← Book details Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 150

Sashe 16

Sakayyah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dai-dai lokacin Moddibo ya isa bakin barandar ɗakin Innayi yana son ya mata bayanin Abba ya kira sa akan yaje yasa yazo wurinta, yana taka step ɗin firko ne.
Ya jiyo sautin Muryan Innayi na cewa.
“Toh Moddibo ai jika nane Hajja Nana.”
Sai kuma tayi murmushi mai cike da jin dadi kana taci gaba da cewa.
“kinga shikenan faɗuwa tazo dai-dai da zama Aliyu jikana aishine Moddibon kinga sai muyi tuwonmu manmu”.
Cikin sauri Hajja Nana ta miƙe tare da kallon Innayi kana ta zare ido sannan ta buga hannunta aƙirji tare da cewa.
“Ji kanki?”.
Jinjina kai Innayi tayi tare da faɗin.
“Eh jikana ne Aliyu”.
Still Hajja Nana na tsaye cikin zare ido tace.
“Shine Moddibo kenan?".
Kai Innayi ta gyaɗa mata cikin tabbatarwa.
Ita kuwa Hajja Nana cikin wani yanayi tace.
“Sannan kuma shine Malamin nasu?”.
Kai Innayi ta kuna gyaɗa mata kana cikin sanyi tace.
“Tabbas shine jikana Moddibo”.
Cike da mamaki Hajja Nana tace.
“Kenan jikanki ne Moddibo wanda Khausar ke so?”.
Still Kai Innayi ta gyaɗaa karo na barkatai tare da cewa.
“Eh".
Cikin wani irin masiyacin kallo Hajja Nana ta kalleta tare da cewa.
“Aikuwa baza ta saɓu ba bindiga aruwa, ai wannan ma ta tsuniyace mara wanzuwa ai wannan ma zancen banza ne, wannan ƙarya ne wlh. Khausar bata isa ba mu zata lalatawa tushe da asalin zuri'a”.
Cikin sauri Innayi ta mike tare da zare ido ta kalli Hajja Nana cike da mmki tace.
“Wannan wace irin kalma kike faɗa?”.
Gyara tsayuwa Hajja Nana tayi kana tace.
“Toh Innare waye bai san cewa jikanki bashi da asali ba, wani mahaukacin ne zai ɗauki ƴa ya baku? waye zai so haɗa zuri'a da jikan ki da bashi da asali! ɗan shege da kika samu akwararo ɗan da ba'asan tushe da Asalinsa ba!!!”.
Cike da matsanancin mamaki Innayi ke kallonta Hajja Nana ta cigaba da cewa.
“Ɗan da ba asan tabbacinsa ba asan asalinsa ba. Yaron da ake da tabbacin cewa ba ɗan sunna bane ɗan zina ne. Shine za ahaɗa zuri'a ta dashi ai wallahi wannan ba zata yuba”.
Ta ƙarashe mgnar cikin yanayinta na ba shina ba sabo.
Cikin fushi da ɓacin rai Innayi ta watsa mata wani irin kallo tare da cewa.
“Ke dakata Hajja Nana ki kama kanki".
Dogon tsaki Hajja Nana taja tare da cewa.
“Bazan kama ba, tabbas abinda na faɗa gaskiya ne, idan har yana da uba to waye Ubansa tun da kuka zauna tsawon rayuwarku shekaru talatin da acikin Garin Gembila waya san Asalinsa wayasan Ubansa wayasan tushensa na faɗa na ƙara fada da ƙarfi shi ɗan shege ne ke kuma magajiya”.
Moddibo dake baranda atsaye ne, yayi wani irin jan numfashi tare da rumtse idanunsa domin tamkar sauƙan aradu haka maganganunta suka ratsa ƙwaƙwalwarsa zuwa dodon kunnensa.
Hajja Nana kuwa cikin fushi da ɓacin rai tace.
“Shegene jikan naki na faɗa zan kuma faɗa”.
Wani irin kallo Innayi ke binta dashi zuciyarta na wani irin tafarfasa ta kalli Hajja Nana kana tace.
“Tabbas babu wanda yasan asalin Jikana sannan babu wanda yasan ina ne tushen jikana amma ke dai baki isa ki jefe mu da mugayen kalamai irin wannan ba”.
Taɓe baki Hajja Nana tayi tare da watsa mata Harara kana tace.
“Na nawa kuma ance da kuturu Allah ya la'ance ka, jikan ki dan kwararo ne ɗa mara tushe da galihu”.
Cikin tsanananin tashin hankali da ruɗu da wani irin tsinkewar zuciya mai tafiya da nunfashi Moddibo ya dafe kansa da hannu bibbiyu tare da rintse idanunsa...!

Littafin SAKAYYAH dai na kuɗi Hajia ba free book bane dan haka ki saya ki karanta cikin Aminci da salama 1k ne kacal kuɗin samun damar karantawa 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar
biyanki ta WHATSAPP 09097853276

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 5*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Runtse idanunsa yayi da karfi, tare dasa hannunsa duka biyu ya matse kansa, sabida yadda ya fara jin kansa yana juyawa tare da sarawa, yayin da kalaman Hajja Nana ke dukan tsakiyar ƙoƙon kansa yana ratsa ƙwaƙwalwar kansa tare da jin suna ratsa kunnuwansa suna yawo tamkar yanda aradu ke yawo asararin samaniya, baki ɗaya idanunsa sun juye sun kaɗa sunyi Jawur, kab ilahirin jikinsa rawa yake kar-kar-kar tamkar mazari cikin wani irin sauri zuciyarsa ke bugawa da kaso Cassa'in da tara cikin ɗari, tana mai wanzar da jini litter-litter a cikin dukkan daƙiƙu yana watsashi wa jijiyoyin jikinsa.
Hakan yasa tuni rigarsa ta fara jikewa da zufa, duda yanayin garin Gembila da ba'a musu zafi.
Sai ga tashin hankali ya sashi tsats-tsafo zufa sabida yadda zuciyarsa ke bugawa da Masifaffen ƙarfi yayin da numfashinsa ke fusga tamkar zai bar ganganar jikinsa, cikin tsanananin tashin hankali da wani irin masifaffen juyi da kansa keyi ya ƙara matse kansa da hannu bibbiyu, da ƙyar ya iya daga ƙafarsa ya sauka daga barandar ya nufi side ɗinsa yana tafiya tare tangaɗi tamkar ɗan maye yayin da kuma jiri ke ɗibarsa.

Yana cikin tafiya tamkar zai faɗi ya tsinkayo muryar Innayi cikin tsananin fushi da takaici cikin zafin zuciya tace.
“Zaki sha mamaki kuwa.
Hajja Nana zan nuna miki ƙarfin iko da isan ɗan shegen da kike faɗi. Zaki gane kinyi kuskure ambatonsa da wannan sunan da yafi ƙarfinsa. Auren nan kuma da izinin Ubangiji tamkar anyi sa angama ma, in dai wannan auren nen kika tashi ki kace zaki yaƙesa sannan kika ce zaki hana toki sa. Aranki anyishi an ɗaura shi angama domin ke dai baki isa ki haramta abinda Allah ya halastaba wlh muddin ina raye toh in Sha Allah kamar ma anyi auren nan an gama zan shayar dake mamaki”.
Wani irin kallon rainin hankali me ɗauke da zafin zuciya Hajja Nana tabi Innayi dashi.
Ita kuwa Innayi. Cikin fushi ta cigaba da cewa.
“Babu wani mahaluki na duniya daya isa ya hana wannan ɗaurin Auren sai Ubangiji daya halicci sammai da ƙassai. idan har kinga wannan Auren bai kasance ba to daga Rabbus Sanawati ne amma ba daga ke Hajja Nana mai kaɗa kai kamar Ƙadangariya ba”.
Wuhuhu ina wuta Hjja na ta faɗa ciki.
Cikin fushi da hatsala Hajja Nana dake ƙoƙarin fita ta tsaya tare da juyawa ta kalleta sai kuma tayi murmushi tare da gyara tsayuwar ta kana tace.
“Wani ƙarfin iko ko kuma isa. Ɗan shege ke dashi? Ai sai dai kuje kunemi watsatstsiya ƴar gaba da Fatiha ku Aura masa, amma dai ba jikata dake da asali da tushe ba zuri'ata tayi miki nisa sai dai hange daga nesa?”.
Afusace Innayi da Idanunta suka kaɗa tamkar garwashi tace.
“Tabbas zaki ga isa da kuma ƙarfin Iko irin na ɗan shegen da kike faɗa agaban idanunki za'a ɗaura Aurensa da Khausar sannan ya ɗauketa su tafi ke babu yanda kika iya, zakisha mmkin ganin tushensa daya girmi tunaninki ya kuma zarta zatonki. domin ke ba kowa bace a kansa, Allah ya wadaran aminiyar da bata mutunta amintaka, kin kasance mara ɗa'a da sanin ya kamata!”.
Ita kuwa Hajja Nana mugun kallo ta watsawa Innayi tare da nuna kanta da tsaya kana tace.
”Ni kika faɗawa haka?”.

Kai Innayi ta gyaɗa cikin tsawa tace.
“An faɗa miki wacece ke?Ko kina tunanin nan ma Jauro yaya ne da kike baza ikon ki da mulkinki kina kaɗa kai uwa ƙadangaruwa, kina abinda kika ga dama? to a hir ɗinki ki sani kece kika shigo muhalli na toh ki sani duk da cewa mu muke neman aure a ƙarƙashin ku ba za ki taka muba in barkiba domin mace bata bada Aure dan haka ki ficemin agidana”.
Wani irin dogon tsaki taja kana tace.
“Ko da baki ce in fice miki agida ba dole zan fita, amma kisa Aranki badai.
Ɗai shegen jikanki da tsarkakakkiyar jikata su haɗa Aure ba”.
Tana faɗin hakan
ta ida ficewa daga ɗakin amma still Idanunta na cikin dakin tace.
“Dama ace ansan tushe ansan asalinku sannan ansan jikan ki tsarka kekkene wanda aka haifa ta sunna, to ba komai amma jikanki da yake Najasa wanda aka haifa ta hanyar ƙazanta ba zaiyu abashi auren jikata ba, zaki ga ƙarfin Ikona da isata sannan kuma da Izzata akan al'amarin auren nan”.
Innayi da zuciyarta ke wani irin tafarfasa tace.
“Toh mu zuba mu gani kada ki fasa idan har ke kin cika mai karfin iko da Izzah”.
Ƙwaffa Hajja Nana tayi tare da sauƙa daga barandar ta juya fuuuu kamar zata tashi sama ta nufi waje.
Chapter 16 · 0% Book details