← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 150

Sashe 101

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai ya girgiza cikin fesar da numfashi yace.
“Bazan miki mugunta ba *Minha* niba mugu bane”.
Cikin shesh-sheƙan kuka ta girgiza kai tare da cewa.
“Baka Sona katsaneni su Momy suka yarda suka kawo Ni wajen wanda baya sona ya tsaneni suka tafi suka barni”.
Runtse idanunsa yayi tare da faɗin.
“Nine bana sonki *Minha?*”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Eh mana baka sona basai mugunta kake tamin ba”.
Kai ya dafe cikin jin zafin hawayenta yace.
“Yaushe nace miki bana sonki, kuma yaushe nai miki mugunta?”.
Cikin tura baki da shesh-sheƙa ta goge fuskarta tace.
“Shekaran jiya da daddare ba mugunta kayi min ba kakusan ka kasheni, kuma sai Allah ya saka min duk muguntar da kake min”.
Cikin taushin lafazi mai cike da kulawa cikin muryar da kashe jiki da zuciya yace.
“Toh kiyi haƙuri ki yafe min ki daina yimin Allah ya isa”.
Hawaye na kwaranya daga idanunta ta maƙe kafaɗarta da cewa.
“Wallahi bazan yafe ba”.
Da damuwa asaman fuskarsa ya motsa laɓɓansa tare da cewa.
“Ya Salam mijinki ne baza ki yafewa ba *Minha* ”.
Kai ta gyaɗa cikin tabbatar wa tace.
“Eg bazan yafe ba tunda zalina kakeci”.
Sai kuma ta kifa kanta ahannun kujera ta cigaba da yin kuka.
Duk rarrashin ta da yake taƙi yin shiru.

Ahankali ya miƙe ya nufi bedroom ɗin sa, ganin ya tafine yasa ta yunkura cikin sauri ta miƙe ta nufi ƙofa tana murɗa handle ɗin taji kofar arufe, komawa tayi ta zauna kan kujeran data tashi kana ta fashe da sabon kuka fahimtar ya rufe ta yadda bazata iya buɗewa bane.

Moddibo kuwa yana shiga bedroom ya ɗauki wayanta.
Call log yashiga number Momy ya Kira buga ɗaya ana biyu ta ɗauka yana dai-dai bakin ƙofan zai fiti falo yaji Momy ta ɗauka cikin nutsuwa, girmamawa, Mutumtaka, kara gami da risinar da Kansa ƙasa yace.
“Momy Barka da Safiya”.

“Barka dai Moddibo ko?”.
Cewar Momy.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Eh Momy nine”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Ya gida yasu Khausar suna lafiya?”.
Cikin damuwa da yanda yake jin shesh-sheƙan kukanta yace.
“Momy tana lafiya amma tunda su Hajja Nana suka tafi take ta kuka Momy nayi-nayi ta daina Kukan taƙi”.
Cikin raunin Murya irin na wanda ke gab da zubda hawaye ya ƙarasa Maganar saboda har cikin ransa yake jin kukanta sai kuma ya cigaba da faɗin.
“Momy dan Allah ki rarrasan min ita kukan zai sa mata zazzaɓi Momy ki rarrasheta ki bata haƙuri”.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya Momy tace.
“Yanzu ina Khausar ɗin?”.
Ahankali yace.
“Gata nan”.
Dai-dai lokacin kuma ya isa gaban Khausar ɗin durƙusawa yayi agabanta tare da manna mata wayar akunnenta.

Momy kuwa ahankali tace.
“Hello Khausar”.
Ta buɗe baki da niyyar cewa na'am Momy kenan kuma kuka ya kufce mata cikin rauni tace.
“Momy sun tafi sun barni basu barmin kowa ba babu wanda na sani”.
Sai kuma tayi shiru sakamakon kuka da yaci ƙarfinta kusan minti biyu ta ɗauka tana kuka still wayan na maƙale kunnenta.

Kallonta kawai Moddibo keyi ya rasa me yake masa daɗi suya yake jin zuciyarsa nayi, hannunta ɗaya na riƙe da nashi yana shafa sajensa yana kallonta ji yake kamar ya buɗe ƙahon zuciyarsa ya sata acikin ya rufe kofar koda zata daina kukan.
Ganin yadda hawayenta ke kwaranya ba ƙaƙƙautawane yasashi, ɗan ƙara matsota, tafukan hannunsa yasa ya tallabe fuskanta tare da matso da tashi fuskar a hankali ya zare harshen sa.
Wani irin dogon ajiyar zuciya Khausar taja a lokacin da taji, sanyin tattausan harshensa yana ratsa kumatunta.
Shi kuwa Modibbo cikin yanayi na musamman, ya fara lasan hawayenta tare da hanasu zuba.
Ita kuwa Khausar haka nan taji ta gaza barin kukan.

Ganin baza tayi shiru ba yasa Momy cewa.
“Toh yanzu magana zakiyi ko Kuka zakiyi Khausar?”.
Cikin kuka sosai tace.
“A'a Momy”.
Sai kuma ta cigaba da kuka.

Cikin ɗaure fuska Momy tace.
“Idan baki daina Kukan nan ba kashe wayar zanyi”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“Momy na daina”.
Ajiyar zuciya Momy ta sauƙe kana tace.
“Wai ni kam Khausar kinyi hauka ne? meyesa baki da hankali ne? Nace wai hauka ne a kanki?”.
Cikin ƙoƙarin hana kanta kuka da shesh-sheƙa take girgiza kai.

Modibbo kuwa a hankali ya lumshe idanunsa domin yanajin duk abinda Mommy ke faɗa, sai kuma yaci gaba da lasar kumatunta da duk ɗigon hawayen da zai ɗiso.

Momy kuwa cikin haɗa fuska tace.
“Waye kika taɓa ganin yayi haka?.
Ke dama kin ɗauka Aure wasa ne?
to ki nutsu ki maida hankalinki cikin jikinki kisan abinda kike yi Aure ba abin wasa bane Aure Sunnar Manzon Allah (S.A.W) kuma Aure unarnine na Allah da Manzonsa sannan kuma keda kanki kikace zaki rayu dashi a ko wanne yanayi.
Dan haka babu yanda za'a yi adawo dake kin taɓa ganin anyi Auren ƴa mace ta koma gidansu?”.
Cikin matsanancin kuka ta girgiza mata kai Momy kuwa cikin nutsuwa ta cigaba da faɗin.
“Hakkine da iko da matsayin miji duk inda yaga dama ya ajiye matarsa ya za'ayi Kice ya dawo dake hauka ne akanki?.
Haka Ummi da muka yi waya take faɗa min Haiydar nata kuka kamar ransa zai fita saboda ya tafi ya barki kina kuka duk hankalinsa ya tashi zaki sa yaro adamuwa kisa ya dawo min da zazzabi shi kansa mijinki kin tayar masa da hankali”.
Cikin faɗa ta cigaba da cewa.
“Har mijinki zai riƙa rarrashinki yana cewa kiyi haƙuri amma ki ƙi kiyita kuka kamar ibada”.
Khausar kam shesh-sheƙa ta cigaba dayi so take ta hana kanta kuka amma kukan yaƙi haɗiyuwa.

Cikin damuwa Momy ta cigaba da cewa.
“Ok zakici gaba da kukan kenan?”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“A'a Momy na dainaaa”.
Irin yanda take kukan har numfashinta na yankewa.

Momy kuwa cikin damuwa ta cigaba da faɗin.
“Mijinki yaita rarrashin ki ki ƙi rarrashuwa hauka ne akanki, Kiyita kuka kina cewa zaki da kowa ba ganan Maman mijinki ba ai zata zame miki madadina in dai kika mata biyayya zata maye miki gurbina mijinki kuma dole ki masa biyayya sannan ki bishi sau da ƙafa domin shine komai na rayuwar ki a yanzu saɓa mishi kamar saɓa umarnin Allah da Manzonsa ne da suka ce Ayiwa miji biyayya”.
Kuka ta cigaba dayi tana jan ajiyan zuciya.
Moddibo kuwa ganin Momy nayi mata faɗa sannan bata daina kukan ba yasa ahankali yasa hannu ya zaro wayar daga kunnenta kana ya mayar kunnensa cikin sanyi da ƙasƙantar da kai murya a raunace yace.
“Kiyi haƙuri Momy rarrashinta za'a yi ba faɗa za'a yi mata ba”.
Yana maganar kamar zaiyi kuka.

Kai Momy ta girgiza kana tace.
“Khausar baza taji rarrashi ba idan ta fara kuka batasan bari ba kafita harƙanta ka barta idan tayi Kukan tagaji da kanta zata bari ka barta na lura Khausar rigima ne da ita”.
Sake ƙasƙantar da muryarsa yayi yace.
“Momy kiyi haƙuri In Sha Allah zan rarrasheta za tayi shiru Mommy bayan iya barinta tana kukaba zai cutar min da ita”.
Kai Momy ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan sai anjina”.
Ahankali ya sanya hannunsa kan kumatunta ya fara share mata hawaye kana cikin sanyi da taushin lafazi yace.
“Kiyi haƙuri ni ba mugu bane bazan miki mugunta ba, nifa Mijinki ne ba kyau kada ki sake cewa mijinki Mugu bakya tsoron Allah ya ƙona kine?”.
Cigaba da kuka tayi wanda yake fitowa daga ƙasan ranta cikin rauni tace.
“Aini ban ce maka mugu ba amma dai kana cin zalina shekaran jiya kusan kasheni kayi kuma Allah zai sa kamin”.
Sake ƙasa da murya yayi cikin taushin lafazi yace.
“Kiyi haƙuri In Sha Allah bazan sake ba ki yafe min kinji ki yafewa Yah Moddibonki Minha”.
Kafaɗa ta maƙale tare da tura baki da juya kumburarrun idanunta tace.
“Ni dai ban yafe ba sai Allah ya saka min daga duniya har kiyama bazan taɓa yafe maka ba”.
Zare idanunsa yayi sai kuma ya langwaɓar da kansa yace.
“Ayyah Khausar am ki yafemin kiyi min duk horon da zaki min amma kiya femin”.
Cikin shesh-sheƙan kukan ta kallesa kana ta tura bakinta tace.
“Da gaske?”.
Cikin sauƙe numfashi yace.
“Yess kimin duk hukuncin da kikaga ya dace da laifina, Amman banda kuka kuma banda cewa bana sonki da kuma cewa zaki koma”.
Cikin sauƙe numfashi shesh-sheƙan tace.
“Toh nima yanda kake cin zalina sai na rama ka kaɗe ɗankwali”.
Ba zato yaji murmushi ya sufce masa sabida mgnar tazo mishi a bazata.
Ya kuma lura yadda tayi mgnar kamar hakan shine babban burinta, ɗan ware idanunsa yayi tare da cewa.
“In kaɗe ɗankwali kuma?”.
Cikin tura baki ta gyaɗa kai tace.
“Eh kaima ba haka kake min duk abinda nayi kaima mugunta da kayi min ka kaɗe ɗankwalin kaji abinda nake ji”.
Numfashi ya fesar cikin tsira mata ido yace.
“Idan na kaɗe ɗankwalin zakiyi shiru?”.
Da sauri ta gyaɗa masa kai tare da faɗin.
“Eh”.
Sassayan ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Toh kawo ɗankwalin in kaɗe sau nawa zan kaɗe?”.
Kallonsa tayi ta wani tura bakisai kuma tace.
“Da gaske zaka kaɗe?”.
Girarsa ɗaya ya ɗaga mata.
Cikin jin dadi tace.
“Toh Sau hamsin zaka kaɗe”

Ware manyan idanunsa dake narke yayi tare da yarfe hannu da faɗin.
“Wayyo Allah na Ni Aleeyu”.
Sai kuma ya zauna ya kifa kansa akan cinyarta cikin langwaɓar da kai yace.
“To ai zaki kashe mijinkeeh”.
Ya ƙare maganar cikin shu'umar muryar da tasa jukinta mutuwa,
Ƙyafƙyafta idanunta tayi kana tace.
“Ba nima kana sani ina kaɗewa sau 30 ko sau 20 ba?“.
A hankali yace.
“Toh ai ke 50 kikace inyi”.
Cikin sharce hawayenta tace.
“Toh kasan Ai laifin da kayi yafi nawa yawa da zafi ko?”.
Numfashi ya fesar kana yace.
“Toh shikenan kawo ɗankwalin In kaɗe”.
Chapter 101 · 0% Book details