← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 150

Sashe 74

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acan ɓangaren Khausar kuwa kwance suke a bedroom su uku Khausar, Asma'u sai Dije.
Juye-juye Khausar keyi tare da jan tsaki bini-bini zataja tsaki.
Ahankali Asma'u ta janyo wayarta tare da duba time taga 1:00am juyawa tayi ta kalli Khausar tare da faɗin.
“Khausar ya dai?,Lafiya kuwa naga tun ɗaxu sai tsaki kike ba kiyi bacci ba?”.
Kai Khausar ta girgiza cikin sanyi murya tace.
“A'a bakomai”.
Ido Asma'u ta tsira mata tare da cewa.
“Ya zakice ba komai gashi tun ɗazu sai juye-juye kike”.
Lumshe idanu Khausar tayi kana tace.
“Da gaske bakomai kawai dai bacci be bai zo idona ba shiyasa”.
Kallonta Asma'u ta kuma yi kana tace.
“Amma kuma dai lafiyar ki ƙalau kam?”.
Kai ta jinjina tare da sauƙe numfashi tace.
“Lafiya ta ƙalau mana Asma'u”.
Ahankali Asma'u ta furta.
“Toh me ya ha naki bacci?”.
Cikin wata irin kasala da yanayin dake tsikaranta tun daga ƙwaƙwalwar kanta har zuwa tafin ƙafanta ta fesar da numfashi tare da faɗin.
“Hmmmm”.
Sai kuma ta jawo Pillow ta kwanta tare da lumshe idanunta atake fuskar Moddibo ya bayyana acikin ƙwayar idanunta lokacin da yake zubar da hawaye.
Kana ahankali ta shiga tuna moment da suka kasance jiya awajen taro daya rungumeta.
Ahankali taja dogon numfashi jin har zuwa lokaci ji take kamar ƙamshin na jikinta.
Runtse idanunta tayi da ƙarfi kana ta rungume Pillow da ƙarfi kamar yanda ya matseta alokacin.
Sake juyawa Asma'u tayi ta kalleta sai kuma tayi murmushi tare da cewa.
“Ko dai zan rakaki ɗakin Yah Moddibo ne?”.
Jin abinda Asma'u tace ne yasa ta buɗe Idanunta tare da kallonta tace.
“Kamar ya kuma ko zaki rakani ɗakin Yah Moddibo? Kefa kika ce Asma'u kin iya maganan banza? nifa na faɗa miki bana son irin maganar nan, ke kuma yanzu so kike kinuna min gaba ɗaya yanzu kin zama ƴar iskane ma”.
Gira Asma'u ta ɗaga mata tare da cewa.
“Rufa min asiri kar ki tara mana jama'a nagane kin kasa bacci sai juyi kike kina rungume-rungumen Pillow nasan meyene matsalarki”.
Hararanta Khausar tayi da idanunta dake lumshe kana tace.
“Toh Ni bani da wata matsala”.
Dariya Asma'u ta sanya tare da faɗin...

*Masu son Maganin infection da maganin mata, ku marmatso wannan account no in ne naku ta ciki zaku turo kuɗin ku 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, Sai ki turo shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276. akwai sabbin kaya masu zafi suna nan bisa hanya, ki turo kuɗinki a saki cikin lissafi. Kayanen mata masu zafi sadidan daga Chadi akwaisu Garukan daka, gumbunan, Tsumummuka, cida Ciccibi Abodi cida kaza ci da jan nama kwanon ƙasaitacciyar mace biyar sirri, furar mata, gumbar madara Gumbar kolli mai ƙyallin al'khairi gumbar uku al'khairi, gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, gumbar riɗi, garin maɗi garin melɗamhi garin ilanwaddihi garin mallaka, tsumin riɗi tsumin tsirtai tsumin kinfi budurwa, tsumin riɗi, tsumin ta baje Sabaya, matsin maliƙi mai masifar matse mace matsin daɗi har maɗiga, mai ɗan kare kyau. Kullacar sirri al'ajabu shu'umar Humra, da duk sauran kan ƙamshi. Haɗin amarya budurwa ko bazawara haɗin mai jego ko uwar gida, akwaisu Available set ɗinmu hawa hawane akwai manya akwai ƙananan, ƙanan daga 40k ne 35k 30k 25k 20k 15k 10k shine ƙarami haɗina na karshe sai kuma haɗin kwanon ƙasaitacciyar shi 7k ne shine ƙarshen haɗina kenan... Manyan set ɗin kuma daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k ke zaki faɗi haɗin nawa kikeso anyi miki kana kimin bayanin yadda kikeso da matsalarki ni kuwa nasan abinda zan haɗa miki, ina araha kam amman ina hana bashi*

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 21*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

“Ki faɗi gaskiya dai ko dai ko dai Magungunan _Aunty Aysha Aliyu Garkuwa_ sun fara aiki ajikin kine dan naji yanda su Aunty Ruƙayya da Aunty Hajara ke tabbatar da kyau da inganci maganin”.
Khausar na gyara kwanciya tace.
“A kin manta ba aiki ba uban aiki suka fara”.
Dariya Asma'u ta sanya tare da faɗin.
“Toh bani na kar zomon ba”....
Cikin sauri ta juya baya tare da rumtse idanunta, tana maganar zuci. haba da gskyar Asma'u inaga harda wannan tsume-tsumen ke ƙara gigitani gashi shima wannan Yah Modibbo duk ya hautsuna min natsuwa da rikitattun idanunsa masu kashe jiki,
da haka bacci ya kwasheta.

Washe gari tun da safe akazo akafara shirya Khausar ahaɗa mata wannan ruwan ƙamshin da Zaran ta gama ta fita za'a sake haɗa mata wani aƙalla sai da aka kusan haɗa mata kala bakwai zuwa dare.
kana aka koma na turaren hayaƙi da zai tsumata suma sun kai kala goma yinin wannan ranan haɗa ta akayi wani irin Masifeffen ƙamshi take da Zaran ta tashi awaje ƙamshinta zai bule.
Yayinda tuni kuma an kai mata Set ɗin akwatinanta duk anje anjere a Side ɗin ta...

Bayan an idar da sallar Isha'i Jakadiya, Lalla Hafsat, Rahma ne suka shigo falon su Khausar yayin da hannunsu ke riƙe da wata jaka abakin gado Lalla Hafsat ta ajiye kana ta juya ta kalli Khausar tace.
“Ya dai ƙanwata?”.
Khausar na murmushi ta sunkuyar da kanta tare da faɗin.
“Lafiya lau Aunty Hafsat ya gida?”.
Cikin sakin fuska tace.
“Alhamdulillah ya gajiyar biki da hidima mun kasa barinki ki huta ko?”.
Murmushi tayi batare da tace komai ba.

Tana zama tace.
“Kiyi haƙuri muɗin ne muna da yawan al'adu dan ma abin ne yazo ahaka an rage saura”.
Murmushi Khausar tayi akaro na biyu ta kuma sunkuyar da kanta.
Kallon Khausar dake wasa da yatsun hannunta tayi tare da cewa.
“Yanzu ki tashi Kije kiyi wanka in Sha Allah daga yau zaki samu ki kwanta kiyi bacci za'a kai ki Side ɗin ki”.
Ummi dake gefe tayi murmushi kana tace.
“Ai dai kam muna shan hidima”.
Dariya Lalla Hafsat ta sanya tare da faɗin.
“Ai dai kam biki ne na musamman Shiyasa baki ɗaya abubuwan komai na musamman ne”.
Kallon Khausar dake zaune Ummi tayi kana tace.
“Toh tashi Kije kiyi wankan mana”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa tashiga toilet ɗin daya ƙawatu komai fes-fes gwanin ban sha'awa kallon Bathtub ɗin da aka cikisa da ruwam haɗe-haɗen turaruka wanda tsaban turare da wasu abubuwan sirri daya sha sai da ya koma Sky blue ga wasu jan Flowes masu masifar kyau da suka ƙawata saman cike da farin ciki ta shiga tayi wanka bayan ta gama ta fito ɗauke da ƙaton Towel days sauƙa har gwiwanta tana fitowa Lalla Hafsat da kanta ta ɗauki Hand-drayea ta busar mata da gashin kanta kana ta ɗauki mayukan gashi masu kyau da turaren kai ta shafa mata su kana ta tufke mata su.
Bayan ta gama ta bata man shafawa tana shafawa a Fuskarta Lalla Hafsat kuwa da kanta ta tsugunna tana shafa mata aƙafanta ahankali ta ɗago kai ta kalleta kana tace.
“Masha Allah wallahi skin ɗin ki yayi kyau Sosai”.

Sunkuyar da kai Khausar tayi ba tare da tace komaiba.
Miƙewa Lalla Hafsat tayi bayan ta gama shafa mata man ta miƙa mata wani tattausan Boxes irin na mata mai masifar taushi wanda bai wuce cinyarta ba kana ta miƙa mata Brasseir tare da cewa.
“Ki shiga Corridor ki sanya”.
Kai ta gyaɗa tare da karɓa tashiga Corridor ta Sanya.
Bayan ta saka Lalla Hafsat ta zaro wasu riga da wando Farare sol acikin jakar masu masifar taushi da santsi taushinsu ya wuce gaban kwatance tamkar jikin Mage haka suke.
Karɓa Khausar tayi ta saka.
Wani irin masifar amsarta kayan yayin da manyan Hips ɗinta suka baje aciki tamkar dan ita akayi su.
Kunya ce ta kama Khausar ganin yanda wanda ya kamata Hips ɗin ta suka baje aciki.

Wani Lifaya mai masifar kyau da taushi Jaa mai ratsin baƙi-baƙi kana shara-shara ne Lalla Hafsat ta warware tare da naɗawa Khausar sosai Khausar tayi wani kyau na ban mamaki ga yalwataccen sumanta da yasha gyara kana Lalla Hafsat ta jera mata wasu fulawowi masu kyau da tsari kana ta sa mata wani siririn sarkan Gwal da ɗan kunnensa sirara marasa nauyi zaunar da ita tayi abakin gado kana ta miƙa mata Kaskon turaren wuta.
Atake Khausar ta shiga baza ƙamshi kai kace A Company turare aka sanyata wasu turaruka kusan kala biyar masu sanyin ƙamshi Lalla Hafsat ta kuma fesa mata.
Tana gamawa Rahma na shigowa idanunta akan Khausar tace.
“Wowww Masha Allah Lalla Hafsat kin yiwa ƙaninki shiri irin wannan tanadi duk Yah Aleey ake yiwa?”.
Murmushi Lalla Hafsat tayi kana tace.
“Ba dole ba ɗan ƙaninmu munefa mafi soyuwa a garemu ai dele mu nema masa farin cikinsa mutu masa duk abinda zai sashi farin cikin duniya”.

Da sauri Khausar ta rumtse idanunta sani tsinkewar da zuciyarta tayi tare bugawa ya bada sautin bu-bu-gum wani irin tsoro ne ya ka mata.
Matsawa kusa da ita Rahma tayi ta manna kumatunta dana Khausar tayi musu selfie.
Murmushi Khausar tayi wanda ya sake ƙawata kyawun fuskarta.

Cikin sakin fuska da ƙaunarta Rahma tace.
“Matar yaya dan Allah akular mana da ɗan Uwan mu asashi farin ciki akwantar mishi da hankali asama mishi nutsuwa da jin daɗi”.
Ware idanu Lalla Hafsat tayi kana ta riƙe haɓa tare da cewa.
“Lalle Rahma yaushe kika fanɗare kika zama haka?".
Murmushi tayi tare da langwaɓar da kai kana tace.
“Ai gaskiya ne Lalla Hafsat ina faɗa mata ne ta kula da Yah Aleey saboda gwara ta sani shi ɗan gata ne ɗan lelenmu ne muna sonshi fiye da yanda muke son kanmu”.
Khausar Kam wani irin tsinkewar zuciya da tsoro na ya mamaye zuciyarta.
Asma'u da bata wani daɗe da shiga ba ta kalli idanun Khausar cikin sauri ta ƙunshe dariyar ta.
Chapter 74 · 0% Book details