← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 150

Sashe 50

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai misalin ƙarfe 9:30 Didi ce da Sarki Youseep Mouleey suka shiga falon suna shiga suka ji falon shiru alamar baya nan yayin da suka fara jiyo wani sautin murya mai daɗi da sanya nutsuwa na karatun Alkur'ani na ratsa kunnensu.
Cikin nutsuwa Sarki Youseep Mouleey ya fara bin direction ɗin da yake jiyo sautin karatun Yayin da Didi ke biye dashi.
Akan darduma suka hango sa da alama Salatul duha ya idar kana idanunsa na lumshe yana karatun akansa.
Daga gefensa suka zauna lokaci ɗaya hawaye ya shiga bin kuncinta cike da farin ciki ta ɗaga hannunta sama kana tace.
“Alhamdulillah Innayi kinyi min duk kan gatan duniya kin bawa ɗana Ilimi mafi girman ilimi mafi tsada da daraja wanda zai amfanesa duniya da lahira sannan zai amfanemu”.
Sai ta kuma kalli Moddibo still hawaye na kwaranya daga idanunta ta cigaba da faɗin.
“Wannan ɗana ne yake karatun Alkur'ani tamkar acikin harami wanda koda acikin harami sai an jinjina masa”.
Moddibo kuwa jin sautin Muryanta da kuma motsin Mahaifinsa yasa ya buɗe Idanunsa jin tana cigaba da cewa.
“Innayi Allah ya biya ki da mafificin Al'khairi Ubangiji Allah ya sadamu inyi miki *SAKAYYAH* da mafi kyawun abinda ki kayi min sannan inyi miki godiyar da ban san da wani irin baki zan miki ba”.
Ahankali Moddibo ya shafa addu'a kasancewar yazo ƙarshen surar da yake karantawa.
Anutse ya juya ya kallesu haka nan zuciyarsa ta aminta da cewa Tabbas suɗin wasu ababene na jikinsa da Zaran ya kalli Mahaifinsa zai ga tsananin kamanninsa dashi babu abinda ya raba su shi kansa kamanninsa da mutumin yana bashi mamaki babu abinda ya rabasu sai dai shi Modibbo yawan shekarun sa bai kai nasa ba zuwa yanzu ya gama gamsuwa iyayensa ne su.
Cike da ladabi ya gaishe su kana suka amsa cikin sakin fuska da tarin ƙaunarsa.

Didi kuwa ahankali ta janyo basket data shigo dashi ta ajiye agabansa, tare da fitar da kulolin, kana ta ɗauki plate ta zuba masa abincin da ta dafa mishi da kanta, kana ta kalleshi cike da so da ƙauna tace.
“Wannan abinci da kaina na shiga kitchen na dafa maka dan kaci da kyau”.
Cikin gamsuwa da kalamanta ya jinjina kai ya tabbatar nutsuwa da kamalarta da kuma kimarta tafi ƙarfin tayi masa ƙarya maganganun da take faɗa daga zuciyarta ne kuma gaskiya ne babu shakka ko haufi aciki shi kanshi ya gamsu mahaifiyarsa ce ita Abualeey kuwa mahaifinsa ne masarautar Mouley kuwa tabbas mahaifarsace...
Fuska ɗauke da yalwataccen murmushi Sarki Youseep Mouleey ya janyo Cup tare da faɗin.
“Ni kuma da kaina zan haɗa maka tea in baka duk kan kulawar daka rasa atare damu na tsawon shekaru, in Sha Allah sai mun haɗa ta mun baka a iya tsawon sauran Rayuwar da Allah ya ƙadddara mana anan gaba”.
Cikin wani irin tattali da kulawa suka ci-gaba da faɗa masa maganganu masu sanyi da ratsa ƙwaƙwalwa wanda ko wani ɗa yake fatan saurara daga iyayensa.
Moddibo kuwa tamkar amafarki haka yake jin abubuwan sai dai wani lokaci wani abu ya taɓa ganinsa amafarki sa.
Haka suka cigaba da kulawa dashi suna hira da kara fahimtar yasan komai ma masarautarsu, yinin wannan rana suna tare dashi koda motsi yayi zasu tambayesa me yake so ko kuma me yake buƙata sai gab Azahar suka yi masa sallama suka fita suna tafiya aka kira sallar Azahar...
Anan yayi Sallar Azahar ɗin sa yinin wannan ranan ma ba'a buɗe sa.
Haka yayi kwanaki biyu anan batare daya fita koda ƙofan falon ba sai dai akawo masa abinci sai dai kuma su shigo suyi hira dashi...
Yau ta kasance Asabar inda ya zama kwanakinsa uku kenan a Masarautar Mouleey bayan fitar Mahaifiyarsa, Mahaifinsa da kuma Sheikh Jabeer yana zaune a falon kamar daga sama ya fara jiyo shesh-sheƙan kuka.
Cikin sauri ya juya ya kalli Hadiman dake tare dashi sai kuma ya kauda kansa ganin basu bane cikin yanayin mamaki da al'ajabi ya juya gabas da yamma kudu da Arewa yaga dai duk basu bane keyi kukan. Bisa alamu kuma kamar su basujiba, ahankali ya miƙe ya nufi Corridor har ya isa falon nan ma ba kowa sai dai yana jin shesh-sheƙan kukan daga cikin bedroom cikin sassarfa ya nufi bedroom ɗin yana shiga ya hangi Jalaluddeen ne zaune agefen gadon yana kuka tamkar ransa zai fita.
Cike da matsanancin mamaki gami da al'ajabi yace.
“Jalaluddeen k...”.....

LITTAFIN SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 in tura miki kisha karatunki.

GAREKU masu son Maganin infection duk maiso ta biya yau in Sha Allah jibi saƙonku zai taho.

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 13*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Tallah !! Tallah !!

Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* , yau ta sake dawo muku Domin tallata muku Littafin mai Suna ( Rai Daya Jan Zaki) littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji.

Farashin wannan littafin Naira Dari biyar ne 500 kacal postin biyu a arana banda ranar Juma'a .
Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci.
Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank
Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku.

Jalaludeen kuwa cikin rauni ya ɗago idanunsa wanda suka zama tamkar garwashin wuta, saboda yanda sukayi ja-jawur yayin da baki ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa kar-kar tamkar wanda aka jona masa Shorking kuka yake mai shiga jiki tare da ratsa zuciyar duk wani mai imani daya saurara.
Da sauri Moddibo ya ƙara sa kusa dashi gefenshi ya zauna cike da matsanancin rauni da kuma famewar mikin dake zuciyarsa na rashin J ɗinsa ya shiga rera wani irin raunataccen kuka tamkar ransa zai fita, kukan wanda bai samu yayi shi ba a lokacin rasuwar, baka jin sautin komai acikin ɗakin, face Shesh-sheƙan kukan su dake cigaba da wanzuwa aƙalla sun ɗauki kimanin minti goma sha biyar suna kuka batare da wani yayi yunƙurin rarrashin ɗan uwansa ba.
Cikin dauriya da ƙoƙarin son hana kansa kuka kana da shesh-sheƙa Jalaludeen ya ɗago tafin hannunsa mai masifar sanyi tamkar wanda aka ciro acikin dusan ƙanƙara ya manna aƙirjin Moddibo daya ke jiyo bugun zuciyarsa, cikin rauni yace.
“Kayi haƙuri Mouley haƙiƙa munyi rashi mai girma.
Munyi rashi mafi ciwo azuciyarmu. Kayi haƙuri Aliyu kaya femin tsawon lokaci baka ganni ba ina cikin haramine! shiyasa baka ganniba”.
Lumshe idanu Moddibo yayi wasu hawaye masu masifar zafi suka zubo akuncinsa yayin da sanyin tafin hannu Jalaludden ke ratsa zuciyarsa Jalaludden kuwa cikin raunatacciyar murya ya cigaba da faɗin.
“Saboda na shiga inayin I'itiƙafi tsawon lokacin nan shiyasa kuma koda na fito munyi tafiya nida Kakana munje ƙasar Sin shiyasa baka ganni ba bansan Jameelu yashiga wannan hali ba bansan Jameelu ya rasuba Mouley”.
Sai kuma ya fesar da numfashi mai zafi tare da cigaba da faɗin.
“Sai jiya Juma'a ne naje Taraba domin kai muku ziyara, kasancewar na daɗe ba muyi magana ba yasa na shirya muku Surprised sai dai kawai ku ganni, toh ina isa gidan innayi na nufa, naje gidan Innayi na samu babu kowa sai na wuce gidan Ummi”.
Kallonsa kawai Moddibo keyi hawaye na cigaba da silala daga idanunsa.

Cikin rauni Jalaludden yace.
“Acan na samu Innayi suna hiran. Jameel ya rasu kuma na tsinkayi cewa kana ƙasar Morocco, nazo ƙasar Morocco na bibiyi al'amarin ka har na gane cewa kana cikin Fadar Rabat!”.
Kuka ne yaci karfinsa cikin kuka kamar ƙaramin yaro ya cigaba da cewa.
“Mouley munyi rashi.
Jameel ya tafi ya barmu Allah yajiƙan Jameel Allah yayi mishi rahma!”.

Cikin sanyin murya Moddibo yace.
“Amin Ya Allah. Amman nayi mamaki rashin jinka Jalaladdeen ina ka shiga, tsawon lokaci ba ɗuriyarka. Na shiga matsanancin damuwa Jameel ɗina ya ɓace tsawon lokaci, bamu sameshi ba.
Naso ace kana kusa damu kayi mana amfani fiye da amfanin da kayi mana abaya ka faɗa mana inda J.yake”.
Kai Jalaludden ya girgiza still hawaye na kwaranya daga idanunsa ya riƙe hannun Moddibo kana yace.
“Bana kusa Aliyu, sannan kuma koda ina kusa muma kanmu jinnu. Ubangiji bai sanar damu gaibu ba Aliyu,
da ace Allah ya sanar damu ilimin gaibu ko a inda nake zan iya sani da zan faɗa maka, amma Allah bai sanar damu gaibu ba.
Sanin gaibu sai Allah kaɗai bansan haka zai faru da Jameel ba.”
Numfashi Moddibo ya fesar kana ya dafe goshinsa da hannunsa na dama tare da faɗin.
“Tabbas munyi rashi mafi girma ban taɓa sanin ya ɗaci da zafin mutuwa yake azahiri ba har sai da na rasa J ɗina, mutuwar J mutuwa ce da bazan taɓa mancewa ba. Sannan bazan daina jin zafi da raɗaɗinsa ba har sai ranar dana koma ga Ubangiji na!”.
Kai Jalaludden ya gyaɗa kana yace.
“Sosai ma kuwa Aliyu, amman haƙuri zamuyi, domin babu abinda Jameel yafi buƙata agaremu yanzu face addu'a addu'ar mu”.
Kai Moddibo ya jinjina tare da cewa.
“Zan cigaba da yiwa J ɗina addu'ar samun rahamar ubangiji har zuwa numfashina na ƙarshe”.
Haka suka kwana suka yini suna hira.
Chapter 50 · 0% Book details