← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 150

Sashe 18

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Acan ɓangaren Abba kuwa bayan sun gama waya da Moddibo number Malam Ahmad yayi dearling jin yayi Picking yasa yayi gyaran murya tare da sallama kana suka gaisa bayan sun gaisa Abba ya sauƙe ajiyar zuciya tare da gyara zamansa kana cikin sanyin murya yace.
“Dan Allah Malam idan anyi sallar La'asar ko zan samu ganinka?”.
Cikin daddataku yace.
“Toh badamuwa Insha Allah zanzo, Allah dai yasa lafiya?”.
Jinjina kai Abba yayi tare da faɗin.
“Eh babu komai Allah ya kawo ka lafiya”.
Bayan Malam Ahmad ya katse kiran ya juya ya kalli Ummi dake gefensa kan 2sitter sai kuma Asma'u da Bashir dake kan 3sitter cikin sanyin murya yace.
“Abban Jameelu ne ya kirani”.
Cikin alamun damuwa Ummi tace.
“Lafiya kuwa!?".
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Lafiya lau”.
Girgiza kai tayi hawaye na taruwa akwarmin Idanunta tace.
“Ka dai ƙara tabbayarsa”.
Ganin bata gamsu bane yace.
“Toh bari in tambayan”.
Ya ida maganar tare da dearling number Abba.
Abba na ɗagawa Malam Ahmad yayi Sallama kana yace.
“Dama na faɗawa Fatima gashi-gashi yanda mu kayi to amma tace wai dan Allah meyake faruwa lafiya kuwa?”.
Kai Abba ya gyaɗa cikin sanyin murya da tarin damuwa yace.
“Eh lafiya lau dama ina so ne kuɗaɗen da suka haɗa na motar ta data saida da kuma na Sarƙoƙinta tunda ga yanda Ubangiji ya ƙaddara to shine kuɗin nake so kazo in baka su sai ka maida mata su, sannan kayi mata bayani tare da kwantar mata da hankali”.
Kai Malam Ahmad ya gyaɗa tare da faɗin.
“Toh shikenan bari zan faɗa mata”.

Ahankali ya juya ya kalli Ummi bayan ya katse kiran kana ya mata bayanin duk yanda sukayi.
Cikin rauni ta sunkuyar da kanta hawaye na kwaranya daga Idanunta Shar-shar-shar suna zuba akuncinta cike da tausayawa suke kallonta musamman Asma'u lokaci ɗaya itama Idanunta suka fara zubar da ƙwalla.
Asanyaye Ummi ta ɗago kanta tare da kallon Malam Ahmad Muryanta na rawa tace.
“Kace masa bana son Kuɗin Na yafe me zanyi da kuɗin da suka kasa ceto min Jameel me zanyi dasu?.
Me zanyi da duk wani kayan ƙawa bana so bana ɓuƙatar su nayafe su duniya da lahira bana ƙaunarsu”.
Anutse Malam Ahmad ya girgiza mata kai cikin rarrashi yace.
“Kada kice haka Fatima kiyi haƙuri Jameelu addu'a zaki yi masa, kuɗin nan kada kice ba zaki karɓaba, idan har kika ce ba zaki karɓa ba zaki sake saka Mahaifinsa cikin damuwa da tashin hankali aransa”.
Kai ta girgiza tare da miƙewa ta nufi Bedroom ɗinta still hawaye na bin kuncinta.
Asma'u kuwa kife kanta da jikin cushin tayi tare da fashewa da sassayan kuka me gunji cikin sauri Bashir ya ɗagota tare da share mata hawaye cikin sanyin murya yace.
“Asma'u Yah Jameel baya ɓuƙatar kukan mu addu'ar mu kawai yake buƙata, dan Allah ki daina yi masa kuka kinji, na tabbata Yah Jameel baya son wannan kukan”.
Kai ta gyaɗa masa still hawaye na bin fuskarta tace.
“Bashir ya zanyi idan na tuna Yah Jameel ya barmu bari na har abada nakan ji zafi da ƙuna acikin zuciyata, nakan ji raɗaɗi mai zafin gaske nakanji.
Tamkar zuciyata zata fashe”.
Cikin sanyin murya Bashir yace.
“Toh ya zamuyi da hukuncin Ubangiji Asma'u haka Allah ya tsara Yah Jameel ba zaiyi tsawon rai ba, koda ace basu sace sa sun kashe ba na tabbata ba zai wuce wannan kwanakin ba mu dai kawai addu'ar mu yake buƙata a hankali kuma waɗanda suka aikata masa hakan zasuga SAKAYYAH mabayyaniya addu'a kawai zakiyi ta masa kinji”.
Jinjina kai tayi kana tace.
“Inayi kuma zan cigaba da har ƙarshen rayuwata da izinin Ubangiji”.

Ummi nashiga Bedroom ta zaune gefen gado tare da fashewa da kuka Malam Ahmad na shiga cikin daƙin ya zauna gefenta kana ya sanya hannunsa tare da janyota ya mannata da jikinsa cikin sanyin murya yace.
“Kiyi hakuri ki daina kuka Fatima, ki yiwa Jameelu addu'a Ubangiji ya masa rahma sannan madadin kice ba zaki karɓi kuɗin nan ba ki sake sakawa mahaifinsa damuwa to ki karɓa”.
Cikin rauni Ummi ta sake manna kanta da ka fadarsa kana ta cigaba da sheshsheƙan kuka.

Tafin hannunta Malam Ahmad ya damƙe acikin nasa kana ya cigaba da cewa.
“Idan yaso idan kika amshi kuɗin sai kiyi amfani dasu wajen yiwa Jameelu Sadaƙatul Jariya.
Kamar Gina Masallaci, Ko kuma gidan marayu, Ko Asibiti,ko makarantar addini, ko kuma yin Bohorle rijiya da dai sauransu da nufin Allah ya kai ladan garesa kinji ko Fatima kada ki butulcewa Ubangiji”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana yace.
“Kada kice ba zaki karɓa ba Ubangiji shi yabamu Jameelu, sannan kuma shi ya ɗauke Jameelu bamu da abinda zamu yiwa Jameelu sama da addu'a shine kaɗai soyayyar daza mu nuna masa amma idan kika bar kuɗin ya mahaifinsa zaiyi dasu?”.
Jinjina kai Ummi tayi cike da gamsuwa kana tace.
“Shike nan insha Allah zanyi yanda kace Allah yajiƙan Jameelu Allah ya gafarta tamasa Ubangiji ya jaddada rahma agaresa”.
Malam Ahmad na share mata hawaye ya amsa da.
“Ameen”.

Ɓangaren Hajiya Lami kuwa zaune take afalonta cikin sanyi Samira ta fito daga Bedroom ta zauna gefenta tare da tsira mata idanu.
Kallonta Hajiya Lami dake riƙe da wayarta tayi kana tace.
“Lafiya kuwa Samira?”.
Girgiza kai Samira tayi cikin sanyin murya tace.
“Mommy cikina ke ciwo”.
Ahankali Hajiya Lami ta ajiye wayarta tare da tsira mata Ido kana tace.
“Meke damunki ne kwanan nan kina yawan complain din cikin ki yana ciwo”.
Rau-rau tayi da ido still Muryanta na rawa tace.
“Mommy nikam wannan ciwon cikin ya fara damuna,
duk fa lokacin daya Murɗa Mommy wani farin ruwa ne yake fito min ta gaba na.
Mommy har saina sa Path agabana kamar mai yin period kuma ba jini bane kawai ruwa ne yake fito min mai ƙarni da masifar wari”.
Zare ido Hajiya Lami tayi tare da cewa.
“Ruwa kuma?,Ni Lami wani irin ruwa kenan?”.
Cikin rawan murya Samira tace.
“Ruwane kamar Sparm yake fita sannan da yawa da yauƙi yake fita Mommy ga wari da ƙarnin Masifa yanzu bakya jin ƙarnin da na matsoki”.
Da sauri ta jujjuya mata kai alamun a'a.
Ita kuwa Samira cike da damuwa taci gaba da cewa.
“Nifa idan na sunkuyar da kaina ƙasa ƙarnin da warin nakeji”.

Girgiza kai Hajiya Lami tayi tare da haɗiye wani abu mai masifar ɗaci kana ta kalli Samira tare da cewa.
“A'a Samira nikam ban jiba. Amma tun yaushe ya fara miki haka?”.
Kallonta Samira tayi tare da faɗin.
“Yafi kwana biyar idan naji cikina ya Murɗa ya Murɗa, sai wannan abin ya zubo da fari ya fara zubowa kaɗan-kaɗan, to amma yanzu ya fara zubowa dayawa, sannan ciwon cikin yana ƙaruwa baki daya hankalina ya tashi Mommy!”.
Cikin sauri Hajiya Lami tace.
“To bari zan shirya Inje wajen boka Kar'uzu in Faɗa masa halin da ake ciki”.
Suna cikin magana suka ji ƙaran buɗe Bedroom ɗin Abban Samira.

Ganinsa yasa Hajiya Lami wayancewa da faɗin.
“Eh Samira Insha Allah Idan Daddy ki ya bari zanje induba Aminan Hajiya Bunayya dake fama da ciwon ciki”.
Cikin nutsuwar Kamilin Dattijo dake cike da kamala da nutsuwa ya ƙaraso cikin falon tare da kallon Hajiya Lami cike da dattako yace.
“Ayyah Subhanallah lallai dai naji kuna maganar ciwon ciki ashe Amina ce ba lafiya Allah ya sawwaƙa”.
Da sauri Hajia Lami tace.
“Amin dai”.
Shi kuwa yana gwara zaman hular kansa yaci gaba da cewa.
“Shiyasa na kwana biyu ban gantaba ashe ba lafiya ne?”.
Kai Hajiya Lami ta gyar'ɗa tare da cewa.
“Eh wallahi dama so nake idan ka fito zanje in dubata Idan ka amince”.
Jinjina kai yayi kana yace.
“Ayyah to ba matsala ki Gaishe su”.
Chapter 18 · 0% Book details