← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 150

Sashe 108

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa Aunty Ruƙayya tayi tana kallon Momy tace.
“Toh nima zan tafi”.
Kai Momy ta gyaɗa kafin duk sukayi mata Sallama suka tafi bayan ta basu komai na biki.
Acan ɓangaren Mazan bayan sun kammala Breakfast Lamiɗo yai musu jagora suka tafi gidan su Malam Ahmad sukayi tambayar Auren Asma'u wa Jameel gaba ɗaya malam Ahmad da yaji lbrin Jameel sai da yashiga ruɗu da tashin hankali jin tsananin kamarsa da Jameel bayan sunyi tambaya sun dawo da tabbacin Anbasu kasancewar Lamiɗo ne ya musu Jagoranci.
Bayan sun dawo Hajja Nana, Hajja Umma Baffa Jimeta suka tafi Jauro Yaya daidai lokacin da Motarsu Hajja Nana ya fita akuma dai-dai lokacin
Text ɗin Yah Ali ya shigo wayar Dija, cikin tsananin mamaki take karanta sakon nasa.
“Tun jiya da dare jikina da zuciyata suke gaya min kun dawo Nigeria kun shigo jihar Adamawa sabida wani irin ni'imtaccen ƙamshi da isaka mai sanyi da nakejin wanda ya tabbatar min kin kusa dani, shiyasa nake fata da burin in ɗaukeki daga Jauro yaya in dawo dake kusa dani a matsayin matar aurena in kin amince Dija”.
Wasu irin tagwayen murmushi take saki ba ƙaƙƙautawa ta karanta sakon a karo na uku kana ta turawa Khausar tare dayi mata bayanin wanda ya turo saƙon da kuma neman shawara, haka dai sukaci gaba da tafiya.

Motarsu Hajiya Lami da Samira Sani yayi Parking sunzo wajen Hajiya Bunayya dan jin cikekken bayanin da tsara batun tafiyarsu.

Zuwa lokacin su Abualeey sun gama komai Lamiɗo ya musu Jagoranci zuwa gidan Abban Jameel Lokacin da Hajiya Turai da Hajiya Karima suka kalli hoton Dr Jameel dasu Abban Jameel da kuma lbrun kakannisu da Jameel da kuma lbrin dangin Modibbo sosai suka shiga mamaki, musamman kamannin Dr Jameel da kuma M Jameel abin yayi masifar basu mamaki ya kuma girgiza su a washe gari suka je Juuro yaya suka gaida Hajja Nana.

Kwanan su biyu acikin Taraba suka koma Adamawa kwana ɗaya sukayi a Adamawa ya zama kwanan su uku sukayi suka shirya komawa Morocco...

A Morocco kuwa rayuwa ta fara tafiya Khausar da Moddibo sun fara samun shaƙuwa na musamman wanda su kansu basu fahimci haka ba aranan dasu Abualeey zasu dawo Khausar ce zaune a falon Didi bayan sun gama girki wanda bisa alamu sun yiwa baƙi da zasu dawo ne sun gama komai sun shirya a dining.
Ahankali Didi ta kalli Khausar tare da cewa kizo ki zauna kici abinci”.
Anutse Khausar ta ɗago Idanunta tare da shafa cikinta kana tace.
“Didi na ƙoshi bana jin yunwa”.
Juyawa Didi tayi tare da kallon Moddibo dake zaune gefe da system a gaban shi bisa alamu aikin da ya shafi campanny Abba ne yake duba, cikin kula tace.
“Taci abinci tunda gari ya waye?”.
Kai ya girgiza cikin alamun damuwa ya kalli Didi kana ya maida kallonsa kan Didi yace.
“Babu abinda taci ni kaina bansan meyesa bata son cin abinci ba kuma ba haka take ba”.
Langwaɓar da kai tayi tare da cewa.
“Nifa bana jin yunwa nasha tea ɗaxu”.
Didi na girgiza kai tace.
“Toh tea Abinci ne? Khausar ai tea ba Abinci bane.
Rahama maza ɗebo min abinci a plate”.
Miƙewa Rahama tayi ta ɗebo abincin ta kawo mata aplate karɓan abinci tayi tare da kallon Khausar tace.
“Sa hannu kici”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“Allah Didi banjin yuwa cikina aƙoshe yake”.
Kai Didi ta girgiza kana tace.
“Bana son zamanki da yunwa Khausar koda bakya jin yunwa ki karɓa kici”.
Kai ta sunkuyar ta ɗauki cokali saboda batason yiwa Didi gardama.
Moddibo kuwa ahankali ya ɗago ya kalleta tare da faɗin.
“Wallahi Didi tunda gari ya waye bata ci abinci ba idan kinga taci abinci sai na matsa mata dole² bansan meyesa ba”.
Dai-dai lokacin Ibraahim dake shigowa yace.
“Toh ko dai bata da lafiya ne?,Idan baki da lafiya ne mu kaiki asibiti aje aduba ki”.
Tana cakalan abincin tace.
“Wallahi lafiyata ƙalau bana jin komai abinci kuma ina ci ina yawan shan Fruit nake gama shine yake hanani cin abinci”.
Ajiyar zuciya Didi ta sauƙe tare da cewa.
“Toh yanzu dai kici bari kuma akawo miki fruit ɗin”.
Cokali biyu zuwa uku ta sake tsakura kana ta tura plate ɗin gaban Rahama tace.
“Toh muci mana”.
Ɗan ware Idanu Rahama tayi tare da faɗin.
“Ai kina gani ɗazu naci”.
Sake langwaɓar da kai tayi tace.
“Ni ma Wallahi na ƙoshi”.
Cikin sauƙe numfashi Didi tace.
“Kici mana Khausar am”.
Ahankali ta sunkuyar da kanta tare da faɗin.
“Allah Didi na ƙoshi”.
Kai Didi ta gyaɗa kana tace.
“Toh shikenan Rahama jeki ɗauko mata fruits”.
Kai Rahama ta gyaɗa sai kuma ta miƙe ta dauko mata wani kekyawan Bowl wanda ke cike da
Inabi, Apple, Banana, Pineapple, Water millo wanda yake a yayyanki an yarayarɗa madara akai.
A hankali ta gyara zamanta tare da ɗaukan fork ɗin jin Didi na cewa.
“Bismillah”. A hankali tai Bismillah tare da soka yankan kankana kana ta buɗe bakinta a hankali tasa, lumshe udanunta tayi sabida zaƙi da garɗin madarar da ya game mata baki, a hankali take taunan kankanan tare da haɗiyewa, sai kuma tattare ƴaƴan kankanan ta haɗesu gefen bakinta.
Shi kuwa Modibbo ta gefen idonshi yake kallonta,
yanka na biyu ta kuma kaiwa bakinta ba tare da ta haɗiye ƴaƴan kankanan ba, sai kuma ta sake harhaɗe ƴaƴan kankanan ta tarasu gefen bakinta sabida bata iya haɗiyesu, sai kuma ta jujjuya kwayar idanunta alamun tana neman wurin da zata zuba ƴaƴan kankanan ne.
A hankali ya miƙo mata hannunshi tare da buɗe mata tafin hannunshi, cikin fidda idanunta waje ta ɗan jujjuyasu alamun tambaya.
“In zuba?”.
A hankali ya ɗan juyo ya ɗan kalleta tare da ɗaga mata girarsa ɗaya alamun yess zuba ya ƙare ɗaga girar da ƙara manna hannunsa ƙasan bakinta kaɗan a hankali ta tattarosu tare da ɗan sunkuyowa ta zuba mishi su cikin tafin hannunshi.

Cike da mamaki Rahama ta buɗe baki da hanci tana kallon su kamar wasu tattabaru.
Ibraahim ma ido ya zuba musu, ita kuwa Rahama kai ta kuma juyawa ta kalli Didi data kauda kanta gefe tana mgnar zuci.
“Uhmmm ai in dai ya ɗauki mahaifinku zai yi abinda yafi hakama”.
ta ƙare mgnar zuci da kallon Ibraahim da ya saki baki yana kallon Modibbo ganin ya afa ƴaƴan kankanan cikin bakinsa tare dasa hannunsa ya tsinki inabi guda ɗaya ya haɗa da ƴaƴan kankanan ya ci.

Ita kuwa Didi murmushin tayi tare da maida kanta kan TV.
Shi kuwa Modibbo hannunshi ya kuma miƙa mata a karo na biyu ta kuma sa mishi ƴaƴan kankanan.
A nutse taci gaba da ci, a hankali ta juya ta kalli Ibraahim dake cewa.
“Yah Aleey in Sha Allah nima gobe zan koma Turkey”.
Kallonsa Moddibo yayi kana yace.
“Ha'a har zaka koma kuma?”.
Ya ƙare maganar da sawa Khausar tafin hannunshi ƙasan bakinta sabida ganin ta kuma tara wasu ƴaƴan kankanan, zuba mishi su tayi tare da zuba mishi idanu,
Shi kuma shu'umin murmushin gefen baki yayi tare da watsa ƴaƴan kankanan a baki domin shi yasan amfanin ƴaƴan kankanan a jikin namiji, domin babu wani abu cikin fruits dake ƙarawa wa maza ƙarfin kamar ƴaƴann kankanan shiyasa duk wani mgnin ƙarfin tattalin lafiya mazantaka zaka samu da sinadarin ƴaƴan kankanan a ciki.
Ya tabbatar bata san amfanin da zasuyi mishi a jikinsa bane da bazata bashi ba.
Yoh shida ko azumin rage ƙarfin sha'awa yayi muddin ya kuskura yayi buɗa baki da kankana to ranar ba bacci, bare ba azumin yayi ba, kuma gata kusa dashi.
Shi kuwa Ibraahim cikin kallon yadda yayan nashi ke amsar ƴaƴan kankanan daga bakin matarsa yana ci ya ɗan gyara zama yace.
“Eh wasu kaya zan sake kaiwa kasan ban cika zama anan ba saboda yanayin kasuwanci na”
Murmushi yayi tare da faɗin.
“Yaro Ƙarami da neman kuɗi”.
Yaaje mgnar yana kallon Khausar data tura baki alamun ya kawo hannunshi ya amshi ƴaƴan kankanan, miƙa mata hannun yayi tare da lasar gefen lip inshi na sama.
Didi dake sauraron tace.
“Wallahi fa kadai faɗa masa kayi masa faɗa ko zai rage Ibraahim da zirga-zirga firr yaron nan yaƙi zama sai jaraban son Kuɗi”.
Murmushi Ibraahim yayi yana mai lallon salon so mai zafi da darasi a wurin ustzun yayansa da ya dasa mai son aure farat ɗaya cikin fesar da numfashi yace.
“Toh Didi Idan ban nemi kuɗi ba mai zanyi nayi karatu na gama kuma Ni ba ayi min Aure ba sannan kuma abubuwan nan abune daya kamata asame su a inda babu tunda dabino ne mutane da dama suna bukatar shi acan shiyasa muke kai musu”.
Kai Didi ta girgiza tana gyara zamanta tace.
“Toh lallai kam wato ba'ayi ma aurena ba?”.
Kanshi ya ɗan sosai tare da sunkuyar da kai dan baisan mgn ta subce mishi ba.
Ita kuwa Didi cikin kulawa tace.
“Toh Amman ai bashi kaɗai kake yi ba inka dawo nan ɗinma komai na hotel ɗin Mouldy ka ciki”.
Ƴar dariya yayi tare da faɗin.
“Toh Didi ba dole inne mi kuɗi ba sune abokan rayuwa”.
Murmushi tayi tace.
“Yanzu kayi magana”.
Cikin sauƙe numfashi yace.
"Da Yauma nayi niyyar tafiya amma ina jira su Abualeey su dawo ne Shiyasa”.
“Allah ya dawo dasu lafiya”.
Cewar Moddibo.
Da ya kuma miƙa Khausar hannun a karo na barkai ita bashi ƴaƴan kankanan da sai yanzu ta cinye sai kuma ta kalli bowl ɗin tuni ya cinye mata inabi.

Zama Didi ta gyara tare da faɗin.
“Aima In Sha Allah nan da awa biyu zasu iso”.
Atare suka hada baki wajen cewa.
“Masha Allah Allah ya kawo su lafiya”. Kana sukaci gaba da hirarsu Rahama kam zama ta gyara tana bin Modibbo da Khausar da kallo domin Ita dai darasi take ɗauka.

Aranan su Abualeey suka dawo sun dawo kuma da labari mai daɗi cewa Mahaifin Asma'u ya bawa Dr Jameel Aurenta sannan Mahaifin Asiya ma ya bawa Zakariyya wanda ansa bikin Auren nanda wata uku ne masu zuwa.
Chapter 108 · 0% Book details