← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 150

Sashe 52

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Didin kuwa fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi ta kallin ƴaƴan nata dake zaune reras agabanta kana tace.
“Alhamadullah Allah na gode maka da ka cika min farin cikin ahlina”.
Kai Abualeey ya jinjina tare da faɗin.
“Masha Allah”.
Ibraahim kuwa
janye hannunsa dake cikin na Modibbo yayi kana ya juya tare da kallon Alƙibla yayi Sujudur Shukur.
Kana ya ɗago tare da komawa gefen Moddibo ya zauna still fuskarsa ɗauke da ƙayateccen murmushi ya kalli Sarki Youseef Mouley tare da faɗin.
“Abualeey Addu'ar mu ta karɓu Ubangiji ya dawo mana da Yah Aliyu alokacin da bamuyi zato ba sannan ba muyi tsammani ba sai nake ji kamar gaba ɗaya burikana na duniya aka gama cika min dan ganin ɗan Uwana kuma gudan jina”.
Kai Sarki Youseef Mouley ya gyaɗa kana yace.
“Tabbas kuwa domin babu abinda ya gagari Ubangji Allah da kansa yace mu roƙeshu zai amsa mana. Domin shi addu'a ba'a gaggawa dashi”.
Moddibo kuwa cike da tsananin so da ƙaunarsu dake ratsa ko wani magudanan jinin jikinsa yace.
“Tabbas kuɗin kun kasance min. Garkuwa ne atare dani ina jin ajikina babu abinda zanyi face godiya ga Allah daya haɗani daku kafin na koma garesa”.
Haka suka cigaba da hira tsawon lokaci ganin suna shirin tafiya yasa Moddibo ya sunkuyar da kansa ƙasa kana yace.
“Ayyah Abba dan Allah Ina bukatar wayoyina akawo min su”.
Murmushi Sarki Youseef Mouley yayi kana yace.
“Kada ka damu za'a kawo maka wayoyinka dan suna hannu na”.
Cikin sauri da mamaki Moddibo ya kallesa tare da faɗin.
“Abba toh a taimaka min dasu Ummi, Innayi, da Abba zasu nemini, musamman ma Innayina zata shiga damuwar rashin jina?”.
Kai Sarki Youseef Mouley ya girgiza kana yace.
“Kada ka damu In sha Allah babu komai rashin ɗaukar wayar yana da muhimmanci, da amfanin da zaiyi Kankane yace kada a ɗauki wayar shiyasa ma ban kawo maka ba”.
A ladabce Moddibo yace
“Abba zasu shiga damuwa saboda zasuji tsoro kada abinda ya faru da Jameel nima ya faru dani”.
Cike da kulawa Sarki Youseef Mouley yace.
“Wanene Jameelun naka?”.
Idanunsa ya lumshe tare da buɗewa kana yace.
“Ai wannan Dr Jameel ɗin dana biyo, da fari ina bibiyarshi a zatona J nane sabida tsananin kamar da sukayi”.
Nan ya shiga basu labarin Jameel da duk abinda ya faru dashi.
Ya ɗaura da faɗin.
“Shiyasa lokacin da naga wannan Dr Jameel baki ɗaya na ɗauka cewa Jameelu na ne saboda kamanninsu yayi yawa, hatta maganarsu, tafiyarsu, muryar su babu abinda ya raba su sai dai ɗabi'unsu ya samu bambanci dana Jameelu na”.
Cikin raunin murya da tunowa da Jameelunsa ya basu cikekken tarihin abotarsu.
Sosai suma suka tausayawa masa tare da yiwa Jameelun fatan samun rahamar Ubangji kana ya cigaba da faɗa musu cewa aikine ya kawo sa kamfanin Baban Jameelu.
Cikin fesar da numfashi Ibraahim yace.
“Allah sarki Yah Jameel Allah ya gafarta masa”.
Cikin sanyi Moddibo yace
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Lalla Khadijah ce ta gyara zama tare da fuskatarsa kana a mutunci tace.
“Da fari dai kaga iya mu yamune cikin mahaifiyarmu da wasu daga cikin amintattun fadane, suka san da isowarka wacce dole labarin ya bazu cikin Faɗa, to Alhamdulillah zan haɗa taro na musamman damon gabatarda kai a tsakiyar family'nka wato zuriyar sarki Aliyu Mouley, wanda zuriyace ta tun kakannin Abbanmu da kuma kakanninmu, mu da kuma iyayenmu da ƴan bappanayenmu dama goggoninmu, in Sha Allah zayi tarone na musamman dan dan haka ka shirya fuskatarta idanu mabanmanta. Alhamdulillah na gamsu da nitsuwarka zuwa yau kuma na fahimci kasan komai na tsarin al'adunmu da nake mamakin yadda akayi ka sansu”.
Da sauri Kalla Hafsat tace.
“Ke kuwa Lalla Khadijah ya za'ayi ya rayu da jakadiya kiyi tunanin akwai wata al'adar da bazai saniba”.
Murmushi Modibbo yayi domin shi dai innayi bata taɓa alaƙantashi da labarin fadaba, sai dai yasan komai na fadar ne a cikin mafarkansa.
Abualeey ne ya gyara zama tare da cewa.
“Zuwa yanzu mun gama shiryawa komai na taron”.
Haka dai sukaci gaba da tattauna lamurran.

Washe gari ranan Asabar misalin ƙarfe uku na yamma Jirginsu Innayi yayi landing a _Rabat Sale international airport_.

Suna sauƙa a airport motocine na alfarma guda biyar suka zo ɗaukar su bisa jagoranci Dr Ahmad abokin Abban Jameel.
Mota ta farko Dr Ahmad ke driving yayin da Abban Jameel ke gefensa daga can baya kuma Innayi ce tare da Hajja Nana da kuma Khausar.
Motar dake bima sa kuwa Ummi ce da Hajiya Bunayya sai kuma ƙanwar Momyn Khausar Aunty Hajara, sai Haiydar da yake gaba gefen direba.
Yayin da mota ta uku kuwa Asiya, Asma'u ce tare da Dija. Sai Aunty Ruƙayya ƙawar Mommy
Motar dake bayansa kuwa Baffa Jimeta ne da matarsa Hajiya Umma, kana da Babbar Ƴar sa mai suna Aunty Hawwa .
Yayin da motocin ke tafiya ajere cikin nutsuwa bisa Jagoranci Dr Ahmad
Bayan sun shiga cikin gari sun nufi unguwar Ben slimane, cikin sauƙe numfashi Innayi ta fesar da numfashi tare da buɗe Idanunta ta kalli cikin garin da tsarukan da kuma gine-gine suka sauya alamar garin ya sake samun cigaba fiye da da.
Cikin sanyayyar murya me cike da kewa da kuma bege ta kalli Dr Ahmad dake driving kana tace.
“Mubi ta unguwar El'gara sai mu ɓullo ta cikin Ben Ahmad dan Masarautar Rabat zamu nufa”
Cikin wani amintacciyar murmushi Abban Jameel ya juya ya kalleta kana yace.
“Kai tsaye kuma?”.
Kai ta jinjina kana tace.
“Eh can zamu nufa shine abinda yafi da cewa”
Still Idanunsa na kanta yace.
“Amma da ya kamata mu fara isa masauƙi mu huta tukunna!”.
Numfashi ta fesar tare da faɗin.
“A'a ai acan ya dace muyi hutun”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Toh shikenan”.
Shi kuwa Dr Ahmad juya akalar motar yayi, kana suma saura suma mara mishi baya.
Nan suka ci-gaba da tafiya cikin nutsuwa still motocinsu na jere.

Suna isa ƙofan Gate na farkon Masarautar Rabat ganin motoci ajere yasa cikin Sauri Hadiman dake bakin gate ɗin mutum biyar suka miƙe biyu suka tsa gefen damar motan biyu gefen hagun motar kana ɗaya ya tsaya agaba.
Cikin nutsuwa da yanayin jikin girma Innayi ta sanya hannu ta buɗe murfin motar kana ta fito yayin hannunta ke riƙe da wani abu kamar murfi kolbar Vaselin sai dai bisa ga alamu ginannene kana anyi sa da hatimin Masarautar.
Wanda ke kusa da ita ta miƙawa.
Karɓa yayi ya duba kana yayi saurin kallon fuskarta sai kuma ya juya ya miƙawa na gefensa shima ya karɓa ya duba.
Da wani irin sauri suka ɗaura hannunsu asaman ƙirjinsu kana suka sunkuyar da kansu alamar girmamawa.
Kai ta jinjina musu.
Kana cikin sassarfa suka juya tare da buɗe musu Gate ɗaya daga cikinsu ya tsaya abakin Gate yayin da sauran huɗun suka marawa moticin baya cikin sassarfa suna isa Gate na biyu ɗaya daga cikin masu binsu yayi saurin buɗe musu Gate ɗin suka shiga kai tsaye har harabar fadar suka isa, suna isa sukayi Parking atare.

Acan motarsu Hajiya Bunayya kuwa Haiydar wani irin zazzafan ajiyar zuciya ta sauƙe mai nuni da zallan mamaki kana ta kalli gabas da yamma kudu da Arewa wani irin daular duniya da suka shiga wanda ya kamata akirasa da Aljannar duniya cike da al'ajabi ta maida idanunta kan Ummi kana tace.
“Toh nan kuma ina muka zo haka”.
Lallausan murmushi Ummi ta sakar mata kana tace.
“Nan gidansu Moddibo muka zo gidan Mahaifinsa”.
Dariyar sheƙiyanci Hajiya Bunayya ta saki tace.
“Kai lallai wannan ta tsuniya yawa ne dashi nan ɗin ne gidansu Moddibo?”.
Kai Ummi ta jinjina tare da faɗin.
“Toh ki zuba ido ki gani”.
Baki ta taɓe tare da yiwa Ummi wani kallo kana tace.
“Caɓ amma Ummin Jameel banyi zaton haka daga gareki ba da girmanki”.
Ta ida maganar tare da ƙyalƙyalewa da dariya ita baki ɗaya ma maganar dariya yake bata yo ai ko amafarki Moddibo bai isa ya kasance jinin wannan ahali ba mutumin da ake kyautata zaton ɗan shegene.
Ummi kuwa da mamaki ta kalli yanda take dariya kana tace.
“Kina mamaki ne?”.
Hajiya Bunayya kuwa cikin taɓe baki tace.
“Sosai ma kuwa ai ba mamaki ba harda Al'ajabi na haɗa Moddibo fa”.
Sai ta kuma fashewa da dariyar sheƙiyanci data tuna wai Ummi tace nan gidansu Moddibo ne.
Kai kawai Ummi ta girgiza batare da tace Uffan ba tana mai bin baki ɗaya ilahirin gidan da kallo.
Chapter 52 · 0% Book details