← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 150

Sashe 141

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Acan asibitin kuwa lokacin da Asma'u take ta kira Dr zuwa lokacin 1:30pm yayi, haka yasa suka fara shirya komai, nan da nan suka gama shirya komai da komai na asibiti kasancewar ƙarfe 2:00 dai-dai za'a shiga da ita ahankali Dr Eshaa ta shiga ɗakin hannunta riƙe da wani riga da hula irin wanda ake sawa idan za'a shiga da mutum ɗakin C's miƙa mata rigar tayi tare da cewa.
“Gashi zakisa wannan ɗin”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da karɓa kana ta juya ta kalli Moddibo cike da tarin ƙaunarta da kuma tausayinta Moddibo yace.
“Insa Miki ne?”.
Langwaɓar da kanta tayi tana rau-rau da Idanunta tace.
“Nikam tsoro nake ji zuciyata bugawa take Yah Mu'allim”.
Kamota yayi kana ya ruggumota jikinsa cikin wata amintacciyar murya mai cike da jin ƙai da tausayi yace.
“Bakomai Minha, ba abinda zai sameki sai alkhairi kinji ko Minha”.
Ya ƙarashe Maganar cikin sanyi haka nan yake jin jikinsa ya mutu kana zuciyarsa na tsinkewa ya rasa mai yake masa daɗi a duniya.
Ganin haka yasa Dr Jameel da Dr Eshaa juyawa suka fita Ahankali Asma'u ta yunƙura da niyyar fita da sauri Khausar ta riƙo tsintsiyar hannunta tare da cewa.
“Asmeey ina zaki je?,Ki tsaya mana”.
Cikin rauni da karyewar zuciya Asma'u ta kalleta kana tace.
“Khausar abinda kike faɗa yana tayar min da hankali ance Miki bakomai a Theater Nan Amma sai wasu maganganu kike masu tarwatsa lissafi da hargitsa mana nitsuwa”.
Araunane ta sunkuyar da kanta tare da cewa.
“Toh ya za muyi da abinda Ubangiji ya tsara mana Asma'u”.
Cikin ƙarfafa mata gwiwa tace.
“In sha Allahu Alkhairi Ubangiji ya rubuta mana”.
Kallonsu tayi sai kuma tace.
“Hmmm Allah yasa”.
Asanyaye Asma'u tace.
“Ameen”.
Shiru ɗakin yayi na wasu mintuna katse shirun Khausar tayi ta hanyar cewa.
“Gashi kuma har yanzu Momyna bata zoba”.
Kallon time Asma'u tayi tare da faɗin.
“Ai zata zo kafin a shiga dake in Sha Allahu yanzu naji Didi na waya da Innayi tana cewa sun taho asibiti”.
Sake jingina bayanta da jikin Moddibo tayi kana tace.
“Allah ya kawo su lafiya ta ganni inganta koda ma na karshene waya sani!?”.
Cikin sauri Moddibo ya sake janyota jikinsa ya rungumeta haka nan yaji wani irin rauni tausayi jin ƙai baisan lokacin da shesh-sheƙan kuka ke taso masa daga ƙasa ba yace.
“Minha meyesa?”.
Kai ta girgiza tare da cewa.
“Bakomai fa Yah Mu'allim”.
Haka yaita rarrashinta tare da kwantar mata da hankali yace.
“Bakomai Minha babu abinda zai sameki sai alkhairi lafiya za'a shiga dake afito dake lafiya”.
Ɗan Murmushi tayi tare da cewa.
“Ameen Yah Mu'allim in Sha Allahu ya Mu'allim na daina damuwa amma ina neman yafiyarka iya tsawon rayuwar da mukayi tare tun daga makaranta har zuwa dana kasance ƙarƙashin Inuwar Aurenka idan akwai abinda nayi maka ka yafe min kayi min aikin gafara”.
Cikin sauri ya sake ƙanƙameta ajikinsa kana yace.
“Babu abinda kika yimin Minha.
Ni kuma me zakiyi kin aduniya Ni babu abinda kika yimin kuma koma akwai na yafe miki duniya da kiyama”.
Kanta ta sake mannawa da ƙirjinsa tare da cewa.
“Nagode Yah Mu'allim”.
Ahankali Dr Eshaa ta sake turo ƙofar ta shigo tare da kallon Moddibo tace.
“Asa mata rigar yanzu fa sauran minti goma a shiga da ita kunga har 1:50 yayi”.
Kai ya gyaɗa kana ya cire mata rigar jikinta ya zira mata na asibitin sai kuma ya tsugunna ya zare mata skintied dake jikinta ya cire ya ɗaura akan gadon da take kwance ya riƙo hannunta yayin da ƙafanta ke sanye cikin wani takalmin roba mai taushi Ahankali ya kama gashin kanta ya nannaɗe kana ya tura acikin hular rigar sai kuma ya sakar mata da lallausan murmushi yace.
“Kin kuwa ga yanda kika yi kyau cikin kayan nan kuwa?”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Hmmm”.
Matsowa jikinta yayi tare da tallafo kanta ya manna da ƙirjinsa kana ya mata kiss agoshi yace.
“Kinyi kyau sosai tare dani za'a shiga ayi Theater dake kinji Minha”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh Yah Mu'allim”.
Yana ɗan janta jiki yace.
“Ana Miki Theater za'a cire mana ɗan mu kina gani muna hira”.
Saurin kallonsa tayi sai kuma ta zaro idanunta tace.
“Yah Mu'allim wani irin Theater ne ina kallo”.
Yana matsa hannunta acikin nasa yace.
“Kawai za'a Miki alluran kashe zafi ne sai ayi Theater kina ji kina gani muna kuma hirarmu Yah Mu'allim ɗinki a kusa dake”.
Cikin sauri ta girgiza masa kai idanunta na tara hawaye tace.
“Um-um nikam bana son wannan Yah Mu'allim a cire min hankalina kawai ayi min Theater”.
Ganin alamar hankalinta ya fara tashi ya sassauta murya tare da cewa.
“Haka kike so?”.
Kai ta gyaɗa dai-dai lokacin Dr Jameel ya karaso yace.
“Bakyaso amiki kina kallo?Idan kina so na sai a jawo Mirror a sama Anuna Miki kina kallo”.
Da sauri ta runtse idanunta tare da manna kanta a dantsen hannun Moddibo tace.
“Nikam ina tsoro nice zan tsaya har acire ɗa ajikina?,Nikam bana so wallahi Dr Jameel kawai dai ayi min alluran da zai cire min hankalina gwara ayi min shi ina bacci in na farfaɗo in ganni da yaro na”.
Moddibo na shafa bayanta ya kalli Dr Jameel tare da cewa.
“Ayi mata yanda take so”
Kai Dr Jameel ya Jinjina kana yace.
“Toh shikenan ba matsala haka za'a yi mata”
Fita sukayi dai-dai lokacin kuma su Momy suka shigo cikin sassarfa taje ta rungume Momy.
Momy kuwa cikin sauri ta lumshe Idanunta jin hawaye na tsats-tsafowa cikin sanyi da rauni tace.
“Ubangiji Allah ya rabaku lafiya Khausar Allah yasa ayi aikin nan cikin lafiya akan alkhairi Allah ya fitar dake lafiya ".
Araunane ta kalli Momy tare da faɗin.
“Ameen ya Allah Momy Allah ya amsa kiyita min Addu'a Momyna kiya femin idan akwai abinda na taɓa yi Miki na cutar wa ko ɓacin rai”.
Da ɗan sauri Momy ta mari kumatunta kadan kana tace.
“Me kikayi min?,Ni babu abinda kika yimin Mamana Ubangiji Allah ya fito miki dashi da sauƙi”.
“Ameen ya Allah” ta faɗa tare da sakin Momy jin muryan Raudhat wacce suka shigo da Ibraahim da sauri ta risina ta rungumo Raudat cike da farin cikin ganinta Raudat tace.
“Oyoyo Addah Khausy ”.
Rungumeta Khausar tayi tana Murmushi cike da farin ciki Raudat ta cigaba da cewa.
“Addah Khausy wannan kayan fa”.
Kallon jinkinta tayi sai kuma tace.
“Raudat Theater za'a yimin”.
Cikin rashin fahimta Raudat tace.
“Addah Khausy menene kuma Thearter?”
Ɗan murmushi tayi tare da cewa.
“Abinda aka yiwa Momy lokacin haihuwar ku keda Ramadan”.
Jim tayi sai kuma tace.
“Toh Addah Khausy Allah ya kawo miki sauƙi da lafiya”
Cikin sanyi da rauni tace.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Moddibo kuwa Ahankali ya kamo hannunta ya tsayar da ita sai kuma ya juyo da ita gaban Momy yace.
“Momy ayi mana addu'a Allah ya fito damu lafiya ”.
Ahankali Momy tace.
“Ameen ya Allah Moddibo”.
Ahankali Khausar ta sake janye hannunta ta rungume Momy sai kuma ta rungume Didi Dr Eshaa ce ta ƙaraso tare da cewa.
“Lokaci yayi fa kizo mu tafi Khausar”.
Cikin sanyi ta kamo hannun Asma'u.
Ita kuwa Asma'u tuni take zubda hawaye hakanne yasa ta kauda kanta gefe tare da ruggumeta.
Ganin hakane yasa Modibbo ya kamo hannun Khausar ɗin suka juya suka nufi cikin ɗakin.

Anutse Khausar ta juya ta fara tafiya Ahankali tana waiwayen su cikin ƙarfin hali Momy tace.
“Mene kike tafiya haka kamar Kazar da ƙwai ya fashewa aciki, kiyi maza kishiga ayi Miki minti nawa kin fito hankalin ki kwance Mamana kike tafiya kina sanɗa”.
Juyawa tayi ta kalli Momy cikin sanyi da langwaɓar da kai tace.
“Momy ba sanɗa nake bafa yunwa nake ji shiyasa bani da ƙarfi”.
Jin haka yasa Moddibo ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Shikenan toh tunda yunwa kike ji”.
Ya ida maganar tare da tsugunnawa ya ɗauke ta cak kamar Baby ya rungumeta.

Raudat dake kallonsu ne ta sanya dariya kana ta buga tsalle tare da faɗin.
”Iyeeee Addah Khausy kin lale kinji daɗin ki Yah Moddibo ya ɗaga ki”.
Ibraahim dake bayanta ya matsa kusa da ita tare da ɗagata sama kana yace.
“Toh kema kiji daɗi an ɗaga ki”.
Cike da farin ciki ta riƙa ƙyalƙyala dariya tana cewa.
“Addah khausy Bye bye sai kin fito”.
Juyawa Khausar tayi ta kalleta kana tace.
“Toh Raudy na”.
Su Momy kuwa shiru kawai sukayi tare da rakasu da ido.
Chapter 141 · 0% Book details