɗi awajen atake a wurin ɓarinta ɗai ya shanye tun, kafin aɗagata ɓarin jikin ta ya mace.
Cikin gigita da Kiɗima Lamiɗo ya kalli Haiydar kana yace.
“Haiydar jeka kira min bappanka”.
Cikin rawan jiki Haiydar ya juya ya fita yaje ya kirasa.
Hajiya Bunayya kuwa ƙoƙarin duka take kai masa ɗankwalin kanta ya since ya ɗaure hannunta.
Dai-dai lokacin da ƙanin nashi ya shigo cikin tashin hankali Lamiɗo yace.
“Yusuf ka ɗauki Hajiya Bunayya ka Kaita Sycatry na cikin Taraba”.
Cike da damuwa yace.
“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un Sycatry kuma?”.
Araunane Lamiɗo ya kalli Hajiya Bunayya dake wani irin fusga tana ƙyalƙyala dariya yace.
“Toh ya zamuyi Yusuf?Bata da wani amfani daya wuce mu Kaita Sycatry dama arayuwa duk abinda mutum zai yi yabi ahankali”.
Kuka sosai Bashir keyi tamkar ransa zai fita Lamiɗo kuwa cikin sanyi ya cigaba da cewa.
“Gashi tun ba aje ko ina ba Ubangiji Allah ya haɗa mata sakamakon aikin ta ya liƙa mata su atsakiyar kanta sun zame mata matsala, muma sun zame mana matsala tun da komai yaya zukatanmu nada Imani zamuji tausayinta”.
Cikin azabebben kuka Amina ta kalli Lamiɗo tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Ummana yanzu Sycatry za'a kai ta?”.
Cikin sauƙe zazzafan ajiyar zuciya yace.
“Yanzu Amina anan za'a barta tayi ta hauka?,Mutane suna kallonta tana since zani idan mun barta anan cikin gari zata shiga tayi ta yawo tana bayyana tsaraici kinga ai baiyi ba”.
Cikin matsanancin kuka da shesh-sheƙa Amina ta gyada kanta tare da faɗin.
“Hakane kam Abba”.
Alh Yusuf kuwa janta yayi ya sata a mota.
Lamiɗo kuwa sai alokacin yaje ya ɗaga Gimbiya Dadu da tuni ta sume.
Cikin kiɗima ya Kaita asibiti, inda duk binciken da akayi likitoci suka tabbatar masa da cewa ta kamu da ciwon ɓarin jiki awanna ranan dai haka suka yini a asibiti koda ta farfaɗo gefen bakinta ya karkace tana magana yawu na zuba cikin zubda yawu da magana irin na wanda suka samu shanyewar ɓarin jiki tace.
“Ohhh nima dai ga karshena nayi ta cin ƴaƴan mutane ina ta zubar da cikin ƴaƴan mutane idan naga ɗan da yamin maiƙo in lashe in naga mai ciki inlamushe”.
Cikin sauri da matsanancin mamaki da tashin hankali Lamiɗo ya rufe mata baki tare da cewa.
“Dadu Ki daina faɗan haka dan Allah ki dai na faɗa ”.
Bakinta na tsulalar da yawu tace.
“Ai dole in faɗa ayyukana ne in ban faɗesu ba ya zanyi.
Ni na aikata kana ganin kamar zargina mutane suke da suke cewa Ni mayyace.
Tabbas ni mayyace da gaske amma kai Allah ya tsare ka da ƴan Uwanka dama nida ƴar uwata siya mukayi bawai tsatson mu bane”.
Araunane Lamiɗo yace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un hasbunallahu wani'imal wakin”.
Haka yaita addu'oi wai ko zai samu ta bar tone-tone ta kama addu'a amman a banza.
Washe gari da safe aka sallamosu a asibiti suka dawo gida saboda Likitoci since babu abinda zasu iya mata dole yasa Lamiɗo ya nemo masu aiki wanda zasu riƙa kula da ita.
Yayin da Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ke can asibiti suna can suna buga wash-shagare wallensu a haukace.
A kuma dai-dai wannan ranan Khausar ce zaune a falonta kunnenta maƙale da waya tana hawaye cikin rauni tace.
“Yanzu Momy haka Umma da Hajiya Lami suka dawo?
Ita ma Gimbiya Dadu haka ta dawo?”.
Cikin sanyi da damuwa Momy tace.
“Wlh Khausar am ai rayuwar nan mu bita a sannu”.
Cikin zubda hawaye Khausar ta gyara zamanta tare da cewa.
“Dama Momy ina faɗa Miki kallon da Gimbiya Dadu take yimin yana ban tsoro kullum cikin kareta kike”.
Ajiyar zuciya Momy ta sauke kana tace.
“Toh Khausar baka da tabbaci ka isa ka tuhumi mutum ne?
ba kiji Manzon Allah (S.A.W.)yace _Azzhana zhambu Walau kana haƙƙun_ ai zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya amma yanzu da taxo ta faɗa da bakinta ai taga *SAKAYYAR ta*”.
Kai Khausar ta jinjina tare da faɗin.
“Allah ya rufa mana asiri ya kare mu”.
Dai-dai lokacin Moddibo ya shigo ganin tana hawaye yasa yayi saurin shigowa ciki, tare da zama a gabanta kana ya sanya hannunsa ya share mata hawaye.
Yana mai kallonta, sai kuma ta ɗan sauƙe ajiyan zuciya, ganin yanda ya zuba mata idanu yasa tace.
“Toh Momy sai anjima”.
Kana suka katse kiran.